Monday 15 February 2016

Dangin Mijina Episode 4


Read The previous episode HERE


Muna shiga class’s nanma wani gurmin ake.kowa nafadan son ranshi.mutane dayawa sun ce soyayya muke da ahmed G nikuma dariya suke ban. Inani ina ahmed G. Ai yafi karfina. Maths teacher mune yashigo, tunda yashigo yake harara na. Hakan yamin nuni dacewa jira yake nayi wani abu kiris yamin rashin mutunci donhaka sai na kiyaye narufawa kaina asiri. Dama a kai danshi inyaashigo lectures zaku mike bayan gai sheshi har sai yayi settling, haka zalika idan yagama Zaku mike kubar aji har yafice daga fanninku. To yauma hakanne datazo fita natashi mikewa sai biro na yafadi na tsugunna donna dauka, Naji yabuga wani irin tsawa Su maeyah!!!! dama. Inyamurine bai iya pronouncing sunanba. A firgice nace naam  sir. Yace follow me to my office.

 Nan nazaro ido. Zafyra tace maganinki bake kinki tashiba na tamke fuska nace kuji iskaro biro nafa nadauka zakimin tsiya nabishi abaya har office yasani nazauna akasa nafi awa biyu agun. Ahmed G yadawo yashigo office din Yajuyo ya kallen baice komaiba, Nikuma kunya naji don tunda nake baataba kawoni staff dasunan nayi wani laifiba sai yau wanda natabbata laifina bawani babba bane. Har aka fita break aka koma bawan Allahnan baicemun komaiba. Ahmed G kuma nazaune shima yaki fita yasa mana ido.kuma baice komaiba. Harna fara tunanin da gayya yakawoni wato don Ahmed G yagan nine yaga matakin dazai dauka tashi yayi yafita can sai gashi yadawo minti biyar saiga zafyra tazo gum math teacher sir barin tambayeta inda ta ajiyemana test Papers dinmu zaa karba. Yace toh, sai tazo daidai kunnena sannan tace. Inji mal. Ahmed G. wai yasanki da taurin kai anma kiyi hakuri kibada hakuri, na kalleta sannan nace Allah sauwaka.
 Tayi tayi na yi kwafa darai naki.hartagaji tafice. Sai shima ahmed G.yafita. Hakan yasa maths teacher yace natashi nayi kneeling haka har aka tashi sannan yace natafi shima don wani teacher yace masa yabarni nayi sallah ne. Ina fita naje bakin tanki nadebi ruwa nazauna sai nayi tagumi. Maganansa naji .Mayah! Yaushe zaki daina taurin kai!? Tsugunawa wada ba gajiyawa bane anma ke kokadan bantaba jin kinbada hakuri ba, Na yi murmushi sannan nace ana bada hakuri ne a lokacin da akayi laifi Yace ba laifi kikayiba? Nace ae. Wannan kuskurene.
 Ya gyada kai sannan yace kije nurse ta dubaki nasan jikinki yayi tsami. Nace a a daga zama kawai? yace God save you anjima nazo tacemun bakizo ba zanmiki bulala jin ya ambaci bulala na tsorata donkuwa dukan dayayi wasu aisha alka nake tunawa yayi dariya sannan yace matsoraciya . Nace uhmn aibani kaunan bulala ne. Ahaka mukayi sallama yafice nikuma nawuce masallaci
 Washe gari bayan chemistry teachernmu yafita saiga math yashigo, na mugun bata rai anma abun mamaki sai wani dariya yakemun yana lallamina. Bayan munkoma hostel ne sister yamina muhd take bamu labara ashe dasu Ahmed G. suka koma quarters na teachers, Da dare ahmed ya kwankwasa kofa shikuwa math teacher yabude. Anan ahmed yatike shi da bindiga yace idan baifita harka naba to saiya harbeshi yaga waye gatansa. Furyad ta kwashe dawani dariyan mugunta hehehe inyamuri yaga mutuwa. Aikuwa washe gari mukaji labari wai yanemi transfer zuwa wani branch din makarantan dake toro anma shi maza ne kawai. Munci dariya kam balaifi.
Laifin dadi karewa .mungama ss1 inda muka shigo ss2 kuma awannan watan ahmed G.zasu gama servise (NYSC) dinsu bashi ba, hattani nawani tsomare nadawo abun tausayi. Shine gatana a makarantan. Yanxu yana tafiya shikenan kuma. Duk da mun shigo senior class anma bazanji dadi ba.
A satin aka hada wani thanks giving wanda zaayi a makarantan. Kowa zai hallata. Aka hada drama dasu fashion parade ahakane nafito as fulani. Bakaramin kyau nayi ba. Nasa kayan Fulani, gashina ma nayi kitson munkimtsa tsaf zamuyi. Naleko tagun don nakarbi takalmi ashe ahmed G. yahangoni. Wani irin. Gigiza yayi bashiri yasauko. Nikuma nakoma gun damuke shiri na tsaya don jira akiramu nima nafita. Yana shigowa ya kutso kai. Ina mayah!!! Gaba daya aka nutsu nace gani. Yakaremin kallo  head to toe. Sannan yace crazy you!! Kina tunanin haka zaki fita!?? Nakalli jikina dakyau sannan nace ai fashion  parade ne. will you shut up? Ya kitseni. Baniba har mutanen gun sun tsorata. Idan kika kuskura kika fita haka i will deal with yo. yajuya yafita. Niko tsugunawa nayi ina tunani.furyad dama a kanuri zata futo, zafyra kuma hausa. Sukace nahakura tunda hakane. Nakallesu sannan nace. Ubanane dazai hanani? ! Its just for fun. Furyad tace kinfi kowa sanin halinshi is left for you. Ana kiran fulani kuwa nafice abuna. Nayi nadawo nahan kalta da yanayin dafuskansa yadawo wanda baya shiga wannan yanayin sai in antabani. Yau gashi nida kaina na batamishi rai. Ina gamawa nakoma hostel.nasa check saiga wata kuwa tazo waikizo inji malam ahmed. nafice ina zuwa baiyi wata wata ba mari ya sharara min tassssss.
Nadago na kalleshi tare da rike fuskana, Nabude baki zanyi magana yace shhhhhhhhhh. Tare dasa hannunsa a bakina alamun nayi shiru. Nayi kwaf ina kallonshi. Mamaki alajabi komai yacikani. Wannan ma ai rainin wayo ne. Ba idda tunanina ba sai yace. “Banaso koda baa gabanaba wani yaganemin jikinki”. Nace anma malam ya katse ni nadai gayamiki. Be warned .yajuya yatafi. Hostel nashiga narinka kuka wannanma ai cin mutuncine ko mamana data haifen bata taba marinaba balle wani, su zafyra da furyad suka shigo. Furyad ce tace meye kuma na kuka? Sai dana gama kukana mai isana sannan nagayamusu abinda yafaru.furyad tana dariya tace ke kishine. Kuma saida akamiki magana. Kinfi kowa sanin halinshi anma kika take kika fita. Haushi yasa ko kulasu banyiba. Washegari munje prep. Dama ranan shine on duty. Ya aika nazo. Nace yarinyan tatafi. Saidaya aiko mutane hudu anma ina zaune kif ko motsawa banyiba. Su furyad kuwa sai lallami suke. Nace su rabu dani. Haka kuwa akayi. Antashi a prep nadauko books dina zamu wuce islamiya. Naganshi zaune a gate din classes din. Yadaura hannu akai. Bayama cikin tunaninsa. Saina koma nazauna.haka akata wucewa har aka watse naga baida niyyan tashi. Sai nabata rai nazo zan wuce. Mayah"!!!!! Yakirani.na tsaya anma ban juya ba. Yataso yazo daidai bayana hakan yasa nadan kara gaba gudun zargin students tunda nagashi ba kunya bane ta isheshi. Yace meyasa zaki zabi ki hukunta ni tahaka?shin baki lura dani bane? Wallahi ina sonki nafara kaunarkine tun randa na hada ido dake, kinada kwarjini sannan a idonki akwai wani sirri wanda bakowa bane zai fahimta. Kece farin cikina. Farin cikinki shine nawa haka bakin ciki. Kiyi hakuri abisa marinki danayi zafin kishine, saidana koma gida abun yadamen. Hawaye ne suka zuba a idona batare dana kalleshiba dasauri nafice agun, gudun karya biyoni shima juyawa yayi yabar gun.
Danaje islamiyanma ban fahimci komaiba. Har aka tashi.sannan muka taho nida su zafyra mukayi alwala mukaje masallaci don muyi magrib. Anan suka takuramin har nagayamusu. Kowacce jikinta yayi sanyi sannan furyad tace. Majidadi kina sonshi aiko! ? Na kalleta sannan najuya kai. Zafyra tace erhn gud shiru ma amsane.
A satin komai na yacanja kaman baniba. Wani irin shaukin so ne yake kwasata. Ina matukar son ahmed G. so na hakika. Babu sirki awannan son. Zan iya salwanta rayuwana akanshi haka kuwa akayi suka gama service dinsu bakaramin tashin hankali nashigaba a satin dazasu kammala. Duk na sukurkuce nawani rame. Karatunma bana iyayi .lura dahakan yasa wata rana ya aika akiran. Jaje office dinsu .nasameshi idona a kasa. Yace mayah!! Nace naam. Yace ayya.yanzu zan barki ko?! To jekiyi kukan missing ungo. Yamikomin handkerchief dawata takarda yace jeki share hawayen naki. Nadan muskuta kaman bazan karba ba.nace waya gayama zanyi missing dinka? ka tattara katafi ko zan samu wasu.duk ka kashemin kasuwa. Wani irin tsorattaccen kallo yamin. Kafin yace komai harna ruga waje Ina zuwa hostel nazauna naci kukana. Na jefar da letan cikin akwati.don a tunanina ba wuce ban hakuri ba. Saida daredare nace barin duba. Ko hankalina zai dan kwanta nasan ahmed G. Da iya kalamu masu dadi. Nadauko nafara karantawa
My Babyyyyy
Just nasanar dake cewa nayi alkawarin zama dake ta kowani hali. Bazan bari a cucekiba. Donhaka nayanke shawaran applying zama permanent teacher don nazauna dake har ranan dazaki kammala. Sannan albishirinki. Nakai goron tambaya na gidanku.kuka an amince min.
Your husband
Ahmed Galadima.
Wani irin tsalle da ihu nayi. Wanda saidana farkar da mutane daga bacci.lafiya aka fara tambaya nace babu.kowa tagama complain dinta sannan takoma.dama furyad da zafyra yan baccin mutuwa ne. Insun kwanta basa tashi sai safiya. Shima da rikici suke tashi.dasafe bayan munsa uniform nafito musu da letan habawa sai akafasa karyawan suka barni da hadawa. Zafyra tadauko iron bucket.furyad tadauko slippers.anan suka fara kida.suna waka.
::Yaune muketa murna Sumayya tazama amarya.zataje gidan miji. Karki nuna fargaba. Ahmadu zoka bata hakkinta na sunnah.

To be Continue…

Credits Benazir


Feel Free To Comments Here...

No comments:

Post a Comment