Continuation of Halaccin Sarauta episode 4
Lalle tana bukatan karin bayani kuma tasan jakadiya ce kadai zata gaya mata donhaka ta nutsu dai har lokacin da falmata zata kwanta sannan suka fito suna tafiya jakadiya nagaba ita tana baya, sannan tace "ranki ya dade inada tambaya" jakadiya tace "mu isa sashinmu tukum", sashin jakadiya da yanuwanta yafi na bayin dan fasalin gani da kyau,tana durkushe akasa jakadiya tace inajinki, aliya ta numfasa sannan tace "bayanin kisan da waziri yakeyi, inaso kidan karamin bayani, inada masaniya akan yadda zaayi" jakadiyan ta kalleta sannan tace "bakida kai, kina baiwa mezaki iyayiwa wazirin garinnan? Ko shi sarki ya yakare? Anma tunda kinason ji shikenan, akwai lokacin da yafara hakan, yasamu saran kashe duk wanda yabata masa rai, hakan yasa sarki hada meeting akan zaa saukeshi abawa galadima waziri tunda yafishi adalci da gaskiya, anma wazirin yayi hada hadansa yasa aka kashe galadiman, anzo zaa daura barade ma nan yakara kashe barade toh kinga bawanda zaice mutuwa daga Allah kowa yasan akwsi dalili" aliya gabanta na tsananta fadi. Tace "nagode insha Allah zannemo mana hanyan tsira" jakadiya dai jinta take don bata yardaba, ta girgiza kai sannan tace "munajira" Fitan aliya fanninsu tanufa, lalle yakamata tabar fada duk tsanani saidai anya zaa barta? Baridai ta saci hanya, shigan kamala tayi kaman bakuwa ce tazo tasami kayan agun bilki wacce tamata kashedi kala kala, sannan tafice gydanta tanufa tabude dakinta har gurin yayi kura, wanka tafara shiga tagoge jikinta sosai sannan tanemi riga da skirt na atamfa yakamsta sosai,tayi sallah sannan tuni tajawo littafanta da abubuwan zane zanenta tafara tunanin yadda zatayi da waziri toh ashe inhakane zaman fada baikamata ba, yakamata tafice takashe waziri tukun, saidai baridai taga mezai faru, tana zaune har bacci me nauyi ya kwasheta tayi bacci sosai sannan tashinta tacigaba da zane zanenta tayadda zata ci karo da waziri. Gani tayi dare yayi bata damuba dama tariga data yiwa jakadiya bayanin zataje ganin wata kakanta, inbaa gantaba, kuma ta amince bilki ce dai hankalinta yatashi sosai.l, karfe tara na dare zaman dakin ya isheta tuni tanemi dogon abaaya tasa sannan tafice tana tafiya tana danna wayanta wani hotel ne wanda akwai restaurant aciki tunda tazo garin kafin ta isa fada agun takecin abinci,shiganta tazauna tayi ordering indomie kawai,tanajira don saisun dafa kafin sukawo agefen gun taji hayaniya a hall mikewa tayi tanufi gurin ga mamakinta ganin yarima yusuf tayi, wanda kwalban giya ne ahannunsa babu dogari, gashi yafara layi aliya taja tsaki tareda cewa "useless" harzata tafi taga mutumin dake aiki a hotel din yana jan yusuf akan yafice yusuf sai zuba hauka yakeyi yana surutai, abun yaci mata rai. Tanufi gun shi sannan tace "yarima yusuf ne don Allah kubarshi" mutumin baice komi ba yatafi tajuya zata tafi yusuf yakamo hannunta ta mugun tsorata anma dai tadanne azatonta yaganeta ne, anma tunanin yana cikin maye hala ne inyaganen yaki saketa donhaka ta fizgeshi suka bar hotel din ,abincin da bataci ba kenan, fitowansu tasakashi akan hanya takare masa kallo, asalin dolo ne, no wonder dan fari ne ashe dole yayi wawanci tace cikin rashin kulawa da rashin damuwa " kawuce katafi gida, wani dolonci ne yasa kafito ba dogarai?yakalleta baice komi ba can kawai yafara yunkurin amai, amai yakwara mata haushi taji kaman takamashi da duka. Taja wani tsaki sannan tace saikayi ai , juyawa tayi tana tafiya harta isa kofan gidanta juyowan dazatayi taga mutum ashe biyota yayi babu yadda batayiba yaki,tashigar dashi tareda cewa "wlh ba yarima ba ko sarki kake inkamin amai anan duka zaka sha" saiyace "nifa dan sarki ne kuma sarki!" Bata kulashiba ganin baya hayyacinsa toilet tashiga tacanja kayan jikinta takara wani wankan sannan tace "kashige kayi wankan kaima, abun haushi bacci tasamu yafarayi wani salati tayi tareda cewa yau na shiga uku....
To be continue ...
Thanks to benazir for sharing this with us. To subscribe to insidearewa Story add 08066680993 on whatsapp
Northern Nigeria (Arewa): Breaking News In Nigeria | Inside Arewa Blog Politics | Entertainment News |Fictional Stories | Lifestyle.
No comments:
Post a Comment