Continuation of Halaccin Sarauta episode 10
kallonta yayi tareda mikewa yana cewa "kinsan hakan baamai yiwuwa bane, donhaka kibari kawai" kukan takara sake mishi bashiri ya dawo tare da nuna amincewarsa, dakyar dai yabarta tafice tanufi fannin yakolo wacce tasamu suna muhawaran kayan azumi da zaa raba wanda saura kwanaki ne kadan, yakolo macece mai kima, mutunci da daraja kowacce ya zataso ace tasameta a matsayin uwa ko suruka, daga kan kayan azumi suka koma bayanin auren abdullahi, nanfa ashe yarinyan yar gidan waziri ce, hankalin aliya yatashi, itadatake shirin daukan fansa meyakai abdullahi? Wani zuciyar tace "keda kike harin uba, meya hadaki da ya" dahaka tabar zancen Yusuf kuwa hankalinsa ya gagara kwanciya da aliya dogarai uku yadiba suka fice daga fadan, gidan aliya suka nufa anma gidan arufe gam, donhaka kawai yusuf ya umurcesu dasu balla mishi kofan, sunsha wahala kafin suka samu suka cire kofan, yana shiga yakarewa idon kallo babu wani abu dazai iyacewa zai cire masa kokontonta aransa, yagama bincikenshi haryafito saiyakoma kasan gado anan yaga wata yar box kamar asusu, yacirota yakira daga cikin dogaransa suka balla masa,sannan yabude. Littatafai ne sai hotuna guda uku, dayana galadima daya kuma na wata wacce da alamu matan galadiman ne, saikuma hoton yarinya da galadiman, daya zura mata ido tabbas aliya ce kammaninta bai canja ba, yafara bude takardun daya bayan daya, tunda yake baitaba shiga tashin hankali irin na wannanba, ya mugun tsorata, tabbas yasan harda sarki a hannun kashe galadima toh anma gashi fansa tazo dauka, yaduba takardun kaf, kwalin degree dinta ne, harda certificate din nysc, ya tsorata da aliya anma yaji nutsuwa aransa, yasan duk dadewa zai aureta tunda itama yar sarauta ce, kuma tanada ilminta, toh anma yazaiyi yaceci mahaifinsa,? Dasauri yamayar da komi sannan yafito alokacin har ankawo wani kofan yasa suka saka sannan aka jingina mata mukullin a kasan kofan, sauran mukullin yatafi dashi, dakyar ya iya takowa yazo fada, jiki a sanyaye yanufi fanninsa, kwanciya yayi akam gado yana juyi babu irin tunanin dabaiyiba aransa, yagagara bacci yakuma gagara tashi yagagara motsi duk tashin hankali na bidansa, sallarhn magrib ce tasashi tashi ko dayaje masallacinma a gefe ya kudundunu, for the first time tunda mahaifiyarsa ta auresa daya mike yayi nafila rakaa biyu yana rokon Allah yabude masa haske a lamarin daya danno masa, Allah yasa abunda yake zargi bahakaba, yayi kuka sosai wanda kowa a masallacin yaji mamaki, abdullahi ne yadafa kafadarsa tareda cewa "zanyi mamakin abunda zai kawoka masallaci harkayi nafila, nasan bakaramin abune, Allah yashige mana gaba, sannan wannan yarinyar aliya!," dasauri yusuf yakalleshi jin ya ambaci aliya , yace " bata taba maka kama ba? Kaman kasanta abaya?, tanamin kama da nasanta anma na manta," dasauri yusuf yace ba itabace wannan daga wata duniya tazo" abdullahi ganin yusuf ya amsa da zafin nama yatabbatar da maganansa don tuni yana zargin yayan nasa da son aliya, shidai babu keta balle hassada adduanshi tazama sanadin shiryuwan yusuf, Yusuf nakomawa fada yashiga daki baifi minti goma ba saiga bilki da aliya sunshigo rike da tire dinsu suka ajiye akan dinning sannan suka koma gefe, yatashi yazo yazauna abincin yake kalla anma baya shaawan ci, asalima baiyi niyyan saukowa daga kan gadonba saidon yakalli aliya dakyau hakan yasa yazo yazauna, kare mata kallo yayi wacce itakuma kanta a sunkuye ne batasan yanayiba, tabbas duk wanda ya tsura mata ido yasan batayi kama da baiwa ba, kuma duk mai ilmi da wayewa yasan cewa aliya wayayyiyar macece, ba daga kayaba kome tasaka wayayyen mutum baya buya , zuciyarsa tayi nauyi jiyake kaman yayi hauka, zaitona mata asirine don yaceci mahafinsa? Kokuma zai rufa mata asiri don yana sonta,duniya tamasa zafi, kansa ya sunkuyar akan table din tareda cewa "kufita" sunfice saidai aliya jikinta yabata ba lfy ba, tadai share suka dawo daki, * bilki tana jaje tareda cewa shekarana goma agydannan bantaba ganinshi haka ba, toh ko kinmasa wani abune?? Aliya bata kulataba alokacin shikuwa yarike kansa wacce take matsanancin ciwo, tunaninsa yarude, bude fridge yayi sannan yaciro giyansa kwalba guda saidaya shanye a lokaci guda, yakara ciro wani yakafa kai saidaya shanye, fadi yayi agun sai bacci, can karfe takwas bayan aliya tagama sallolinta tafito tayi magana shiru jin baimata isoba tasan meyake ayyanawa, donhaka tashiga tareda dubawa ga mamakinta taganshi a kasa kaman matacce, kanshi tanufa tana girgizashi sai dai yana numfashi hakan yasa ta tabbatar bacci yake, pillow tadauko masa sannan tasaka masa, tarufa masa bargon domin a.c na dakin akunnene, tana zaune ta zura masa ido tana tunani "yarima! Meyake damunka? Meya sameka kashiga damuwa? Bantaba ganinka hakaba!" Fuskarshi ta dishe ,zuciyanta na mata radadi jitayi kaman andaura mata dutse akirji, batasan hawaye nazuba a idontaba, dawuri tasa hannu tana gogewa, abun yabata mamaki daga ganinshi haka shine tafara kuka? "Yooo ni aliya wani irin so nake maka? Innalilahi, karnazo nagagara cimma burina, zuciya batada kashi" wasa wasa hawaye nazuba saigashi tanata kuka, oh ni benaxir abun mamaki dama haka first love din take?, Tun karfe takwas aliya take zaune akan yusuf bata runtsaba har karfe uku nadare tana gadinsa, lokaci lokaci dogaran suna lekowa don tabbatar da babu abinda yasami yariman, karfe uku tamike tayo alwala tahau sallah, a sujjadda ta tsinci kanta da rokon Allah ya shiryi yusuf, Allah yabashi lafiya ya yaye masa damuwansa sannan yanema masa mafita, sai asuba tahakura bayan sallahn asuba tacigaba da gadinsa, yusuf bai farkaba sai karfe goma nasafe tana ganin yabude ido tafara tambayanshi ko lafiyansa lao, yayi matukar jin kunya bayajin kunyan.
To be continue....
Godiya ga benazir Umar for more follow @insidearewa on twitter
Northern Nigeria (Arewa): Breaking News In Nigeria | Inside Arewa Blog Politics | Entertainment News |Fictional Stories | Lifestyle.
No comments:
Post a Comment