Mahaifiyarsa bayajin kunyan mahaifinsa anma ya tsinci kansa da jin kunyan aliya, ta taimaka mishi yaje bandaki sannan tafito. Wanka taje tayi sannan tacanja uniform dinta tamike kan gado, bacci mai nauyine ya kwasheta, Yusuf kuwa fitowarsa yaga babu ita dasauri yakira dogarinsa daya tareda cewa "ina aliya? Kiramun ita ai batagama aikin ba" ya amsa da toh, bilkisu ce ta tasheta anma haka tamike sukaje fannin, tea yasa tahada mishi yana kare mata kallo, tayi iya kokarints ganin ta danne baccin datakeji, tahadamai yaci da cake sannan yakoma kan gado, zata dita yace "dawo ki tsaya harsainayi bacci" tana tsaye haryafara bacci sannan tafito bacci takomayi, har azahar alokacin yatashi yaga bilki ransa ba karamin baci yayiba tareda cewa ina aliya? Kikiramin ita, ta sunkuyar dakai gami dacewa "bataji dadibane yarima tana bacci yanzu haka" yazaro ido mai yasameta?" "Babu baccin dabatayibane yajawo mata, tun shekaranjiya rabonta da bacci, " shiru yayi yana tunawa tabbass yatashi yaganta kenan azaune ta kwana, tsanar kansa yayi yanajin haushin kansa oh aliya, kiyimini hakuri, shikadanshi kaman yakashe kanshi, mikewa yayi yanufi fannin bayi Budewa yayi yashiga wanda yabawa bayin mamaki domin yaran sarakunan har matan basu zuwa gun, umma uwar soro ce kadai me shiga da fice agun, gaba dayansu kowa ya sunkuyar dakai domin sun gama tsorata, ayadda suka sanshi sunsan sarai cewa ba lafiya ba, bayada mutunci ko kadan , yakare musu kallo yaga wani gado ne akwai mutum kan gadon yanufa, aliya ce tana bacci , yazura mata ido sosai. Yasa hannu yasa ajikinta yaji yayi zafi sosai, bayin sunyi mamaki nan da nan kowacce tafara tsegumi, yafice fanninsa yanufa yadau wayarsa yakira likitan gydan, bashiri yazo anan yasa bilkisu suka kamo aliya suka kawota fanninsa aka dubata, likitan yace rashin hutu ne da wahala, da rashin sabo da wahalan, yabata pain reliever, da maganin bacci, haka dai yatafi hankakin yusuf atashe baiyi motsi agefenta ba, yanata kallonta yarasa wani yanayi zai fassara kansa, Maganan yusuf yashiga fannin bayi tuni tabaza cikin fada, falmata ranta yabaci sosai, data bukaci bayani agun jakadiya nan jakadiya ta ce mata "bayin sunce kwana biyu yana nuna alamun damuwa wa aliya" falmata tazaro idanu domin ta mugun tsorata, yanzu yarasa wacce zaice zai kula sai baiwa? Duk neman matanshi bai kare awaje ba harsai yazo gun bayi?" Jakadiya tadanyi gyran murya sannan tace " gimbiya wannan fa inaga nufinsa daban, don sundade tare, inhar biyan bukata ne kinsan yarima yanayi sau daya zai shareta" falmata takara tsumuwa, batasan lokacin data mike tanufi fanninsa ba, dogarai suna kokarin yimata iso anma ko jiransu batayiba tafice tashigo, gabanta ne yayi mummunan fadi ganin yusuf yana zaune agefen aliya, da alamu yayi nisan tunani tunda baisan tashigo dakin ba, wani tsawa ta daka masa wanda saidaya firgita ganinta yasa yadanrusuna, bai idda ba tace "wani rashin hankali newannan? Jakadiya fita da ita!" Jakadiya taje ta tashi aliya wacce jikinta yayi zafi sosai tarasa yadda zatayi, donhaka taruketa zasu fice falmata tace "saketa!" Aikuwa aliya tajita akasa dasauri yusuf yanufeta yadagota zaifice da ita budan bakin falmata tace "zandaga maka nono yusuf, wlh inka kuskura kabita zandaga maka nono".
To be continue insha Allah.
Thanks to Benaxir for sharing with us, for more follow the link
Northern Nigeria (Arewa): Breaking News In Nigeria | Inside Arewa Blog Politics | Entertainment News |Fictional Stories | Lifestyle.
No comments:
Post a Comment