Saturday, 7 May 2016

Halaccin Sarauta episode 9

Continuation of Halaccin Sarauta Episode 8

Bilki tace "ran laraba menene?"aliya tace " babu kawai inason sanine" dadi taji ganin plans dinta yana tafiya daidai, Ran laraba dasafe tanufi gun dogari isa, shine wanda tasaba dashi sosai kuma tarokeshi alfarmar yanema mata kayan dogorai set daya, duk da yaso yakawo mata taurin kai. Dubi goman ta mint tahada tabashi,ba bata lokaci ya amince, donhaka ta karba tanufi baya tasaka tarufe kanta, tadauko fatar gemu wanda tayo guziurin kayanta tun daga kudu, tsayawa tayi a babban gate gurin da dole kayan sarakunnan sushigo, a tsayawanta tafara gadi, dogari isa ne agefenta abun mamaki dukka dogaran bawanda yace komi asalima basu nuna sunsan bakon fuska bane, hakan yatabbatar mata dacewa dogari isa yatoshe bakinsu, oh kudi samunka mutunci, rashinka balai, karfe daya daidai suka iso, matan sun shige yayinda kayansu dole aduba kamar yadda sarki ya umurta, ahaka aliya tagama cuse cusenta takulla komi sannan tacire kaya tabawa dogari isa, wanda tuni ya ajiye a boyeyyen gu don kar asiri yatonu, anshiga anyi iso ma matan sarautan harda mazajen nasu, lami lafiya anci abinci anyi tadi, anan aka fara fitar da kayan kowa ana dubawa, matan sarkin sun nua farincikinsu musammamn ma yakolo wanda don ita akadawo dazuwan laraba musababbin ciwonta, sarkoki ne, sai laces,shadoddi. Da kayan kwalama, can kasan wani shadda gezner jakadiya tana budewa sai ga laya da zobe, gaba daya hankalinsu yayi kan gun don sun mugun tsorata , jakadiya wacce ada take gudan farin ciki tana kirari saigashi tafara salati, tuni hankalim kowa yayi gun, umma uwar soro ce tanufi gun tareda cewa "kayan waye" jakadiya tace "na matan waziri" falmata wacce ta harzuka sosai tace "ku kamata" bashiri dogaran suka nufo kanta tareda bata hanyan fita, magana kaman iska tuni fada tadauki hayaniya waziri wanda ke fadar sarki jin abunda yafaru yasashi rudewa, bashiri ya roki da abarshi yashiga daga ciki, anma sarki yace mai " uwar soro zata mata hukuncin daya dace, babu ruwan fada ko sarki aciki". Falmata kuwa abunnema yasamu duka sosai matar waziri eshallo tasha, Adda Bena: Yakolo bataji dadiba acewarta yakamata ko darajan sarautan mijinta a lamunta mata, anma falmata taki , dadi takeji tasamu naman fansa akai, bakin ciki kaman zai kashe waziri anma babu yadda ya iya, uwar gayyan kuwa aliya taji dadi acewarta yanzu tafara daukan fansa, tunda yarabata da kowa nata saita rabashi dakowa nashi da duk wani wanda yasa hannu a kashe iyayenta, tana zaune bilki tashigo tareda cewa kizo inji yarima yusuf, shiganta tasameshi yana zaune da kwalban giyansa, da alamun maye, tuni tadaure fuska, yakalleta tare dacewa "kinga ko ni yarima ne, kuma kome nakeso ina samu, ina sonki kinji? "Aliya bata furta komi ba, kwace kwalban tayi tareda ajiyewa agefe. Kallonsa take sosai, yusuf namiji iya namiji saidai yasaka shaye shaye agabansa duk yayi baki yadawo wani iri, wannan wani irin rayuwa ne, itama zata iya amincewa kanta cewa tana sonsa saidai soyayya yanzu bashine solution dinba, gwara tadanne ranta tabi hakkinta tukunna, tajuya zata fice taji yana sumbatu, kwance akan kujera, zuwa tayi tagyra masa kwanciyan tadauko bargo tarufesa sannan tazura mishi ido gashin girarsa acike yake ga gashin akwance tamike zata fita taji yaruko hannunta, Kufara turowa adda bena da naman sallahnta.
To be continue....
Godiya ga benazir Umar for more follow @insidearewa on twitter

No comments:

Post a Comment