Aliya tanuna jin dadinta tareda cewa "barinje hotel din dana ajiye kayanna nadebo tukuna" dahaka suka danyi tadi aliya ta musu taaziya inda yakolo ta amsa, fitowa tayi tanufi fannin da aka kaita taroki bayin da su kira mata bilki don Allah sunji dadin ganinta suma dahaka suka kira bilki itama magana ce acike a bakinta, nan ta zayyana ma aliya cewa bawanda yasan waye , aliya ta tambayeta waye abokin da abdullahi ke shigowa dashi tace " oh dan gidan galadima marigayi ne , sunanshi sufyan, tun wancan satin yazo"
"Kisa masa ido! Sosai fa" "Toh" Suna rabuwa tafito tanufi gydanta tadibi kayanta na sati biyu hade da kayan sallahnta sannan tadawo fadan, tuni ta makale wa fannin yakolo tunda taji labari cewa sufyan da abdullahi suna yawan shigowa" tuni shakuwa tashiga tsakaninsu domma duk yaranta mata sunkoma makaranta saura abdullahi ne shehu ma bayanan, aikuwa an idar da sallah sai gasu sunshigo tana zaune akan kujera suma suka shigo abdullahi na ganinta yafara murmushi "aliya ce yau agydannan?" "Yarima na gaydaka" nan tajuyya takalli sufyan saida gabanta yafadi shima kallonta yake, kammaninsa daya da babanta, tabbas yayanta ne babu tantama ta amince, Allah mai iko anma yadda yayi ta tabbata bai ganeta ba, taji dadin haka donhaka sai suka gaysa sunadan tadi, yakolo tashige daki tabarsu inda sukasha hiransu sosai anan tadansan wasu abubuwan akanshi, nacewa ashe kasar waje aka tafi dashi tun primary yaje gun kanin babansu a cyprus anan yafara makaranta harya gama, jitakeyi kaman taje ta rungumi yayanta anma babu dama,koba komi tanada danuwan dazata kishingida ajikinsa idan tashiga damuwa, basu tafi ba sai karfe 10 sun sake sosai abdullahi ma baida matsala har cewa yayi washegari zasuje gun matar dazai aura takuma amince, , donhaka washegari dasuka shirya tashiga mota abdullahi na gefe sufyan na tukawa, suka isa yarinyan tanada kyau ga kamala da mutunci da dattako, tana kallom aliya da sufyan tace "anma kai yayanta ne ko? Kuna kaman sosai" gabanta yayi mummunan fadi bashiri taji sufyan yayi dariya yana cewa "tsabar soyayya ne muka dawo kama, budurwa tace fa" tace "awhh gaskiya kam, Allah bar soyayya"
Yabar aliya da tunani tuni shima abdullahi yafara tsokansu Yusuf yaje gidan aliya yaji shiru yabude da extra key dinsa anma duk dahaka baiganta ba, akwai kayanta donhaka saiyayi tsammani kotaje wani gurine ganin har karfe sha daya yatabbatar masa da bazata kwana a gida ba, aduk zamansa da ita baitaba jin takira sunan wani ko taje gun wani ba balle yayi tsammanin zataje, tuni yafara tunani lallema tayi sabon saurayi, tafita dashi kishi duk yabi ya turnukeshi dahaka yadawo, washegaru ma yakoma shiru bata dawi ba dayagaji yakoma shigowansa gida kenan yaganta tafito a mota tareda abdullahi dakuma sufyan, tunaninsa tadaure kayan jikinta yatabbatar masa da ba baiwa bace tadawo, toh metazo yi? Wannan yarinya da kwainane. Suna tafiya yakamota tabaya tajuyo tareda fuzge hannunta menene! "Mekikazo yi anan? "Meruwanka?" "Bazaki fadaba?"
"Ziyara nazo na sati biyu, kuma karka kuskura kanuna muna tare don zan dizga ka" Yayi mugun tsorata lalle yarinyannan munafuncinta ko sallah bayayi, Aliya da sufyan da abdullahi sun shaku sosai don ran sallah saidata fita tagansu suna hawa, duk da ta kalli masoyin nata wanda bakin ciki yasa yanzu yake shareta yakoma ruwa tsundum ba shan giyansa, Satinta biyu cif tasamu tahada duk wani info din dazata hada, ayadda taga sufyan bai ganetaba ita aganinta tagama dashi duk wani hanyoyinsa zata toshe, sunmata goma na arziki kafin ta tafi gydanta takoma ta zauna tana tunani tabbas yakammata tamike tsaye jin datayi abdullahi da sufyan suna magana a mota ya tsaya mata arai tagagara ganewa kuma " toh wanda bashida laifi ya mutu dalaifin wani" Sallah tayi takwanta acikin barci taji kaman ana shafa kafanta bude ido tayi mugun figita tayi don ganin wanda ke gabanta, sufyan ne sanye da kananun kaya, tajuya takalli dakin ta tabbatar dacewa ae gydanta nefa sannan ta kalleshi "sufyan mekazo yi anan?" "" hello little sister! Long time no see! Tazaro ido
To be continue insha Allah
No comments:
Post a Comment