Continuation of Halaccin Sarauta Episode 6
dogari ne yaleko nan da nan yusuf yace "kaita cell" wani wawan damka yamata tana fizgewa anma haka yafice da ita , rufeta sukayi a gun ,ko da falmata tayi cikiyanta domin taje tasawa abdullahi maganinshi anan tasamu labarin yusuf yarufeta, donhaka tuni ta nufi fanninsa fuska a murtuke tace "anma dai kasan cewa wannan baiwata ce ko?" Batareda yadamu ba yace "anma laifi tayi donhaka dole na hukunta ta" yana fada ya sunkuyar dakai" falmata tamike tareda cewa dogari "ciromin ita yanzunnan tazo tasamen" aikuwa ana cirota wanka tayi sanmam tanufi gun falmata wacce take kunshe da wasu kaya agabanta, laya ne dawasu kullin magani, jakadiya tamikawa aliya wacce bata tsorata ba, don duk takaranta a littafai salo salo na makirci da kishi, jakadiya tamika mata sannan falmata tacigaba da magana " zaki san yadda xakiyi kikai dakin yakolo, guda biyune naraba ko da zaasamu matsala da naki, gida biyu maganin gobara" aliya tamike tareda cewa toh, fitanta tanufi daki tana tunanin yadda zatayi saida tabari daredare sannan taje baya tagida tabinnesu, mikewanta dasafe tanufi fannin falmata tareda cewa "gimbiya bansan tayaya zanshiga fannin ta ba" falmata tace "nasan yadda zaayi kixo nan gobe dasafe" Washegari dasafe tajeta alokacin dukkansu daga falmatan har yakolo suna zaune suna karban gaysuwa saiga aliya, falmata na ganin aliya ta umurci jakadiya data kamota, duk sauran bayin dakatawa sukayi suna kallon ikon Allah don sunsan halin falmata sarai, jakadiya narikota falmata tahau fada wa aliya " baki da hankali ne? Tun karfe nawa nace kizo na aikeki? Ku bata jikinta!" Bashiri suka hau dirkanta yakolo ce tabata hakuri anma falmata taki saurarawa tunda aliya take bata taba shan duka irin wannan ba , ana gama dukantan falmata tace sukoreta, alokacin yakolo uwar tausayi kamar yadda mutane suke mata laakaci, tasa aka kawo aliya tabata uniform dinsu nacan sannan tace tadauketa aikin, shikenan plan din falmata yayi daidai, alokacin hauwa yarinyar yakolo ta tausayawa aliya sosai donhaka ta ce yakamata tana aiki acikin gurin ko da zamane agefe tadan taimaka dawasu abun, yakolo kuwa ta amince, fitowar aliya zuwa dakinsu tuni jakadiyar falmata tanufota tareda cewa "kinsam yanzu baza ana ganinki damu ba, donhaka kisan yadda zakiyi kibada maganin, akwai wacce muka bata sauran baizama dole kisantaba" dahaka aliya ta amince aanma akasan ramta tariga datasan tabirne maganin, saidai batasan wane aka bawa sauran maganin ba dazata san yadda zatayi tahana, anma duk dahaka bata cire hope ba, suna zaune watarana kawai saiga gimbiya tamike daga kan gado, tacire laqqabinta ta fizge gashin kanta, tuni tafara jan jikinta tana jan fatanta, hankalin kowa yatashi tuni aka isar da sako ga sarki, ya umurce da ariketa, sannan ayi addua ya iso gun dakanshi, yakolo tayi luf sai surutai takeyi " bakuga bera bane suke bin jikina? Duk dakina kananun bera, kutashi kuciremin ina jakadiya? Kiyi sauri kiciremin" aliya dake gefe kuka take kallon idon falmata tana ta kuka, oh ! Mata da kissa ita adole kishiyanta ba lafiya, can dai dataga sarkin yazauna agefe sannan tafara tafara magana "Allah sarki yakolo ta kiyi hakuri Allallah zai kawomiki dauki, Allah karemin ke,"daga ita har jakadiyan sai hawaye suke, abin yabawa aliya haushi yayin yakolo malamin yafara mata adduoi, wani zobe yagani a hannunta sannan yace tacire sarki dakansa yacire mata yamika masa, yakalli sarkin sannan yace "wannan zoben mai girma na tsafi ne, yawo ake da kurwanta asama,aina tasamo?" Sarki yakalli jakadiya maanan yana neman karin bayani jikinta nabari tace "nima haka nagani tana sawa bansan aina bane" dasauri hauwa tace "kawowa akayi alokacin gaysuwan sarakuna umma falmata tabata"falmata cikin kuka da kissa tace nima inadashi bantaba sawa bane. Acikin kayan sarakuna aka kawo(kayan sarakuna kyauta ne da matan sauran sarakunnan garin suke kawowa don hada zumunci kowa yakan hada nashi) sarki cikin zafin rai yace malam gama aikinka zamu binciko wayayi wannan danyen aikin,aliya taji dadin haka Koba komi zatasamu daman ganin matan waziri .
To be continue....
Thanks to Benazir Umar for sharing with us