Wednesday, 16 March 2016

JININ JIKINA Episode 2 March 16th 2016





Continuation of “JININ JIKINA Episode 2

Read Episode 1 here if you miss it

Umma ta kalleta tare dacewa Allah yashiryeki kikuma wuce kiyi alwala kiyi sallah. Tamike tsum tsum kamar munafuka. Tashiga daki tana jimami wannan rayuwa datasa kanta. Meyasa bata iya musu aduk lokacin daya umurceta tayi abu? Wani xuciyan tace mata saboda yazama jinin jikinki. Anma baikamata ali yamata abunda yakeyiba. Baikamata yayi wasa da soyayyartaba kokuma ya wulakantata haka? Nan tashare hawayen dayake zubo mata. Ummanta tashigo tazauna agefenta tadafe kafadanta tare dacewa nana inaso kinutsu kiyi tunani. Banhanaki ki so ali ba saboda ya cancanta kisoshi sai dai kisoshi hanya tsarkakkiya. Wacce bata fita a addiniba. Kokuma kishuka rayuwarki ta hanyan addini. Nana ta kalle mahaifiyarta tare dacewa nagode umma insha Allah zan canja. Nagode. Nan tacigaba dabata baki tare da nasihohi.
Bayan ta idar da sallan isha. Saiga yaro ya aiko wai akira mishi nana. Kamar bazatajeba tadai mike tafita tana isa zaure ta taroshi kanta a sunkuye. Yace sweety yaki kayi shiru? Ta girgiza masa kanta. Nan yazauna yafara bayani. Yanzu nasamu wani alhaji wallah zaki moreshi. Nan danan tabata rai. Aikuwa yafara masifa. Ke wai meke damunki ne? Daga miki magana kinyi wani ficifici da fuska kamar wacce aka mara, tagirgiza kai tare da zubar da makallalen hawayen da yake fuskan nata. Nanda nan hankalin sa yatashi. Yahau lallashi yi hakuri mana sweety meyasa kike haka wallahi inasonki. Kiyi hakuri please. Duk abinda nakeyi yazama min dole nayi banda wani uzurri. Kitaimaka min da Allah.
Ta kalleshi ido jajur. Uhm cewa fa kayi ba yanda ka iya. Yace eh. Anma karki tambayen. Takaleshi tareda cewa bakomi anma kana tunani . Yace tunanin kenan bazan taba cutarki ba. Tayi jim. Tare dacewa to shikenan sweety na zakije? Ta daga masa kai. Yamike tare da gyara mata gyalenta. Sukayi sallama tashiga gida. To wai ita abun daya dameta shine baya taba rike hannunta koyi mata wani abu. Anma shi ya iya kaiwa wasu. Toh wannan bayasontane? Tasan dai yana kishinta kamar hauka. Anma tanan fannin kwata kwata babu kishi. Taci kukanta takoshi tareda tunawa da mahaifinta. Allah kadai yasan inda yake ko awani hali yake ciki. Ahaka bacci ya kwasheta.
Washegari bayan tagama kimtsawa tadauki takalminta a hannu bayan ta waiga taga umman nata na karatun qurani. Ta zare dagwas dagwas tafice. Awani lungu suka hadu da ali. Tuni ya tsare musu abin hawa suka hau. Takaleshi yanayin data saba ganinshi aduk lokacin dazai kaita yauma shine aciki. Yanayi irin wanda zaace ko an tursasashine. Ko ansashi dole atakure yake. Gawani bacin rai dake lullube a fuskanshi. Tarasa meke mata dadi. Tadan bugashi da gyalenta sweety don Allah meyasa kake bata rai don Allah?. Kona bata maka raine?. Baice komaiba illa hararanta dayayi nandanan tajuya yayinda shikuma yajuya kansa gefe yana share kwalla, duk kokarinsa yadanna zuciyansa abin yafara fin karfinsa, anya zai iya cigaba da yin abunda yakeyi?. Wata zuciyar tace bayanzuba Sun isa inda zasu je. Nanyamikata kamar yadda yasaba yazauna zaman jira. Shi aduniyanshi na Allah worst moment nashi shine lokacin da zaibar nana ta kebe dawani. Anma yaya iya daransa?. Baida wata zabi data wuce yayi hakan. Fitowansu keda wuya aka sallameshi da kudin. Sunfito yakawota har gida yajuya yatafi.
Kwance yake adakimsa yana kallon ceiling Isa ne yashigo. Yatabashi shiru. Can yakuma tabashi shiru girgiza shidayayi yasashi dawowa hayyacinsa. Yamike tare da share kwalla. Tohfa aminina meye kake kuka?. Ali ya girgiza kai tareda cewa babu. Isa yace akwai mana. Ganin baida niyyan gayamishi yacigaba da cewaa. Dole bakin ciki ta isheka kamayar da yar mutane. Abin sanaa. Ali kaji tsoron Allah. Ali yakalleshi ido jajur tareda cewa da tsoronka zanji?. Tashi kafita min daki…
To be continue…






Feel Free To Comments Here...

No comments:

Post a Comment