Ahaka aka watse don barin yakolo tayi bacci, aliya tagaji sosai anma duk tana tunanin yazatayi don tasan tsafin da falmata tayine yake aiki, bata idda tunaninta ba taji hayaniya mikewa tayi tafice tafannin yakolo ne, dogaran basu bari ashigaa anma kasancewar sun wayeta suka barta, yakolo ce itakadai tanata hada kanta da bango, tana kuka duk jikinta jina jina, jakadiya dasauri tariko aliya tareda cewa kitsaya da ita barin yi magana da umma uwar soro, ficewanta aliya tanufi gimbiya yakolo wacce ganin aliya take cewa "aliya kirike matannan tadena rikemin kai, " aliya duk tarude dagudu abdullahi da hawa suka shiga hauwa tana zubar da hawaye, aliya cikin zafin nama take cewa "kina lailalaha illahala, auxubikallimatti lahi tammat min sharri ma kalaq" dasauri hauwa tafara fada aliya ma nafada abdullahi nafada, kara yakolo tasake tanacewa takamani sunayi dakarfi ahakan har tayi shiru tana nishi mai karfi, can tace " ga matan can tana kuka wai ina konata, kuma zata dawo takasheni" aliya tadebo ruwa ta tofa adduoi sannan ta watsa mata suka shafa mata ajiki, nan da nan bacci mai nauyi ya kwasheta, juyowan dazasuyi sukaga umma uwar soro tana labe agefe. Tana kallo ta tsorata sosai anma tace mutum biyu suzauna anan sauran sufice, hauwa da jakadiya ne suka zauna, alokacin aliya tafito domin tawuce dakinsu tana tafiya abdullah dake bayanta yace "baiwar Allah" tajuyo a hankali tareda sunkuyar dakai yace "nagode da taimakon mahaifiyata dakikayi, Allah bar zumunci," aliya tace ameen yarabb,tana tafiya yabita da kallo shidai yasan kaman yasanta awani guri anma dai yawuce dakinsa. Tana isa daki takwanta luff sai bacci Dasafe tafito dontaje mika gaysuwanta agun yakolo, dogarai ne suka tsaya akanta tareda nuna mata hanya tabisu baki alaikum har fannin yusuf, yana zaune akan kujera dagashi sai singlet ko a jikinta don ko lokacin training dinta mazan da singlet suke training ganin bata damuba yasan yana dealing da babbar yar bariki, cewa yayi danna zakimin!, zaro ido tayi anma ya katseta dacewa "kiyi ko na tona miki asiri.
To be continue...
Thanks to benazir Umar for sharing her story with us
No comments:
Post a Comment