Wednesday, 1 June 2016

Halaccin Sarauta episode 18

To read the previous episodes follow the
Inside arewa's Blog: Halaccin Sarauta episode 17

"So am the fool here" yadanyi murmushi sannan yace "Kinda" zama yayi agefen gadon yayinda itama tamike tazauna, "meyasa kika kasheshi? Kinsan hukuncin kisa?" Kallonshi tayi a harzuke sannan tace "meye zakawani ce nakasheshi? Sharri zakamin?" "Idan ba ke kika kasheshiba toh waye?, yayi daidai ma domin kuwa bashi yakashe baba ba!, bakuma sarki bane" zare ido tayi jin yace bashi yakasheshiba , sannan jin kuma bashi yakashe mahaifinsu ba toh waye? , "keda kike zaune anan fiye da watanni ni acikin sati nazo nasamu labarin dakika garara samowa,"

"Yoo toh ai kai namiji ne ka manta? Zaka iya shiga ka fita duk inda kakeso, nikuwa mace inada limits," "ba abunda ke tafe dani ba kenan, gidannan zaki tattara kibarshi acikin satinnan, kikoma gydan inna nagayamata zaki koma,kina ya'mace kina zaune ke kadai, in wani abu yafaru fa, kinje kin koyo halin yahudawa," "Nifa zaka takuramin wallahi, kaida kaje can wani bariki ne baka koyo ba, angayamaka bana lura dakai da abdullahi ne? Kuma akanme zanje gun inna? Nasan da ita ai naki zuwa" "So kike kizauna saboda wannan katon yusuf din yana zuwa kuna rufe daki kubiyu ko? Mekuke ayyanawa?" "Awhhhsh yayah kanada zato, nifa ba abunda yataba hadani dashi!" "Ki rantse baitaba rike yatsanki ba" "Ae baitaba ba" tana fada tana murkuda baki, hannu yasa ya riko kunnenta tareda cewa "ko ki tattara ko namiki duka" "Wayyo yayah sakemin kunne zafi," yasake tacigaba da murguda masa baki tana tattare wayoyinta "nikam ka fita wallahi, duk kazo ka takurani"

"Ba inda zanje, ki zauna ki sauraren, waziri baya gari lokacin da akayi kisan baba, wanda hakan yana nuna baisan da labari ba, alokacin yaje taaziyan mahaifin matarsa, dole mukara tsananta bincike," "Toh naji katafi sai anjima"

Mikewa yayi yafice tareda murmushi rufo kofan tayi, tazauna tana tunani tasan yadda yafara maganan nan bazai barta ba saiyasamu biyan bukata, duk yana nema yatakurata tana zaman lafiyata, yusuf ne yashigo fuska a murtuke ganin yazauna bai kulataba tace "meye kashigomin kaman gunki" Bai kulataba sai haki dayakeyi ganin zai bata mata lokaci tadauko jakanta sannan tafito harzata wuceshi yamike yarufo kofar, ganin yatsaya kaman gunkin gasken, ta harzuka sosai tabugeshi da zummar tawuce hannu daya yasa ya bangeta, saigata a kan gado, yakoma yazauna akan kujera sannan yafara "Aliya kinsan inasonki, kuma bana danganta soyayyanki dakomi, aliya meyasa kike min haka? Meye tsakaninki da sufyan yanzu naga yafito daga gydannan? Dama dalilinki nazama a fada kenan don ku shaku dashi? Meyasa kike haka aliya? Kina wahalar min da zuciya" Dariya tayi tareda cewa "sufyan fa kace," Mikewa yayi yabuga table din dake gabansa dakarfi sannan yafice binshi tayi da kallo don mamaki take harta mike tafito saigashi yadawo rike kanta yayi dakarfi, yaki sakewa, gashinta nazafi tanacewa "yarima ka saken, dazafi nace kasaken.

To be continue insha Allah

No comments:

Post a Comment