Wednesday, 23 December 2015

"NIMA MACECE" Episode 1 12th dec 2015



Cikin takun kasaita ta isa bakin motan wanda guard dinta har yabude tashiga gidan baya yabi yarufe motan tabar harabar kafteren gidan, grand square suka nufa, yayinda tafito mazan biyu wanda suke matsayin guards dinta suke biye da ita ta isa bakin kofan inda guards din gurin suka bude mata kofa tashige jakanta na hannun guard dinta wanda yake biye da ita cikin bakaken coats sanye take da jan dogon riga mai duwatsu a jiki dinkin fitet ne yafitar da shape din jikinta kaman wanda aka yi dokinta kana ganin rigan kasan dollars yaci uwashi agun!!, Da takalminta high heel lafiyayye baki, saita daura bakin gyale shima akwai designs ajiki, sanye take da glass a fuskanta wanda ta manna shi yayi bala'in mata kyau.

  Doguwa ce mai kirar 'kalangu' zaki iya cewa coca cola shape kalan fatanta yafi kama da black americans very fresh, tana da dogon hanci wanda yafado daidai karamin bakinta, wanda fararen hakuranta suna jere cas aciki, manyan ball eyes dinta farare tas wanda bakin glass din bazai hanaka ganin su ba. Taku take cikin kasaita wanda zakayi tsammani ko tayi makarantan koyon tafiya.
Dayan guard dinta shine yadauko basket yana binta dashi tana diba tana jefawa har suka kammala takarbi jakanta tabiya kudin suka fito.
Guard din yace Ma! Ina zamuje? Ta juyo da fiskan agogonta taja tsaki sannan tace muje gida kawai. Hakan kuwa akayi suna isa gida batako kula da kayan ba tahaura sama. Kafteren gida ne wanda tsayawa yin bayani zai bata mana lokaci, mai karatu saika kisfaya dakanka.
Kafteren dakinta tashiga hayewa kan katon gadonta tayi wanda akalla mutane 12 zasu iya kwana akai ba takuri, batare da ta cire takalminta ba ta kwanta tana nishi kaman wacce tayi noman sati ba hutawa.
 Wayanta ne yayi kara tamika hannu taciro ajaka takara a kunnenta 'Hi Momy!  Mamantan tace kizo daki kisameni. Tace tom. Batare da bata lokaci ba tafice tafiya tayi mai tsawo kafin ta iso wani falo yahadu iya haduwa tabude tana shiga taga wasu a zaune yayinda momyntan agefe itama, Tanemi wuri tazauna batare da ta cewa bakin uffanba. Momy gani. Maman nata ta kalleta sannan tace ina kikaje? Tace shopping, Okay. To ga wadannan zaki kaisu office din dad dinki yace akwai aikin dazakiyi. Tajuya don taga suwaye.
 Maza ne biyu akalla bazasu wuce 30-32 ba. Tamike sannan tace kubiyoni, mota suka shiga tasa su a mota itama tashiga nata akaja suka nufi 'FAWU' Resources Orientation
'Basant ibn Fawu' Ya ce kwaya daya tilo agun attajirin mai kudi wanda akasanshi da sana'an sayar da petur da gwalagwalai, Alhaji Ibrahim fawu, dakuma mahaifiyarta Hajiya Aisha wacce ake kira Adda. Kasancewarta ita kadai yasa iyayenta suka dauki son duniya suka daura mata, anma hakan bai hanasu bata tarbiya na gariba! Tayi makarantan ta a turkish abuja. Yayinda ta tafi UK Takarasa makarantanta, kasancewar tafara makaranta dawuri hakan yasa tagama dawuri tana da shekaru 23 tana rike da qualifications na degree dinta na petroleum engineering!. Wanda tayi hakanne don ta dawo tasa hannunta a business din mahaifinta.

*** Bude kofan tayi tare da sallama tana mai cewa: "Dad"... Zaune taganshi da files agabanshi yadago yana murmushi my dota ya akayi?. Ta ce dad kalau munmy ce tace kana nemana sannan akwai wasu tace mutaho tare. Dasauri yace yes inasuke?. Tamike tafita jim saigasu sunshigo tare. Bayan sun zauna dad dinta yake sanar da ita yayan bappanshi zasu zo sufara aiki dasu, tace okay badamuwa. Office dinta tashiga tazauna minti kadan tamike tafito tace kuban key din motan zanje nadawo yanzu, suka bata tafita da niyyan shakatawa.
Tuki take hankalinta akwance daga ganinta kasan irin matan dabasu da damuwa ne. Wani hanya tagani wanda daka gani baa wucewa ta kusa kai batare da damuwan ina zata shiga ba. Tayi nisa a hanyan a tsammaninta bawani gubane anma saitaga hanyan yaki karshe. Birki ta ja, dataga wasu mutane azaune agun daga gani yan dabane ko yan kwaya. Tajuya zata tafi anma tayi latti domin suntaho dasauri sunyi banke- banke akan titin dazata wuce suna masu nunamata bindiga. Dayan yace gaskiya munsamu saa ayau. Dotan fawi guda gaskiya zamuci kudi! Bindiga suka dura akanta inkikayi motsi zamu harba miki! Cikin rawan jiki da tsananin kidima tare da kuma razana ta girgiza kai alamun taji. Motansu suka sakata. Wani towel dayan ta tusa mata ahanci wanda tayi bacci bashiri. Kash munzo karshen kashi na daya, a biyo mu sati mai zuwa domin cigaba. Add 08066680993 for more updates and other stories on whatsapp. Feel free to comment below thanks.

2 comments:

  1. Replies
    1. It is a well-known fact that Illuminati consist of Multi Millionaires,
      Billionaires who have major influence regarding most global affairs,
      including the planning of a New World Order. Many world leaders,
      Presidents, Prime Ministers, royalty and senior executives of major Fortune
      500 companies are members of Illuminati. join a secret cabal of mysterious
      forces and become rich with boundless measures of wealth in your company or
      any given business, the great Illuminati can make everything possible just
      contact : join666cult@gmail.com or WhatsApp +1(646)481-0376 EL
      IAI LEXION Thaddeus Iam Vice-President of Citizen Outreach THE ILLUMINATI
      ORGANIZATION

      Do not hesitate to contact us by WhatsApp.

      Whatsapp: +1(646)481-0376
      Email : join666cult@gmail.com

      BEWARE OF SCAMMERS, THERE IS NO SUCH THING AS REGISTRATION FEE AND YOU MUST
      BE ABOVE THE AGE OF 18YRS.
      THANKS...

      Delete