Tuesday, 12 June 2018

Shugabannin Yarbawa Na Ci gaba Da Jinjinawa Buhari Kan Baiwa Abiola Lambar GfCR

▪ Dole In Yiwa Buhari Yakin Neman Zabe A 2019 — Tinubu

▪ Buhari Ya Amince Da Baiwa Wasu 'Yan Siyasa Lambobin Yabo

Shugabannin Yarbawa na ci gaba jinjinawa Shugaba Muhammad Buhari bisa matakin da ya dauka na baiwa Marigayi M.K.O Abiola Babbar lambar girmamawa ta kasa wato, GFCR a yau a ranar 12 ga watan Yuni wadda rana ce da aka soke zaben Shugaban kasa da marigayin ya lashe a 1993.

Tuni dai, Tsohon Gwamnan Legas, Bola Tinubu ya tabbatar da cewa wannan mataki da Buhari ya dauka na girmama Abiola ya sa dole ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa Buhari yakin neman zabe a shekarar 2019 inda ya nuna yin haka girmamawa ce ga daukacin Yarbawa.

Shi kuwa dan fitaccen lauyan nan Marigayi Gani Fawehenme wanda shi ma ya samu lambar girmamawa duk da yake a lokacin yana raye ya ki karbar lambar, Mohammed Fawehenme ya nuna cewa babu wani Shugaba a tarihin Nijeriya da ya san abin da ya dace irin Shubaga Buhari.

Haka nan kuma Shugaba Buhari ya amince da baiwa wasu Fitattun 'yan siyasa da suka taka rawa a dimokradiyyar Nijeriya lambar girmamawa. Da yake tabbatar da haka Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustafa ya ce nan bada jimawa za a fitar da sunayen wadannan 'yan siyasar

Shugaba Buhari ya yabi matasan Najeriya a ganawar da yayi da firaiministan Morocco

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gana da firaministan kasar Morocco, Saadeddine Othmani, inda ya shaida mishi cewa mutanen Najeriya, wanda yawancin su matasa ne suna da kokarin aiki tukuru duk inda suka samu kansu a gida Najeriya ko a kasashen waje.

Shugaba Buhari ya kara da cewa shi yasa gwamnatin shi take kokarin ganin ta tallafawa matasan dan su bayar da gudummuwar data dace wajan ciyar da kasar gaba,

Ya kara da cewa Najeriya na kokarin ganin ta inganta harkokin Ilimi dana noma ta hanyar yin hadaka da kasashen Duniya wajan tabbatar da hakan.

Ya bayyana cewa an samu raguwar shigar da shinkafa kasar sosai, sannan kuma hadin gwiwar da Najeriya tayi da kasar Moroccon yasa kudin takin zamani ya ragu da kashi hamsin cikin dari.

Da yake jawabi a ganawar tasu, Firaiminista, Saadeddine ya bayyana cewa 'yan Morocco sun tabbatar da 'yan Najeriya nada hazaka dan sun gani a kasa, sannan kuma zasu cigaba da tabbatar da dangantaka me kyau da Najeriya.

Shugaba Buhari ya kuma gana da shugaban masu bayar da shawara akan harkar kasuwanci na kasar ta Morocco Ben Chemmas da kuma shugaban majalisar wakilai Habib El-Malki.

'Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum 8 a arangamar da 'yan baranda su kayi da 'yan banga a Sakkwato

Hukumar Yan sanda reshen Jihar Sakkwato ta tabbatar da rasuwar mutane takwas a wata rikici da ya barke tsakanin yan baranda da yan banga a jiya Litinin a karamar hukumar Isa da ke Jihar Sakkwato.

Jami'ar hulda da jama'a ta rundunar, Cordelia Nwawe ta shaidawa yan jaridar cewa ana kyautata zaton mutane takwas ne suka rasu ciki har da wani dattijo da yan barandan su kayi kokarin sacewa.

Mrs.Nwawe ta kara da cewa har yanzu ana cigaba da gudanar da bincike a kan lamarin, ta kuma ce ana kyautata zaton yan barandan sun zo ne daga kauyukan jihar Zamfara da ke makwabtaka da Sakkwato.

Ta kuma ce kwamishinan Yan sanda na jihar ya ziyarci kauyen da abin ya faru don yin jaje ga iyalen wadanda abin ya shafa tare da tabbatar musu cewa yan sanda za su binciko wadanda suka aikata wannan laifin.

Sai dai a wani rahoton, an ce mutane 13 ne suka rasu sakamakon yunkurin da yan barandan su kayi na sace wani dattijo ranar Asabar a kauyen Dan Tasango a Gundumar Gebe.

A cewar wani ganau, yan barandan sun harbe dattijon ne saboda ya ki yarda su tafi dashi, hakan ne yasa yan bangan garin suka hada kai don bin sahun yan barandan.

Majiyar ta cigaba da cewa 'yan barandan sunyi wa yan bangan kwantar bauna a hanyar Kamarawa-Barafawa inda akayi musayar wuta inda yan barandan suka kashe yan banga bakwai su kuma aka kashe musu mutane biyar.

Sai dai yan barandan sun kwace gawawwakin mutane biyar din da aka kashe musu kamar yadda suka saba saboda kar a gane kosu wanene.

Monday, 11 June 2018

Matashi Ya Yi Wa Budurwarsa Yankan Rago A Jihar Yobe

Ana zargin wani matashi dan garin Potiskum dake jihar Yobe mai suna Muhammad Isa Adamu da yi wa budurwasa mai suna Hauwa yankan rago.

A bisa bayanan da iyayen Hauwa mazauna garin Damaturu suka yi, sun ce a ranar 29/05/2018 Hauwa ta fita da safe da niyyar sayo biredi a shago mafi kusa da su, sai dai tun daga fitar ta ba ta dawo ba har zuwa yammaci, wannan dalilin ya sa suka bazama nemanta, yayin da suka bada cigiyar ta a gidajen rediyo da ma wajen 'yan sanda.

Kwatsam sai suka ji an samu gawar wata budurwa a kan titin Gujba, inda ba su yi kasa a guiwa ba zuwa wurin inda suka tabbatar da 'yarsu ce.

A yayin da wannan matashi yake karin haske akan abun da ya faru, ya shaidawa manema labarai a garin Damaturu cewa, ya gayyaci Hauwa tsohuwar budurwarsa wadda ya fara nemanta tun 2014, soyayyarsu tayi nisa sosai, kuma bai taba sa ta wani abu ta ki yi ba, ya tabbatar da irin biyayya da Hauwa take masa, wannan dalilin yasa da ya gayyace ta kan hanyar Gujba, ba ta yi masa jayayya ba.

A cewar sa, bayan sun gama hirar su da Hauwa, sai ya umarce ta da ta rufe idonta, ba ta yi jayayya ba nan take ta rufe idon ta ba tare da ta san me yake shirin yi mata ba, sai ya ciro wuka ya soke ta a wuya, bada wani bata lokaci ba rai ya yi halinsa.

Da aka tambaye shi ko mai ya yi zafi har ya yanke wannan danyen hukunci ga wadda yake so?

Sai ya ce, ya yi iya kokarin sa don ganin mahaifansa su je Damaturu su nema masa auren Hauwa amma sun ki, kwatsam sai ya ga wani matashi ya fara zuwa wajen ta, wannan dalilin ya sa ya yanke hukuncin kashe ta kowa ma ya rasa.

A bisa bayanan da kwamishinan 'yan sanda na jihar Yobe ya yi wa manema labarai, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma yi alkawarin nan bada jimawa ba za su gurfanar da wannan matashi gaban kotu dan yanke masa hukunci.

Barazanar Tsige Buhari Ta Jefa Dogara Cikin Jangwan

Shugabanni jam'iyyar APC na mazabar Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara sun cimma matsaya na maye gurbinsa da wani sabon dan takarar mai suna Godfrey Mannaseh bisa abin da suka kira adawar da Dogara ke yi da Buhari da kuma Gwamnan Bauchi.

Shugabannin uku, Haruna Rikaya, Malam Zubairu da Wakili Amadi sun nuna cewa Shugaban majalisar wakilan da na hannu kan barazanar da 'yan majalisar suka yi kwanaki na tsige Shugaba Buhari inda suka jaddada cewa ba irin wakilcin da suka tura shi ya yi masu ba kenan.

Shugaba Buhari Da Sarkin Moroco Sun Kulla Alaka Kan Harkokin Man Fetur, Gas Da Sauransu

Shugabannin biyu sun tattauna da kuma cimma yarjejeniya na karfara tattalin arzikin kasashen biyu.

Wadanda suka rattaba hannu kan wannan yarjejeniya sune Manaja a kamfanin NNPC, Mr Farouq da kuma ministan man kasar Moroco, Misis Amina Benkhadra

Haka kuma shugaba Muhammadu Buhari da Sarki Muhammad VI sun shaida yarjejeniyar gina babban masana’antar hada sinadarin takin zamani wato Ammonia, wanda shugaban sanya hannun jarin Nijeriya, Mista Uche Orji da Mista Mostafa Terrab na Moroco suka rattaba hannu.

An Nemi Buhari Ya Binciki Yadda Obasonjo Ya Mikawa Kamaru Yankin Bakassi

An Nemi Buhari Ya Binciki Yadda Obasonjo Ya Mikawa Kamaru Yankin Bakassi

Tsohon Gwamnan Abia, Orji Uzor Kalu ya nemi Shugaba Muhammad Buhari kan ya binciki Cif Olusegun Obasonjo game da yadda ya mikawa Kasar Kamaru yankin nan mai arzikin man fetur na Bakassi .

Tsohon Gwamnan ya ce, akwai wata manufa ta biyan bukata kansa idan aka yi la'akari da yadda Obasonjo ya mika yankin cikin sauki ba tare da wata jayayya ba.