Monday 30 April 2018

A Karshe Kotu Ta Damka Wasu Gidajen Patience Jonathan Ga Gwamnati




Wata kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta damkawa gwamnatin tarayya wasu gidaje guda biyu mallakar Uwargidan Tsohon Shugaban Kasa, Patience Jonathan.
Rahotanni sun nuna cewa dukkanin gidajen guda biyu suna cikin Babban birnin tarayya Abuja ne wadanda aka mallake shi da sunan gidauniyar Ariwabai Aruera Reachout wadda Patience Jonathan ta kafa a zamanin mulkinsu.

Friday 27 April 2018

Manoman Jihar Neja Ta Arewa Sun Samu Horo Akan Dabarun Noma Na Zamani

Taron bita da karawa juna sani akan sabbin hanyoyin dabarun noma na zamani ga manoman yankin Neja ta Arewa da sanata mai wakiltar Jihar Neja ta Arewa kuma mai magana da yawun majalisar dattijan Najeriya Dr. Aliyu Sabi Abdullahi (Baraden Borgu) ya shiryawa manomar yankinsa tare da hadin guiwar hukumar bunkasa harkar noma na jami'ar Obafemi Awolowo.

Taron bitar na yini biyu da ya gudana a dakin taro na hukumar gidan gona na Kontagora yasamu halartar manoma daga kananan hukumomi 8 dake yankin inda manyan masana harkar noma daga jami'ar Obafemi Awolowo suka gabatar da lakcoci daban-daban ga manoman, tare da koyarwa na zahiri ga manoman.

Hakazalika anbaiwa manoman tallafin irin masara da dawa na zamani tare da tallafin naira dubu ashirin da hudu ga wadanda suka halarci bitan domin bunkasa harkar noma a yankin Neja ta Arewa da Kasa baki daya.

Ko a shekarar da ta gaba ta ya dauki nauyin shirin karawa juna ilimi ga malammai 125 wanda ya gudana a Safara Motel Kontagora tare da basu tallafin naira dubu talatin-talatin, sannan a wannan shekarar ya dauki nauyin karawa juna sani ga malamai 130 wanda ya gudana a garin New Bussa tare da basu tallafin dubu talatin talatin.

Bayan haka shirya shirin bada taffalin jarin sana'o'i na musamman ga mata 95 wanda ya gudana a Safara Motel Kontagora tare da basu tallafin naira dubu talatin-talatin, hakazalika ya sake shirya makamancin wannan horas wa a garin New Bussa.

Bangaren matasa ya daukin nauyin horar da matasa 100 daga kananan hukumomi 8 dake yankin sa a kwalejin koyon kiwon kifi tare da basu tallafi.

Majalisa Ta Nemi A Kafa Dokar Ta- Baci A Binuwa


▪ Ana Ingiza Rikicin Binuwai Ne Don A Raba Nijeriya — Buhari

Majalisar Dattawa ta kalubalanci Shugaba Muhammad Buhari kan ya kakaba dokar ta-baci a jihar Binuwai don ganin an kawo karshen zubar da jini da ake yi sakamakon rikicin makiyaya da manoma.

A nasa bangaren, Shugaba Buhari ya jaddada cewa masu Ingiza rikicin jihar Binuwai na neman wargaza Nijeriya inda ya gargadi al'ummar jihar kan su yi takatsantsa da makiyan kasar nan wadanda ke ingiza su kan kashe junansu.

Mai Magana Da Yawun Gwamnan Sokoto, Imam Imam Ya Rasu


Allah Ya yi wa Malam Imam Imam rasuwa da sanyin safiyar yau Juma'a bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.

Shi dai marigayi Malam Imam Imam shine mai  magana da yawun Gwamnan jihar Sokoto Rt Hon Aminu Waziri Tambuwal.

Matasan Kiristoci Sun Kashe Musulmai 27 Tare Da Kona Masallatai Biyu A Jihar Binuwai

Rahotanni sun nuna cewa akalla mutum 27 ne aka kashe, yayin da wasu da dama suka jikkata a rikici na baya-bayan nan a Makurdi, babban birnin jihar Benue.

An kuma kona masallatai da kuma hasarar dukiya a harin wanda ake zargin na ramuwar gayya ne da ake zargin 'yan kabilar Tivi da kai wa Hausa/Fulani.

Wadansu da suka ga lamarin sun shaida wa BBC cewa wadansu gungun mutane ne suka "tare hanyoyin cikin gari tare da tsare mutane, inda suka rinka kashe su."

Rundunar 'yan sandan jihar ta ki cewa uffan kan bukatar da BBC ta mata na yin magana kan lamarin. Shi ma sakataren yada labaran gwamantin jihar, Terve Akase, ya ce ba shi da labarin harin.

Sai dai wani Basarake na kabilar Tivi, wadanda aka zarga da kai harin, ya ce suna iya kokarinsu domin ganin ba a kai hare-haren ramuwar gayya ba.

Wani dalibi da ya shida lamarin wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce da idanunsa ya ga yadda gungun mutane suka "tare hanyar zuwa jami'ar garin kusa da wani asibiti suna tare mutane su doke su, kana kuma kuma su yi musu kwace sannan su kashe su."

Dalibin ya kara da cewa "Hausawa ne ko Musulmi ake yi wa hakan."

Shi ma babba limamin masallacin Izala na birnin, Sheikh Shu'aibu, ya shaida wa BBC cewa, da idanunsa ya ga "gawawwakin Musulmi da aka kashe 27" a asibitin koyarwa da ke birnin.

Limamin ya ce an ji wa wadansu "Musulmin rauni da dama," ba ya ga wadanda ba a gansu ba kuma.

Sheikh Shu'aibu, ya ci gaba da cewa, an "kona wadansu masallatai guda biyu" wadanda aka gyara su bayan an kona su a rikicin baya.

Sheikh Sha'aibu ya ce yanzu dai abin ya dan lafa, kuma dama lamarin dai yafi kamari ne a wajen birnin.

To sai kuma shugaban kabilar Tivi, Tar Makurdi Chief Sule Abenga, ya shaida wa BBC cewa:

"Na san cewa akwai zaman dar-dar a Makurdi, tun bayan da aka kashe wadansu limaman coci da wadansu Kiristoci, alamu suka nuna cewa za a iya daukar fansa,"

Ya ci gaba da cewa: "amma mun yi bakin kokarinsu don tabbatar da ganin hakan bai faru ba. Kuma shi bai san cewa mutanensu na aikata irin wannan ta'asa ba."

Matashiya.

Wannan zaman dar-dar din ya samo asali ne tun a ranar Talatar da ta gabata lokacin da ta bayyana cewa wadansu 'yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun shiga wata majami'a a wani kauye karkashin karamar hukumar Gwer.

Maharan sun kuma bude wuta irin ta kan mai uwa da wabi, al'amarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 17 ciki har da limaman coci biyu.

Rikicin manoma da makiyaya dai a Najeriya ya yi sanadin asarar rayuka daga dukkan bangarorin biyu.

Rikicin ya fi kamari ne a jihohin Filato da Benue da Taraba da Nassarawa da Kaduna.

A baya gwamnatin tarayya ta yi kira ga gwamnonin jihohin da lamarin ya shafa su samar da wuraren kiwo.

Sai dai gwamnonin sun yi fatali da wannan bukata, suna masu cewa ba su da isassun filayen da za su bayar.

Friday 20 April 2018

Kisan Soja Ya Janyo Kona Gidaje 300 A Binuwai

Wasu sojoji sun kai wani mummunan hari a garin Naka da ke cikin karamar hukumar Gwer a jihar Binuwai inda suka kona gidaje har 300 sakamakon kashe wani soja da aka yi a kusa da garin.

Shugaban Karamar Hukumar, Francis Ayagah ya ce, wasu kangararrun matasa ne suka kashe Sojan kuma mazauna garin sun kama mutum biyar daga cikinsu bayan an yi zama da Kwamandan sojojin amma kuma kafin a mika su sai kawai sojojin suka kai farmaki. Ya kara da cewa mafi yawan gidajen da aka kona ba na wadanda ke da hannu wajen kisan Sojan ba ne.

An Fatattaki Wuraren Sayar Da Barasa Da Gidajen Karuwai A Jigawa

Biyo Bayan Zaman Kwamitin Kula Da Harkokin Tsaro Na Karamar Hukumar Hadejia Da Kuma Zaman Majalisar kansiloli Na Karamar Hukumar Da Aka Gudanar A Jiya Alhamis, Kwamitin Tsaro Na Karamar Hukuma Ya Karbi Koke-Koken Al'ummar Daban-daban Musamman Mutanen Dake Zaune A Unguwar Mai Randa Dake Kan Hanyar Kano Cikin Garin Hadejia, Dangane Da Yadda Wasu Tsiraru Suka Mayar Da Yankunan Matattarar Gidajen Siyar Da Barasa Da Bude Gidajen Mata Masu Zaman Kansu.

Sakamakon Karbar wannan Koke Da Yadda Hakan Ke Yin Barazana Da Zaman Lafiyar Al'umma Hadi Da Yinn Karan Tsaye Da  Addini Da Al'adun  Karamar Hukumar Hadejia.

Majalissar Kansilolin Karamar Hukumar  Bisa Jagorancin Kakakin Majalisaar Hon Dawaki Baffa, Hade Da Majalissar Harkokin Tsaro Na Karamar Hukumar Sun Zartar  Da Dokar Hana Sayar Da Giya A Dukkan Fadin Karamar Hukumar  Tareda Gidajen Mata Masu Zaman Kansu.

Inda A Yau Majalissar Kula Da Harkokin Tsaro Na Karamar Hukumar  Hadejia Wadda Ya Kunshi Shugaban Karamar Hukumar, Da Mataimakinsa,  Rundunonin Tsaro Na Yan sanda, DSS, Hisbah, Civil Defence, Immigration, Prison Service, Jamian Sojoji, Vigilante Dasauransu.

Sannan Kuma da Dukkannin Majalissar kansilolin Karamar Hukumar, Sukayi Tataki Zuwa Wannan Gidaje Dake Unguwar Mai Randa, Wajen Kulle Dukkannin Wannan Gidaje Na Sayar Da Giya Da Aiyukan Badala.

Hukumar 'Yan Sanda Ta Yi Wa Magu Karin Girma

Hukumar 'yan sanda ta kasa, a yau Juma'a ta sanar da karin girma ga manyan jami'an 'yan sanda 18.

Shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu na daga cikin wadanda aka karawa girman.

Hukumar ta kara masa girma ne daga matsayin mataimakin kwamishanan 'yan sanda zuwa kwamishana.

Idan za a iya tunawa, shugaba Muhammadu Buhari ya nada Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar EFCC domin yaki da cin hanci da rashawa. Amma duk da hakan, majalisar dattawa ta ki tabbatar da shi bisa wasu dalilai nasu.

Wannan sabon karin girma da aka yi wa su Magu,na kunshe ne cikin jawabin kakakin hukumar ta 'yan sanda, Ikechukwu Ani.

Thursday 19 April 2018

Mutane Da Yawa Ba Su Fahimci Kalaman Shugaba Buhari Ba, Musamman Wasu 'Yan Arewa

Daga Comrade Affan Buba Abuya Gombe

Abun da Buhari yake nufi a fahimta ta, Matasa da yawa a yankin da ake tono mai suna zaman jiran a ba su kudi ba tare da sun yi aikin komai ba saboda a yankin su ake tono mai kamar yadda yanzu haka ake kashe biliyoyin kudi a wannan yanki ga wadanda basa aikin komai ba sa yiwa kasa wani katabus.

Da yawan su matasa ne masu zaman banza kuma ko karatu ba suyi ba, jira sukeyi a basu kuma wannan hali ba zai taba daurewa ba, ba zai taimaki tattalin arzikin kasa ba da rayuwar matasa a gaba.

Domin tabbatar da haka kaje garin ku cikin anguwanku zakaga yanda matasa suke zaman banza, ba karatu, ba sana’a kuma suna so suyi kudi sai KJK da shaye shaye da zama yan kalare sukeyi ko sara suka wasu gurbatattu suna amfani dasu a siyasa.

Muna tare da kalaman Shugaban Kasa Buhari, Allah ya shiryar mana da matasan mu.

Gwamnatin Jihar Kaduna Za Ta Kara Daukar Malaman Firamare Guda Dubu 13,665




Gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Malam Nasiru Ahmad El Rufa'i, ta shirya tsaf domin sake daukar kwararrun Malaman Firamare 13,665, a wani shiri na kara inganta harkar ilimi a fadin jihar.
Kwamishinan Ma'aikatar ilimi ta Jihar Alhaji Ja'afaru Sani ya bayyana hakan, a yayin wani taron manema labarai da Ma'aikatar ta kira a ranar Larabar nan.

Rundunar 'Yan Sandan Neja Ta Kama Gaggan Barayin Da Suka Addabi Jihar



Daga Comrade Zakari Y Adamu Kontagora
A kokarin kawar da aiyukan ta'addanci bisa ga umarnin babban sufeton 'yan sandan Nijeriya Ibrahim Idris, rundunar 'yan sandan jihar Neja ta yi nasarar kama wasu gaggan masu laifi da suka hada da barayin shanu, masu garkuwa da mutane, barayin motoci, fyade, da wadanda suka mallaki bindigogi ba bisa ka'ida ba.
Rundunar tayi nasarar kama wadanda ake zargin ne a wani kwarya-kwaryar samame da ta gudanar a kananan hukumomin, Suleja (Madalla), Mashegu, da Tafa inda ta kama mutum 19 tare da makamai a hannun su, kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan na Jihar Neja Abubakar Dan Inna ya tabbatar.
Daga cikin wadanda ake zargin sun hada da Ali Muhammad dan garin Sawmil a karamar hukumar

Za Mu Sa Kafar Wando Daya Da Masu Cin Zarafin Mutane Masu Mutunci A Kafafun Sadarwa, Inji Rundunar 'Yan Sandan Kano


Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce za ta sanya kafar wando daya da ma'abota shafukan sada zumunta wadanda suke cin mutumcin jama'a da yin kalaman tayar da tinziri.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, SP Majia, yace rundunar ta shirya tsaf wajen magance wannan matsala, inda ya ce sam ba daidai bane wasu tsirari su ringa amfani da wannan kafa wajen yin batanci ga masu mutunci ba, yace wasu na amfani da wannan kafa wajen zagin malaman addini da shugabanni ta hanyar hada hotunan su da matan banza ko dabbobi da yin zantukan da basu kamata ba.

An Gano Sandar Iko Na Majalisar Dattawa Da Aka Sace


Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta bayyana cewa ta gano sandan iko na majalisar Dattawa wadda wasu 'yan daba suka sace a lokacin zaman majalisar a jiya Laraba.

Wednesday 18 April 2018

Jiragen Yakin Nijeriya Sun Yi Luguden Wuta A Kan Mayakan Boko Haram


Jiragen yakin Amurka sun yi luguden wuta a kan wasu mayakan Boko Haram a gabashin Arege da ke yankin Tafkin Chadi inda aka hallaka wasu daga cikinsu tare da lalata motocinsu da ke dauke da makamai.

Majalisa Za Ta Binciki Sayen Jiragen Yaki Da Aka Sayo Kan Milyan 462


Majalisar Dattawa za ta binciki ministocin kudi da harkokin tsaro da kuma Shugaban Babban Bankin Nijeriya kan yadda suka yi gaban kansu wajen cire dala milyan 462 wajen sayo jiragen yaki daga Amurka.

Kotu Za Ta Bayyana Ranar Da Za A Bayyana Kudaden Da Aka Kashe Wajen Jinyar Buhari


Wata kotun tarayya ta sanya ranar 5 ga watan Yuni a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan karar da kungiyar ASRADI ta shigar bayan da Shugaban Babban Bankin Nijeriya, Godwin Emefiele ya ki amincewa da bukatar kungiyar na bayyana mata adadin kudaden da aka salwantar wajen jinyar Shugaba Buhari a London.

'Yan Daba Sun Arce Da Sandan Iko Na Majalisar Dattawa


Wasu 'yan daba da suka yi ikirarin suna tare da dan majalisar Dattawan da aka dakatar, Sanata Ovie Omo-Agege sun kutsa kai zauren majalisar inda suka arce da sandan ikon majalisar.
Rahotanni sun nuna cewa 'yan dabar wanda sun kai su goma sun iso harabar majalisar ce Jin kadan bayan isowar dakataccen dan majalisar inda suka shaidawa masu gadin zauren majalisar cewa suna tare da Sanatan ne wanda suka kuma arce da sandan ikon majalisar.

Monday 2 April 2018

Sojoji Sun Kama 'Yan Ta'adda A Jihar Taraba

An kama su ne a yankin Mayo Ndaga dake jihar ta Taraba a jiya Asabar. Sannan kuma an gano makamai a wajensu.

Adam A. Zango Ya Kori Yaransa Baki Daya, Har Ma Da Wasu Abokansa


Rahotanni daga jihar Kaduna sun nuna cewa fitaccen jarumin finafinan Hausa Adam A. Zango ya kori yaransa baki daya, inda ya bayyana cewa daga yanzu ba shi ba su.

Rahotannin sun kara da cewa baya ga hadiman nasa da Adamu Usher ya sallama har da wasu daga cikin abokansa.

Majiyar ta kara da cewa daga cikin dalilan da ya sa Adam Zango yanke wannan hukuncin shine sau da yawa yaran nasa na ji kuma suna gani ana ci masa mutunci amma ba za su iya kare masa hakkin sa ba, inda a wasu lokutan ma da su ake haduwa a bata masa suna, duk da cewa yana biya musu bukatunsu daidai gwargwado.