Tuesday 12 June 2018

Shugabannin Yarbawa Na Ci gaba Da Jinjinawa Buhari Kan Baiwa Abiola Lambar GfCR

▪ Dole In Yiwa Buhari Yakin Neman Zabe A 2019 — Tinubu

▪ Buhari Ya Amince Da Baiwa Wasu 'Yan Siyasa Lambobin Yabo

Shugabannin Yarbawa na ci gaba jinjinawa Shugaba Muhammad Buhari bisa matakin da ya dauka na baiwa Marigayi M.K.O Abiola Babbar lambar girmamawa ta kasa wato, GFCR a yau a ranar 12 ga watan Yuni wadda rana ce da aka soke zaben Shugaban kasa da marigayin ya lashe a 1993.

Tuni dai, Tsohon Gwamnan Legas, Bola Tinubu ya tabbatar da cewa wannan mataki da Buhari ya dauka na girmama Abiola ya sa dole ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa Buhari yakin neman zabe a shekarar 2019 inda ya nuna yin haka girmamawa ce ga daukacin Yarbawa.

Shi kuwa dan fitaccen lauyan nan Marigayi Gani Fawehenme wanda shi ma ya samu lambar girmamawa duk da yake a lokacin yana raye ya ki karbar lambar, Mohammed Fawehenme ya nuna cewa babu wani Shugaba a tarihin Nijeriya da ya san abin da ya dace irin Shubaga Buhari.

Haka nan kuma Shugaba Buhari ya amince da baiwa wasu Fitattun 'yan siyasa da suka taka rawa a dimokradiyyar Nijeriya lambar girmamawa. Da yake tabbatar da haka Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustafa ya ce nan bada jimawa za a fitar da sunayen wadannan 'yan siyasar

Shugaba Buhari ya yabi matasan Najeriya a ganawar da yayi da firaiministan Morocco

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gana da firaministan kasar Morocco, Saadeddine Othmani, inda ya shaida mishi cewa mutanen Najeriya, wanda yawancin su matasa ne suna da kokarin aiki tukuru duk inda suka samu kansu a gida Najeriya ko a kasashen waje.

Shugaba Buhari ya kara da cewa shi yasa gwamnatin shi take kokarin ganin ta tallafawa matasan dan su bayar da gudummuwar data dace wajan ciyar da kasar gaba,

Ya kara da cewa Najeriya na kokarin ganin ta inganta harkokin Ilimi dana noma ta hanyar yin hadaka da kasashen Duniya wajan tabbatar da hakan.

Ya bayyana cewa an samu raguwar shigar da shinkafa kasar sosai, sannan kuma hadin gwiwar da Najeriya tayi da kasar Moroccon yasa kudin takin zamani ya ragu da kashi hamsin cikin dari.

Da yake jawabi a ganawar tasu, Firaiminista, Saadeddine ya bayyana cewa 'yan Morocco sun tabbatar da 'yan Najeriya nada hazaka dan sun gani a kasa, sannan kuma zasu cigaba da tabbatar da dangantaka me kyau da Najeriya.

Shugaba Buhari ya kuma gana da shugaban masu bayar da shawara akan harkar kasuwanci na kasar ta Morocco Ben Chemmas da kuma shugaban majalisar wakilai Habib El-Malki.

'Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum 8 a arangamar da 'yan baranda su kayi da 'yan banga a Sakkwato

Hukumar Yan sanda reshen Jihar Sakkwato ta tabbatar da rasuwar mutane takwas a wata rikici da ya barke tsakanin yan baranda da yan banga a jiya Litinin a karamar hukumar Isa da ke Jihar Sakkwato.

Jami'ar hulda da jama'a ta rundunar, Cordelia Nwawe ta shaidawa yan jaridar cewa ana kyautata zaton mutane takwas ne suka rasu ciki har da wani dattijo da yan barandan su kayi kokarin sacewa.

Mrs.Nwawe ta kara da cewa har yanzu ana cigaba da gudanar da bincike a kan lamarin, ta kuma ce ana kyautata zaton yan barandan sun zo ne daga kauyukan jihar Zamfara da ke makwabtaka da Sakkwato.

Ta kuma ce kwamishinan Yan sanda na jihar ya ziyarci kauyen da abin ya faru don yin jaje ga iyalen wadanda abin ya shafa tare da tabbatar musu cewa yan sanda za su binciko wadanda suka aikata wannan laifin.

Sai dai a wani rahoton, an ce mutane 13 ne suka rasu sakamakon yunkurin da yan barandan su kayi na sace wani dattijo ranar Asabar a kauyen Dan Tasango a Gundumar Gebe.

A cewar wani ganau, yan barandan sun harbe dattijon ne saboda ya ki yarda su tafi dashi, hakan ne yasa yan bangan garin suka hada kai don bin sahun yan barandan.

Majiyar ta cigaba da cewa 'yan barandan sunyi wa yan bangan kwantar bauna a hanyar Kamarawa-Barafawa inda akayi musayar wuta inda yan barandan suka kashe yan banga bakwai su kuma aka kashe musu mutane biyar.

Sai dai yan barandan sun kwace gawawwakin mutane biyar din da aka kashe musu kamar yadda suka saba saboda kar a gane kosu wanene.

Monday 11 June 2018

Matashi Ya Yi Wa Budurwarsa Yankan Rago A Jihar Yobe

Ana zargin wani matashi dan garin Potiskum dake jihar Yobe mai suna Muhammad Isa Adamu da yi wa budurwasa mai suna Hauwa yankan rago.

A bisa bayanan da iyayen Hauwa mazauna garin Damaturu suka yi, sun ce a ranar 29/05/2018 Hauwa ta fita da safe da niyyar sayo biredi a shago mafi kusa da su, sai dai tun daga fitar ta ba ta dawo ba har zuwa yammaci, wannan dalilin ya sa suka bazama nemanta, yayin da suka bada cigiyar ta a gidajen rediyo da ma wajen 'yan sanda.

Kwatsam sai suka ji an samu gawar wata budurwa a kan titin Gujba, inda ba su yi kasa a guiwa ba zuwa wurin inda suka tabbatar da 'yarsu ce.

A yayin da wannan matashi yake karin haske akan abun da ya faru, ya shaidawa manema labarai a garin Damaturu cewa, ya gayyaci Hauwa tsohuwar budurwarsa wadda ya fara nemanta tun 2014, soyayyarsu tayi nisa sosai, kuma bai taba sa ta wani abu ta ki yi ba, ya tabbatar da irin biyayya da Hauwa take masa, wannan dalilin yasa da ya gayyace ta kan hanyar Gujba, ba ta yi masa jayayya ba.

A cewar sa, bayan sun gama hirar su da Hauwa, sai ya umarce ta da ta rufe idonta, ba ta yi jayayya ba nan take ta rufe idon ta ba tare da ta san me yake shirin yi mata ba, sai ya ciro wuka ya soke ta a wuya, bada wani bata lokaci ba rai ya yi halinsa.

Da aka tambaye shi ko mai ya yi zafi har ya yanke wannan danyen hukunci ga wadda yake so?

Sai ya ce, ya yi iya kokarin sa don ganin mahaifansa su je Damaturu su nema masa auren Hauwa amma sun ki, kwatsam sai ya ga wani matashi ya fara zuwa wajen ta, wannan dalilin ya sa ya yanke hukuncin kashe ta kowa ma ya rasa.

A bisa bayanan da kwamishinan 'yan sanda na jihar Yobe ya yi wa manema labarai, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma yi alkawarin nan bada jimawa ba za su gurfanar da wannan matashi gaban kotu dan yanke masa hukunci.

Barazanar Tsige Buhari Ta Jefa Dogara Cikin Jangwan

Shugabanni jam'iyyar APC na mazabar Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara sun cimma matsaya na maye gurbinsa da wani sabon dan takarar mai suna Godfrey Mannaseh bisa abin da suka kira adawar da Dogara ke yi da Buhari da kuma Gwamnan Bauchi.

Shugabannin uku, Haruna Rikaya, Malam Zubairu da Wakili Amadi sun nuna cewa Shugaban majalisar wakilan da na hannu kan barazanar da 'yan majalisar suka yi kwanaki na tsige Shugaba Buhari inda suka jaddada cewa ba irin wakilcin da suka tura shi ya yi masu ba kenan.

Shugaba Buhari Da Sarkin Moroco Sun Kulla Alaka Kan Harkokin Man Fetur, Gas Da Sauransu

Shugabannin biyu sun tattauna da kuma cimma yarjejeniya na karfara tattalin arzikin kasashen biyu.

Wadanda suka rattaba hannu kan wannan yarjejeniya sune Manaja a kamfanin NNPC, Mr Farouq da kuma ministan man kasar Moroco, Misis Amina Benkhadra

Haka kuma shugaba Muhammadu Buhari da Sarki Muhammad VI sun shaida yarjejeniyar gina babban masana’antar hada sinadarin takin zamani wato Ammonia, wanda shugaban sanya hannun jarin Nijeriya, Mista Uche Orji da Mista Mostafa Terrab na Moroco suka rattaba hannu.

An Nemi Buhari Ya Binciki Yadda Obasonjo Ya Mikawa Kamaru Yankin Bakassi

An Nemi Buhari Ya Binciki Yadda Obasonjo Ya Mikawa Kamaru Yankin Bakassi

Tsohon Gwamnan Abia, Orji Uzor Kalu ya nemi Shugaba Muhammad Buhari kan ya binciki Cif Olusegun Obasonjo game da yadda ya mikawa Kasar Kamaru yankin nan mai arzikin man fetur na Bakassi .

Tsohon Gwamnan ya ce, akwai wata manufa ta biyan bukata kansa idan aka yi la'akari da yadda Obasonjo ya mika yankin cikin sauki ba tare da wata jayayya ba.

Wasu Inyamurai Guda Biyar Sun Musulunta


Ga abinda Malama Aishat Obi 'yar kabilar Ibo dake da'awar jawo 'yan uwanta Inyamurai cikin addinin musulunci ta rubuta a shafi ta na facebook:

"Allahu Akbar, Asalamu alaikum 'yan uwana musulmai maza da mata. Ku taya ni murnar shigowar wasu 'yan yankunan kudu maso kudu da kudu maso gabashin kasar nan cikin addinin musulunci a jiya a garin Fatakwal.

Sunayen su sune kamar haka:

(1) Believe Isaiah (Sehid Isaiah)  (daga jihar Rivers)

(2) Okechukwu Onwusaraka (Isan Onwusaraka) (daga jihar Imo)

(3) Chinonso Onyejiako (Hassan Onyejiako) (daga jihar Imo)

(4) Ngozi Uwa (Nafisa Hassan) (daga jihar Imo)

(5) Oluchi Eze (Khadija Eze) (daga jihar Imo)

Malama Aishat Obi ta kuma yi fatan Allah ya kare ta tare da ba ta nasara a da'awar da take yi don ganin ta jawo 'yan uwanta Inyamurai cikin addinin Musulunci.

Friday 8 June 2018

Zan Bada Kyauta Mai Tsoka Ga Duk Wanda Ya Nuna Mini Aikin Da Buhari Yayi Cikin Shekaru Uku—Tanko Yakasai

Zan Bada Kyauta Mai Tsoka Ga Duk Wanda Ya Nuna  Mini Aikin Da Buhari Yayi Cikin Shekaru Uku—Tanko Yakasai

Shugaban Majalisar Dattawan Arewa, Alhaji Tanko Yakasai ya kalubalanci kowane ne kan a nuna masa aiki guda da Shugaba Muhammad Buhari ya kammala a cikin shekaru uku da ya yi kan mulki.

Ya kara da cewa mutane nawa ne aka yankewa hukunci bisa tuhumar rashawa a shirin yaki da rashawa da Shugaban ya kaddamar inda ya nuna cewa har yanzu Buhari ya kasa hukunta tsohon Sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal wanda aka samu da laifin rashawa dumu-dumu.

Bincike : Matafiya da kafa da sauri,sun fi tsawon rai

Bincike : Matafiya da kafa da sauri,sun fi tsawon rai

Sakamakon wani sabon bincike da aka wallafa a makalar  "MotsaJiki"  ta kasar Ingila,ya nuna alakar da ke tsakanin tafiya da kafa da sauri-sauri da kuma tsawon rai.

Masana a kasashen Burtaniya da Ostireliya sun sanar da cewa, yawancin wadanda ke tafiya da kafa a gaggauce,basa kamuwa da ciwon zuciya.

Da wannan dabarar,hatsarin kamuwa da ciwon zuciya wanda a yawancin lokaci shi ne ummal-aba'isar mutuwar masu sama da shekaru 60,na raguwa da kaso 53 cikin dari.

Masu bincike sun gano cewa,tafiya da kafa da sauri tsawon awanni 5 zuwa 7 sun isa matuka gaya ga masu bukatar suyi rayuwa lami-lafiya.

Manufar wannan tafiyar ita ce,  bai wa zuciya damar bugawa da gaggawa,shi yasa kamata yayi a dinka takawa da sauri ta yadda za a yi kankanuwar zufa.

Masanan na Burtaniyar sun sanar da cewa, motsa jiki tsawon dakiku 30 a kowace rana da kuma cin lafiyayyen abinci, na tsawaita raywuwar mutum da shekaru 10.

Ya zama wajibi Allah ya jarrabci jihar Zamfara da masifu da bala'o'i daban daban

Ya zama wajibi Allah ya jarrabci jihar Zamfara da masifu da bala'o'i daban daban,

kamar kisan jama'a da garkuwa da mutane da suka zama ruwan dare yanzu a fadin jihar.

Magidanta na zina Matan aure na zina, samari na zina 'yan mata na zina, wasu mazan na luwadi wasu Mata na madigo, wasu na lalata da Mata mahaukata, wasu na bin dabbobi da lalata, ana satar jarirai ana yankawa, wasu na zuwa makarbarta suna tono gawawwaki ana cire wasu sassa na jikinsu domin tsafi, 'ya'ya na bijirewa iyayen su, da sauran manyan laifuka da ake aikatawa ba dare ba rana a Zamfara, wallahi dole Allah ya fitini jihar Zamfara, Allah mun tuba!!! ~ Inji Dakta Tukur Sani Jangebe a yayin karatun tafsirin kur'ani mai girma da yake gabatarwa a Massalachin GRA Gusau jihar Zamfara.

Tsaffin ‘yan sabuwar PDP zasu fice daga APC 23 ga watan Yuni

Wata majiya mai tushe ta shaidawa gidan jaridar DAILY TRUST cewar nan da ranar 23 ga watan Yuni tsaffin ‘yan sabuwar PDP da suka hada da SHugaban majalisar dattawa dBukola Saraki da kakakin majalisar wakilai na tarayya Yakubu Dogara zasu fice daga jam’iyyar APC zuwa wata jam’iyya.

Tsaffin ‘yan sabuwar PDP din sun zabi ranar 23 ga watan Yuni ne, domin ta zamo daidai da ranar da jam’iyyar APC zata yi babban taron ta na kasa inda zata zabi sabbin Shugabanni.

Majiyar ta shaidawajaridar cewar jiga jigan jam’iyyar sun gama tattara komatsansu domin ficewa daga jam’iyyar ta APC domin tsallakawa zuwa jam’iyyar adawa wanda suke karkashin jagorancin Alhaji Kawu Baraje.

Idan har ta tabbata tsaffin ‘yan sabuwar PDP zasu fice daga jam’iyyar APC a ranar babban taron jam’iyyar na kasa, to, tarihi zai maimaita kansa. Domin a shekarar 2013 ne tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya jagoranci wasu Gwamnoni da mukarraban PDP suka ficee daga jam’iyyar a lokacin da jam’iyyar ke yin babban taron ta na kasa.

Inda bayan ficewarsu daga jam’iyyar PDP suka hallara a Shehu YarAdua santa inda suka bayyana kansu a matsayin sabuwar PDP, karkashin jagorancin Alhaji Kawu Baraje wanda ya jagorance su a lokacin.

Ficewar da tsaffin ‘yan sabuwar PDP suka yi daga jam’iyyar tasu, na daga cikin dalilan da suka sabbabawa jam’iyyar ta PDP samun koma baya tare kuma da faduwa babban zaben shekarar 2015.

Thursday 7 June 2018

Uwar Nakasassu da Marasa Galihu na Jihar Kaduna , Hajiya Hadiza El-Rufai ta Sha Ruwa da Mata Nakasassu.

Uwar Gidan Maigirma Gwamnan Jihar Kaduna, Hajiya Hadiza El-Rufai wanda ake yi wa lakabi da “Uwar Nakassu da Marasa Galihu” yau Alhamis 7 ga watan Yuni, 2018 ta kira mata nakasassu da marasa galihu na Jihar Kaduna a nan Gidan Gwamnati na Sa Kashim Ibrahim da ke Kaduna don shan ruwa tare da su.

Hajiya Hadiza El-Rufai takan kira wadannan masu bukata ta musamman ne shan ruwa don nuna musu irin yadda Gwamnatin Jihar Kaduna ta damu da su. Wannan dalilin ya sa duk shekara ita uwar gidan gwamnan kan kira su Shan ruwa, sannan har ta ba su atamfofi don su je su dinka su sami kayan sallah.

A jawabin Kwamishinan Mata da walwalar Jama’a, Hajiya Hafsat Baba ta bayyana wa wadannan mata nakasassu, Gwamnatin Jihar Kaduna na nan tana gyarawa da gina sababbin cibiyoyi na koyar da nakasassu sana’o’i a mazabu uku da ke fadin jihar don su da ‘ya’yansu su zama masu dogaro da kai.

Sannan ta bayyana yadda Gwamnatin Jihar Kaduna ta dauki daya daga cikin wadannan mata nakasassu aka ba ta mukami na P.A a ofishinta duk dai don nuna wannan gwamnati ta damu da su.

Su ma a nasu bangaren, wasu daga cikin nakasassun sun bayyana irin jin dadinsu yadda wannan gwamnati ta damu da su, wanda ba a taba nuna musu irin wannan kaunar ba a gwamnatocin baya.

A Nuna Mani Aiki Guda Da Buhari Ya Kammala A Shekaru Uku—Tanko Yakasai


Shugaban Majalisar Dattawan Arewa, Alhaji Tanko Yakasai ya kalubalanci kowane ne kan a nuna masa aiki guda da Shugaba Muhammad Buhari ya kammala a cikin shekaru uku da ya yi kan mulki.

Ya kara da cewa mutane nawa ne aka yankewa hukunci bisa tuhumar rashawa a shirin yaki da rashawa da Shugaban ya kaddamar inda ya nuna cewa har yanzu Buhari ya kasa hukunta tsohon Sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal wanda aka samu da laifin rashawa dumu-dumu.

Wednesday 6 June 2018

Tsige Buhari za mu yi tunda dai shi ba Allah bane – Hon.Jagaba Adams

Rahotanni sun nuna cewa wani dan majalisar wakilai, Jagaba Adams Jagaba ya caccaki gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A cewar dan majalisar, babu wani abu da ake fuskanta a wannan mulkin baya ga bakar wahala da matsananciyar yunwa.

Jagaba ya kasance dan majalisa mai wakilatar Kachia da Kagarko na jihar Kaduna.

Furucin dan majalisar na zuwa ne bayan da majalisar dokokin kasar tayi barazanar tsige shugaba Buhari idan har bai aiwatar da kudurorin da suka zartar ba.

Mista Jagaba ya ce idan har Shugaba Buhari bai aiwatar da kudurorin da suka bukata ba to za su tsige shi a bisa tsarin kundin mulkin kasa.

Jagaba ya jadadda cewa basa dari-dari akan yiwuwar hakan saboda

"Buharin ba Allah ba ne kuma bai yi kama da Annabi ba, duk inda ya yi kuskure za mu take shi" .

Buhari Ma Ya Ci Kudin Makamai, Cewar Sule Lamido

...idan Buhari ya kama Jonathan sai sama ta fado, cewarsa

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Dakta Sule Lamido ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da cewa shi ma yaci kudin makamai.

Lamido ya bayyana haka ne a shafinsa na kafar sadarwar zamani, Facebook, inda yace tsohon mai baiwa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara kan harkokin tsaro, Kanau Sambo Dasuki ya baiwa Buhari motoci masu sulke guda biyu bayan da Boko Haram ta kai masa hari a Kaduna.

Haka kuma Sule Lamido ya kara da cewa me ya sa Buhari ya gagara kama Jonathan, bayan duk wadanda ake tuhuma suna na da nasaba da tsohon shugaban?

“Wai a ina Dasuki ya samu dala biliyan 2.5 da ya rarrabawa manyan mutane yayin da ake gab da zaben 2015, laifin da ya sa har yanzu yake daure a hannun hukumar DSS? A ina Nenadi ta samu makudan bilyoyi da ta rarrabawa jihohi wanda ya sa a yanzu haka take gaban Kotu?

“Ga amsa, dukkaninsu sun samu kudaden ne daga babban bankin Nijeriya dake karkashin shugaban bankin na yanzu, Godwin Emefeile, kuma tsohon shuhgaba Jonathan ne ya bada wannan umarni", cewar Lamido.

Daga karshe Sule Lamido wanda yake  takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP yace: “Don haka tunda Alkali Binta Nyako ta yanke hukucin cewar bai kamata a kama duk wanda aka basu umarnin yin laifi ba, Gwmanatin Buhari ba zata iya kama Jonathan bane, ta gwada mu gani, da sai sama ta fado".

Shekaru Hudu Masu Albarka Akan Karagar Masarautar Gombe

Daga Haji Shehu

Tun bayan dalewarsa kan karagar mulki. Mai martaba sarkin Gombe Dr. Abubakar Shehu Abubakar lll, yazamto zakaran gwajin dafin sarakuna a fagen tallafawa talakawan jaharsa ta fuskoki daban daban ba tare da gajiyawa ba Dare, Rana, Ruwa, da ma iska basu katsewa mai martaba cigaba da shimfida ayyukan alkairi ga talakawan jahar Gombe ba.

Halinsa na jinkan talakawa yasa mai martaba Abubakar Shehu Abubakar lll ya kirkiro wata gidauniya wacce zatake tallafawa mabukata musamman talakawa, marayu, marasa galihu da sauran su, gidauniyar mai suna SHEHU USMAN ABUBAKAR FOUNDATION wacce akayiwa lakabi da sunan marigayi sarkin Gombe Dr. Shehu Usman Abubakar Allah ya jikanshi, ta cigaba da daura ayyukan alkairi karkashin jagorancin mai martaba sarki.

Shehu Usman Abubakar Foundation wacce aka kirkito ta a watan Feburairu na alif 2015 ta cimma ayyuka daban daban don inganta rayuwar talakawa da marasa galihu. Sati biyu da kafa wannan gidauniya, gidauniyar ta rarraba manyan motocin abinci guda biyar ga talakawa da marayu don inganta walwalar su.

A watan Yuli na 2015, gidauniyar ta tallafawa fiye da matasa 200 shiga makarantar gaba da secondary ta hanyar biya musu kudin rijista.

A watan azumi, tawagar gidauniyar karkashin jagorancin shugabanta Mai Martaba sarkin Gombe Abubakar Shehu Abubakar lll sunkai ziyarar duba marasa lafiya a asibitin koyarwa na Gomnatin tarayya dake Gombe (FED. TEACHING HOSPITAL) da kuma asibitin kwararru mallakan jahar Gombe (SPECIALIST HOSPITAL), inda suka bawa kowane majinyaci Naira dubu 5000 don shan ruwa. Tawagar bata tsayaba saida ta fadada ziyarar zuwa masallatai tare da rarraba kayan abinci ga mabukata.

A watan Satumba 2015, Gidauniyar ta duba kiraye kirayen al'umma na neman a samar musu da ruwan sha, nan take gidauniyar tayi azama ta bada kwangilar tonon famfunan burtsatsai guda 21 a unguwanni da kuma sansanonin yan gudun hijira don samun saukin wahalhalun ruwan sha.

A watan October/November 2015, gidauniyar tayi bikin da ya sosawa dubun dubatan jama'a rai, domin kuwa gidauniyar ta karrama yara marayu da marasa galihu tayi ta hanyar daukan nauyin karatun yara fiye da 1500 daga firamare harzuwa jami'a.

Gidauniyar bata tsaya nan ba domin a watan November 2015 ta leka zuwa gidan yarin dake jahar Gombe, namma ta yanta fursunoni guda 61 sannan ta koyar musu sana'a don kaucewa sake afkuwar abunda yafaru da su abaya.

A watan December ta 2015, gidauniyar ta samo kwararrun likitotin ido don yiwa majinyata 21 aikin ido kyauta

Gidauniyar ta tallafa da kashi 30% na kudin abincin mai gina jiki da ake ciyarda yara kankana masu duke da ciwon HIV, a wajen wani biki da hukumar dake yaki da yaduwar cutar HIV na jahar Gombe mai suna GOMSACA ta shirya.

Gidauniyar tare da hadin guiwar kamfanin Media trust LTD sun rarraba kayakin abinci da na aikace aikacen gida na zunzurutun kudi har naira miliyon 5000000 ga yan gudun hijira a jahar Gombe.

Gidauniyar bata tsaya nan ba saida ta tallafawa almajirai kimanin dubu 26000 daga makarantu 333 da buhu hunan abinci taburmai da kuma littatafa na karatu.

Ruwan Sama Da Iska Mai Karfin Gaske Ya Jawo Asarar Dukiyoyi A Jihar Kebbi


Barnar ruwan sama da iska mai karfi sun yi barna a kauyen Kambaza na karamar hukumar Mulkin Gwandu, inda aka yi asarar dukiya mai dibin yawa da kuma rushewar gidaje, kuma jama'a da dama sun samu raunuka. Sai dai babu asarar rayuwa, sannan mutane da dama sun rasa matsugunnansu.

Daga Zaidu Bala Kofa Sabuwa, Birnin Kebbi

Tuesday 5 June 2018

Tsuguno bata karewa Dino Malaye ba za'a cigaba da gurfanar dashi gaban Kotu


Tunda Dino Melaye ya samu lafiya, a cigaba da gurfanarsa – AGF Malami ya bukaci kotu

Naijdotcom ta ruwaito Ministan Shari’a kuma babban lauyan tarayya, Abubakar Malami, ya bukaci babban kotun birnin tarayya Abuja, da ta cigaba da gurfanar da Sanata Dino Melaye, bayan dakatad da sanadiyar jinya da yake yi.

Jaridar Punch ta bada rahoto a jiya Litinin cewa ta samu wasikan da aka turawa kotu tana sanar da ita cewa Dino Melaye ya samu lafiya har ya koma bakin aiki a majalisar dattawa ranan30 ga watan Mayu.

Ofishin babban lauyan kasa tana tuhumar Dino Melaye da karya ga hukumar yan sanda domin yiwa na kusa da gwamnan jihar Kogi, Edward Onoja David, sharri cewa ya tura wasu kashe shi.

A ranan 17 ga watan Mayu 2018, Justice Olasunbo Goodluck, ya dakatad da karar Melaye ne zuwa lokacin da za’a sallameshi daga babban asibitin tarayya da ke Abuja inda yake kwance.

A wasikar, lauyan gwamnati, Mr Shuaibu Labara, ya laburtawa kotu cewa an salami Melaye kuma ya koma bakin aiki rike da sanda da abu a wuya.

Tunda ya koma kuma, an ganshi yana magana a majalisa saboda haka, kotu ta bada sabon ranan domin cigaba da gurfanarsa.

Gwamnatin Jonathan ba ta yi kama karya irin ta wannan Gwamnain ba – inji Dakta Gumi

Daga DailyNigerian Hausa

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan,Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya caccaki rundunar ‘yan sanda ta kasa kan yadda suka ci zarafin Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki. A cewarsa cin fuska ne ‘yan sanda su gayyace shi maimakon su je su same shi.

Mutum na uku a kasar nan yana da matukar muhimmanci kwarai da gaske, bai kamata ba kuma a wulakanta shi ba, irin yadda ‘yan sanda suke yi masa yanzu haka. Idan Shugaban kasa ya bari aka wulakanta shi, to ya sani kansa ya wulakanta”

“Idan aka dore a haka, to, shima Shugaban kasa duk ranar da ya sauka haka zai kare ba shi da kima, ana iya sanya ‘yan sanda su kama shi ko su wulakanta shi babu kuma abinda zai faru”

“Me yasa ake tsare da Sambo Dasuki, ku gaya mana a lokacin Gwamnatin Jonathan da ta gabata an yihaka ne? Amma me yasa yanzu ake yiwa mutane bitada da kulli bayan a zamanin gwamnatin Jonathan sam bamu shaidi hakan ba”

Anci zarafin addinin Musulunci a wakar Shaku Shaku – MURIC


Daga DailyNigerian Hausa

*Wakar fitsarar da aka ci zarafin addinin Musulunci*

Wani mawaki da ake kira da sunan Folarin Falana ko inkiya (Falz the Bahd Guy) ya fitar da wata sabuwar waka mai suna Shaku Shaku da yaci zarafin Fulani da kuma addinin Musulunci a cikinta.

A cikin faifan bidiyon wakar an nuna wani Bafulatani yana sare kan mutane babu gaira babu dalili, abinda yake nuna cin zarafi ga kabilar Fulani a Najeriya. haka kuma a cikin akar an ci zarafin addinin Musulunci, inda aka nuna wata mata sanye da Hijabi tana rawar ‘yan kwaya.

Wakar dai an sanya mata sunan “This is Nigeria” ma’ana “Wannan ita ce Najeriya” inda a cikin wakar aka dinga wata rawa ta rashin mutunci da aka sanya sunan shaku shaku.

A sabpda haka ne itacciyar kungiyar kare ‘yancin Musulmi ta MURIC ta yi Allawadai da wannan sabon faifan bidiyo da ya ci zarafin Musulmi, ta nemi kuma a gaggauta janye wakar daga kasuwa matukar ana son zaman lafiya.

Ta Ya Za A Magance Karuwar Zubar Da Ciki Ba Bisa Ka’ida Ba?

Tsoro da abin kunya da buna kyama ya sanya miliyon mata tsunda zubar da juna biyu harda yin hakan ba’ a bisa ka’ida ba, inda suke zuwa harmatattun asibiti don su zubar da juna biyun da suka dauka  kuma hakan yana jefa rayuwar su da lafiyar su a cikin hadari.

A wannan rahoton da SADE OGUNTOLA ta rubuta kuma ABUBAKAR ABBA ya fassara, kwararru akan harkar kiwon lafiya sun bayyana cewar, kaucewa mutuwar masu zubar da ciki ba’a bisa ka’ida ba, za’a iya samun nasara hakan ne idan irin wadannan matan sun kula da ‘yancin su yin jima’i da kuma kula da kiwon lafiyar  su.

Lokacin da ‘yan fashi da makami suka yiwa wata Mildred Haruna (wanda wannan ba shine sunanta na ainahi ba) fyade, a anguwar su dake cikin jihar Legas a shekarar 2005, ba ta taba tsammanin fyaden da aka yi mata da daren ranar ba zaici gaba da rikitar mata da rayuwar ta ba.


Bayan dimautar data tsinci kanta bayan yi mata fyaden, Mildred ta gano cewar, ta samu juna biyu kuma dimautar tata, taci gaba da karuwa saboda, duk da shawarar data yanke na ta bar juna biyun, sai dai dan albashin da take karba ba zai iya ba ta sukunin daukar dawainiyar abinda zata haifa ba.

Sannan kuma mutane za su dinga kallon abinda zata haifa a matsayin shege tunda baida uba. Sai dai, taga abinda yafi mata mafita shine ta zubar da cikin amma sai dai ba abu ne mai sauki a gare ta ba domin kuwa, maganar zubar da ciki abu ne da ya kamata ayi shi a asirce. Ta yanke shawarar zuwa asibiti don ta yiwa likita korafin ba ta da lafiya yadda zata ja hankalin likitan.

Amma ba za ta yi korafin jin tabin hankali ba ko nuna akawai damuwa tare da ita ba saboda jaririn dake cikinta yana ci gaba da kara girma, inda a karshe dai ta haifi abinda ke cikinta. A wata sabuwa kuma, wata ‘yar shekara ashirin da biyu mai suna Comfort, wadda dalibace a jami’a, itama an dirka mata ciki.

Sakamakon cikin, ta shiga cikin rudani da jin tsoro akan abinda zaije yazo, inda daga baya ta yanke shawar zubar da cikin ta hanyar zuwa gun likitan bogi. Sai dai, ta samu nasarar zubarda cikin, amma daga bisani ta fara jin zafi wanda ya janyo mata ta fara kwarar da jini an kuma yi gaggawar kaita Asibiti daga bisani da ta mutu.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewar an samu kimanin miliyan ashirin da biyar na zubar da ciki ba bisa ka’ida ba da aka kiyasta ya faru a fadin duniya dukkan shekara, musamman a kasashen masu tasowa. Daga cikin wannan adadin, miliyan takwas na zubar da cikin, anyi su ne ba bisa ka’ida ba ko kuma a cikin wasu yanayi masu hadarin gaske. Bugu da kari, yawan  zubar da cikin da aka yi ba a bisa ka’ida ba, ya faru ne a nahiyar Asia kuma uku daga cikin hudu na zubar da cikin, ya auku ne a nahiyar Afirika da Latin Amurka.

Zubar da cikin da aka yi ba’a bisa ka’ida wanda har ya janyo mutuwa, yafi yawa a Afirika. Ganin irin tunanin mafi yawancin ‘yan mata da kuma mata da suka dauki cikin da basu shirya ba, kwararru akan kiwon lafiya sunyi imanin cewar, zubar da ciki ba a bisa ka’ida ba yana kara zama babbar matsala akan harkar kiwon lafiya, musamman a kasashen da masu  karamin karfin tattalin arziki, harda Najeriya. Maganar gaskiya, jin tsoro da fadawa a cikin abin kunya da nuna kyama sune ke jefa miliyoyin mata zuwa Asibitocin boji don a zubar masu da cikin ba’a bisa ka’iba, inda hakan ke shafar lafiyar su da kuma rayuwar su kuma matan sune suke jin jiki in hakan ta faru gare su a kowanne lokaci.

Ana samun zubar da ciki ba ‘a bisa ka’ida ba idan wanda zaiyi aikin zubar da cikin  baida wata kwarewa ko kuma a Asibitin da bai cika sharuddan zama Asibiti ba ko kuma dukkan biyun. Abin takaici, nuna kyama ga matan da suka samu ciki ba tare da yin aure ba ko kuma a tsakanin ‘yan mata, ya kan sanya su fada a hannun likitocin bogi, inda hakan yake janyo masu ziyartar kabari ba tare da sun shirya ba. Ba kowa wacce mace data sanu ciki ba tare da aure ba, takan kasance abin nunawa a gari.

A cewar wata Darakata ta Ipas Hauwa Shekarau tace,”sai dai mutane baza su samu cikakken labarin ba.” Ipas kungiya ce mai zaman kanta da take gudanar da ayyukan kiwon lafiya a fadin duniya da kuma tabbatar da mata suna zubar da ciki a bisa ka’ida da samar da magunguna. Shekarau ta bayyana hakan ne a wani taron bita na kwana uku da tsare-tsare data shiryawa ‘yan jarida.

A cewar ta,“za su sanar da masalaha ga abokin wanda zai samar masu da hanya mafita, amma wadanda za su jagorance su zuwa ga zubar da ciki ba a bisa ka’ida.”

Shekarau taci gaba da cewa, sai dai abin takaici, damuwa ta zubar da ciki tanada yawa dake hana mutane akan daukar matakan da ya dace.” A cewar ta,“tunda basu san komai ba a zahiri, suna kawai dauka maganar kamar ba wata illa bace.” Ta yi nuni da cewa “wannan shine yake haifar da fadawa ga hannun likitocin bogi  da rashin samun kulawa na kiwon lafiya da ya dace.” Tace, illolin zubar da ciki ta hada da, zai iya janyo cutar cancer ta nono kuma matar data zubar da ciki ya kai har sau hudu, zatafi saurin mutuwa haka yin amfani da magunguna don a zubar da ciki zai iya janyo cutar (menopause). Bugu da kari, hana samun damar zubar da ciki, itace hanyar da tafi dacewa wajen rage zubar da ciki kuma idan mace tana zubar da ciki zai hana mata haihuwa saboda wasu sassan dake cikin jikinta za su lalace.

Ta bayyana cewar “kuma wani abin takaici, kin bin ka’ida wajen zubar da ciki ba wai kawai yana shafar yawan zubar da ciki bane, yana kuma hana cimma burin da ake bukata.“

Ta yi nuni da cewa, mafi yawancin kama  masu zubawarwa da mata ciki da aka yi  suna karewa ne a kotu kuma ba’a yanke masu hukunci, sai dai idan wadda aka zubarwa da cikin ta mutu ko kuma wata illa ta same ta.” A cewar ta, miliyan 1.25 na zubar da ciki da akeyi a duk shekara, ya faru ne a Najeriya a shekarar 2012 a bisa binciken da ciniyar Guttmacher ta gudanar. Wannan adadin, kamar a tsoma Allura ce a cikin ruwa sakamakon wani bincike da wani Asibiti ya gudanar a cikin jihohi sha takwas a Najeriya.” Yawan karuwar zubar da ciki ba ‘a bisa ka’ida yana da yawan gaske.

Sai dai, ta koka da akan tsar-tsaurar dokar da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauka a fadin duniya, inda tace, hakan zai kara nuna kyama akan zubar da ciki domin hakan zai kara sanya illa akan binciken da kungiyoyi suke yi akan shirin lafiyar mata a nahiyoyin. Tsarin garin Medico da aka sani na doka ya rufewa kasar Amurka bayar da kudi ga kungiyoyi masu zaman kansu wanda suke gudanar da aikin da ya shafi zubar da ciki ko bayar da shawarwari ko kuma kare ‘yancin mata na daukar juna biyu.

A cewar Shugaban kungiyar gangamin kayyade iyali Dakta Ejike Orji, zubar da ciki ba ‘a bisa ka’ida ba yana faruwa ne sakamakon nauyin tattalin arzikin kasa. Orji ya zayyana illolin dake tattare da zubar da ciki ba’a bisa ka’ida wadanda kuma ya ce sune suka janyo hana daukar ciki a Najeriya. Ya ce, “akwai rashin jin dadi ga magidantan da basu iya daukar ciki, ya kara da cewa, a maganar gaskiya, mace musamman wadda ba ta iya daukar ciki ‘yan uwan nijinta sukan jefata a cikin damuwa.

” Dakta Orji ya ce koda yake, a kalla ga dukkan mata biyar da suke zubar da ciki ba’ bisa ka’ida ba, daya na iya mutuwa, kuma akwai wasu illolin dake biyo baya in sunyi hakan kuma akwai tsada sosai sakamakon kamuwar da matan suka yi da illolin zubar da cikin a yayin yi masu magani. Babban abinda yafi yi janyo barazana wajen zubar da ciki a bisa ka’ida, yana haifar kwararar jini da kamuwa da kwayoyin cuta da jin rauni a cikin sassan dake jikin matan.

A cewar sa, tsadar kudin da ake kashewa wajen samar da lafiya sakamakon matsalolin da suka auku a yayain zubar da ciki ba’a bisa ka’ida ba, yana zama nauyi ga harkar kiwon kafiya a tsakanin kasashe masu tasowa. Ya yi nuni da cewar “amma za’a iya magance wannan tsadar ta zubar da cikin idan an rugumi hanyar kayyade iyali data kamata.” Ya bayyana cewa, zubar da ciki wani abu ne mai wahalar gaske kuma abin tausayi da mutane suke ganin wani abu ne na rashin ‘yanci. Shi kuwa Mista  Edoza Obiawe wanda shima yake aiki a IPAS, “ya ce, samun ‘yancin daukar ciki wani abu ne na ‘yancin dan adam. Samun wadatacciyar tarawa da ingantaciyyar kiwon lafiya sun hada da; samar da magunguna na zamani da kula da zubar da ciki ko kuma karewa kamuwa da kwayar cutar kanjamau, wasu abu ne da za su taimaka wajen cimma burin ci gaba.

” Ya yi nuni da cewa, hanawa mata sararin zubar da ciki musamman idan akwai barazana ga rayuwar mata da suka dauki ciki, ko kiwon lafiyar su ko kuma idan cikin an same shine sakamakon fyade zubar sa cikin  ya sabawa ‘yancin dan adam. A karshe ya ce,” idan ‘yan mata suna da koshin lafiya suna kuma da ‘yancin su, za su kuma  iya zuwa makaranta don su koyo wasu dabaru don kula da lafiyar su yadda za su zama manya da aka tallafawa.”

Daga Leadship Hausa

Sanatoci da yan majalisar dokoki sun yanke shawarar tsige Buhari muddin bai cika sharudda 10 ba

DA DUMI DUMI: Sanatoci da yan majalisar dokoki sun yanke shawarar tsige Buhari muddin bai cika sharudda 10 ba

Naij.com ta ruwaito Yan majalisan wakilai da dattawa sun lashi takobin tsige shugaba Muhamadu Buhari face ya cika wasu sharruda goma da suka kindaya masa.

Bayan ganawar da yan majalisan sukayi a yau wanda ya kwashe akalla sa’o’I 4, yan majalisan sun yanke shawaran cewa za su tsige shugaban da karfinsu idan har bai cika wadannan sharruda 10 ba.

Sharrudan sune,:

1. A baiwa hukumomin tsaro umurnin kawo karshen kashe-kashen da ke faruwa a fadin kasa.

2. Cin mutuncin yan adawan da fadar shugaban kasa keyi ya isa hakan kuma kada ya sake faruwa

3. Wajibi ne bangaren zantarwa su bi doka

4. Za’a daurawa shugaban kawa alhakin dukkan abinda wadanda ya nada suka yi

5. Gwamnatin tarayya ta nuna gaskiya wajen yaki da rashawan da takeyi

6. Wajibi ne a karewa majalisar dokoki hakkinsu kuma ayi binciken wadanda suka sace sandar majalisa

7. Majalisar dokoki za ta hada kai da majalisar ECOWAS, EU,UN da yan kungiyoyin fafutuka wajen kare demokradiyyan Najeriya

8. Wajibi ne a kawo karshen rashin aikin yi a Najeriya

9. Wajibi ne a ja kunne kuma a caccaki sifeto janar na hukumar yan sanda

10. Wajibi ne a jinjinawa shugaban majalisan dattawa, Bukola Saraki da kuma kakakin wakilai, Yakubu Dogara.

Yan majalisan sunce face an cika wadannan sharruda, ba zasu dagawa bangaren shugaban kasa kafa ba.

Sunday 3 June 2018

Cigaba Da Tsare Zakzaky Tsagwaron Rashin Adalci Ne ~ Inji Buba Galadima

Tsohon babban na hannun daman shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari kuma fitaccen dan adawar cikin gida Injiniya Buba Galadima ya bayyana cewa
cigaba da tsare jagoran 'yan shi'a a Najeriya Ibrahim Zakzaky da gwamnatin tarayya ke cigaba dayi a matsayin rashin adalci tsagwaron sa.

Injiniya Buba Galadima ya bayyana hakan ne a yayin da ake tattaunawa da shi a gidan talabijin din nan mai zaman kan sa na AIT a wani shiri da ake cewa "Focus Nigeria: Matters Arising"
A lokacin da aka tambaye shi ra'ayin sa game da cigaba da tsare shi.

Wata ma'aikaciyar gwamnati ta rasa aikinta bayan sukar Osinbajo da Aisha Buhari

Wata mace 'yar Najeriya, Bolouere Opukiri ta rasa aikin ta mako daya bayan ta yi suka a kan mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha a dandalin sada zumunta na Twitter.

A ranar 5 ga watan Yulin shekarar 2017, Opukiri ta ayyana cewa Osinbajo 'Dan koyo' ne saboda a kwanakin baya ya yi tafiya zuwa kasar waje a yayinda shugaba Buhari ke birnin Landan duk da cewa ana samun rashin jituwa tsakanin fadar shugaban kasa da majalisa a wannan lokacin.

Wasu Sanatocin Najeriya sunyi suka a kan tafiyar ta Osinbajo kwana daya kafin matar tayi nata sukar, Sanata Enyinnaya Abaribe na jihar Abia ya ce tafiyar ta Osinbajo ta bar wani 'gibi' da ya dace shugaban majalisa Bukola Saraki ya cike ta.

Kazalika, ta kuma sake yin wani rubutu a Twitter kwanaki biyar bayan na farkon inda ta soki Aisha Buhari da cewa ta fiye kwakwazo a kan wasu daga cikin 'kuraye' da 'dila' da kusanci da mijinta inda ta ke kokarin nuna cewa Aisha Buhari ba ta da wayewa irin ta tsohuwar matar shugaba Jonathan wato Patience.

Wasu 'yan Najeriya masu kishin gwamnatin Buhari sun tattara wannan rubuce-rubuce guda biyu da ma wasu da suka biyo baya kuma suka aike da shi zuwa ga ofishin yada labarai na shirin yin afuwa ga masu tada kayan bayan Neja Delta inda Opukiri ke aiki don daukan mataki.

Ofishin ya yi nazari a kan rubuce-rubucen tare da yin wasu bincike kuma daga baya ya yanke shawarar korar Ms Opukiri inda suka ce abinda ta yi ya sabawa dokokin aikin gwamnati kuma barazana ce ga tsaron kasa.

Ms Opukiri ta shaida wa Premium Times cewa korar da akayi mata ba bisa ka'ida bace kuma an tauye mata hakkin bayyana ra'ayinta inda ta ce tabbas za ta garzaya kotu don a bi mata hakkin ta.

Saturday 2 June 2018

Iya Tsawon Rayuwa Ta Ba Zan Samu Amini Kamar Kwankwaso Ba - Ganduje

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyanawa manema labarai cewa, Ba shi da kamar Kwankwaso, kamar yadda Kwankwaso ba shi da wanda ya fi Ganduje

“Zan bayar da duk lokacina domin yin sulhu da shi domin ba zan taba samun aboki kamar Kwankwaso ba iya tsawon rayuwa ta. Kuma shima ba shi da amini kamar Ganduje iya tsawon rayuwar sa".

Wannan a 2017 kenan

Tuni yan kudu sun dawo daga rakiyar Buhari, sai dakikai daga Arewa- inji Sheikh Gumi


...yace idan gaskiya ne a dora Buhari da Shagari akan mizani aga waye mai gaskiya a cikinsu

DailyNigerian ta ruwaito fitaccen Malamin Addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Gumi ya soki lamirin Gwamnatin Buhari kan batun yaki da cin hanci da rashawa. Shehun Malamin yayi wannan bayani ne a wajen Tafsirin Al-Kurani da yake gabatarwa a masallacin Sultan Bello.

Ya soki lamirin hukumar yaki da cin hanci da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, musamman abinda suka yiwa tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Alhaji Mukhtar Ramalan Yero,inda aka makala masa wani allo dauke da sunan cewar shi mai laifi ne.

Sheikh Gumi yace, “Ina kan hanya zan taho wajen Tafseer din nan ne, aka tura min wani hoto dauke da tsohon Gwamnan Kaduna Ramalan Yero yana rike da wani allo da ya nuna cewar shi mai laifi ne”

“Wannan ba daidai bane, abinda suka yi masa kuskure ne, dole ne a garemu mu gaya musu gaskiya”

“Da ya kamata Ramalan Yero ya jefar da allon yaki yadda ya daga, ba abinda zai faru in yayi haka, domin kotu ce kadai ke da ikon kama mutum da laifi”

“Batun Demokaradiyyar da ake magana, karya ake yi, domin ana take hakkin mutane”

“Idan ba dan an yafewa Shugaba Buhari laifukansa ba, da ba zai sake zama Shugaban Najeriya ba”

“Idan gaskiya ne a dora Buhari da Shagari akan mizani aga waye mai gaskiya a cikinsu”

AL'AJABI: An Haifi Yaro Dauke Da Kur'ani Da Carbi A Jihar Bauchi


...wannan raddi ne ga masu inkari da Annabi (S.A.W), cewar Sheik Dahiru Bauchi

Daga Maiwada B. Atake

Wata mata a garin Burga dake jihar Bauchi ta haifi yaro da Kur'ani da kuma carbi a hanunsa.

A yayin da matar ta zo da labarin al'ajabin zuwa gidan Shehin Malamin nan, wato Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ta shaida cewa, wannan yaro wanda aka rada masa suna Muhammad Auwal, haka ta haife shi. Ta kuma rantse da Allah cewa wannan lamari gaskiya ne babu kokonto.

A yayain hadubar Juma'ar da ta gabata da Sheik Dahiru Bauchi ya yi, ya ce "wannan ba komai bane a wurin Ubangiji illah raddi ga kafurai masu inkari da Annabi (SAW), don kara nuna musu cewa Manzon Allah gaskiya ne.

"Sannan ya kara nuna wa duniya irin mu'ujizar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam. Shine ya sa aka haifo wannan yaro da Kur'ani da kuma carbi".

Shehin Malamin ya kara da cewa "wannan carbi kuma ba komai bane face raddi ne ga masu inkarin Shehu Tijjani da darikarsa ta Tijjaniyya, don Allah ya kara nuna wa duniya cewa Dariku gaskiya ne.

Shehin ya kara da cewa duk ga alamomin Tijjaniyya a jikin wannan carbin. Wannan karamar Shehu Tijjani ne ta kara bayyana ga masu inkarin me Darikar ta Tijjaniyya.

A karshe Shehin ya yi addu'ar Allah ya kare Musulunci Da Musulmai, ya kuma zaunar da Nijeriya lafiya tare da kare ta daga dukkan bala'o'i.