Wednesday, 24 February 2016

Dangin Mijina Episode 5

If its your first time read the pevious HERE


Inna da baba sunyi murna matuka da dawowa na.sunga yadda nakara girma.kyau da haske.inna tace ana ramewa a boadn kekam kyau kikeyi .
A wani dare ne. Inna tace yan nan. Wannan malaminkun yaxo kwanaki yayi tambaya. Da bamuso mubasu amsaba. Anma mahaifinki yaga yadda yake lura dake a makaranta ya tabbata cewa shi mai taimakonki ne .hakan yasa ya amince.dafatan zabin yamiki?! Nace ae inna badamuwa. Ahaka muka kare hutunmu. Muka koma hutu.a lokacin aka raba prefectship abin mamaki waini aka bawa headgal.zafyra labour Furyad kitchen.mukam mune da makarantan. Tunda duk muhimman post a hannunmu suke. Muka bi da yara yanda sukeso. Kowa ka laluma yanason mu.shi kanshi principal yaji dadin kasancewarmu. Prefect.a lokacim su aisha alka suka zana jarabawa suka fita. Ran fitansu takirani taban leta. Nakarba naje na nutsu ina karantawa
Zuwa gareki

Ina mai tabbatar miki dacewa kuma baki shawara ki guji shigowa gidanmu don bagurin zamanki bane. Ahmed nawane har abada. Idan kikayi garajen aurensa zakiyi dana sani a rayiwanki.
Na tsaya na tsurawa letan ido. Yagawa nayi atake batare danasa komai arainaba. Aganina razanana takesonyi ahaka muka kammala secondary school, ranan fita munyi kuka da juna, da masoya. Ahmed shima a ranan yayi resign basuyi mamakiba, dama principal din yasan don nine. Ahmed ne yadawo damu saidaya sauke zafyra a igbo quarters.sannan muka sauke furyad a federal low cost.don duk naga gidansu. Mukayi alkawarin sada zumunci wa juna.
 Sannan yadawo dani gida, Nashiga natarar gidan a cike makil abun yaban mamaki. Ko ina na gifta ga amaryan tazo! haka inna takaini gunsu gwaggonanina. Akafaramin gyaran jiki. Anan inna take gayamin tun wancan jummaan aka daura aurena da ahmed G, nayi mamaki kwarai dagaske to meyasa bai gayaminba..? bangama mamaki ba saidayyama danaga zafyra dasu furyad dakuka wasu yan ajinmu da ashogbensu kowa takure adaka. Anan suke gayamin ahmed G ne yadauki nauyin komai.kuma yasanar dasu yace karsu gayamin.yanzu ma shiyabada motoci akawosu mukayi walima.
  Sannan dare dare ahmed G.da abokansa suka shirya dinner .munje mundawo lafiya washegari inna takiranit tarinkamin waazi, hakama baba. Dare dare aka kaini dakina. Dake GRA.
Katon gidan da aka shiga dani shiya matukar bani tsoro. haka muka shiga. Da misalin karfe sha daya bayan kowa ya watse. Angona yashigo .
Washegari da asuba bayan munyi sallah sai namike da zummar nemana abunci .yace inazaki ? Nace abinci zan daura mana. Yace dawo kizauna nadawo. Haka yasa muka koma bacci.da misalin karfe 8 nafarka nayo wanka na tsara kwalliyata. Nadaurawa maigidan nawa. Bayan mun kammala. Ne aka kawomana abinci daga gidansu ahmed G.muka karya. Sannan na nufi palour nazauna ina kallo. Yace bari yaje gun hajiyansa su gaysa zai dawo. Anan namike nazaga gidan. Nayi mamaki kwarai dagaske. Dama ahmed G. nada wannan arzikin? don ko yar minista albarka. Nasanshi yamin wannan kayan gidanmu bamuda arzikin dazaamin kayan dakin danaci karo dasu don har gun swimming da gym nagani . Bayan nazaga. Ina dawowa naji anbuga kofa azatona maigidan nawane saidana bude nasha mamaki. Bakowa bane illa aisha alka dakuma wata wacce suke kama daga gani yaruwarta ce. Sannan tayi murmushi. Ta rungumoni. Yauwa yar albarka amarya ta ango. Yakike? nayi mamaki matuka anma sai na hadiya nakirkiro murmushi.muka shiga tarinka zolayana. Ina bros din yake? nace yaje gayda hajiya. Tayi murmushi sannan tace toh Allah dawo dashi lafiya .kekuma 'you are welcome to the family' nayi murmushi sannan nace thanks . Mukadanyi tadi kafin nan ahmed yadawo. Ganinmu muna tare yasa yayi murmushi little sis? tace naam big bros. Yakike? Lafiya lau nazo ganin amarya ne. Aiho
Nan mukayita dadi harsuka tafi.
Cikin sati uku kullum sai aisha alka tazo tun ina dar dar da ita har nasake raina. Komai tare muke. Zaka zata mu kishiyoyine. Matsalaj tafara tun watana daya da rabi a gudan ahmed G.
Ina zaune ina karanta jarida saigata tashigo. Sis ya akayine? Nace sis wallahi inaduba wannan newspapern ne. Ohk tom. Mukadanyi tadi.sannan nace bara naje nayi sallah. Nafice nabarta agun. Fitowana naga bata falon.kasancewar gidan babba sai nayi zargin kotana wani gunne.donhaka sai nazauna. Can saiga ahmed G. Yadawo .narungumeshi tare damishi sannu da dawowa.nadauko riwan wankanshi da zummar nakaimishi bandaki. Baki a bude.ruwan zafin nasake agun. Ahmed nagani rungume da aisha alka. Wani irin kara nasaka ayayinda nasake butan. A razane yajuyo.idonsa tayi jajur.nikuma ashe ruwan yadan zubemin tagefen kafana.fadi nayi agun.
Bayan gwaje gwaje likita yayi wa ahmed kashedi akan akiyaye sannan aka yi drippn gun ciwon. Kallonsa nayi idona na zubar da hawaye. Ya kalleni cikin sanyin jiki. Mayah!! Meyasa kike da saurin fushi? Mekika gani dazaki tsorata har ki zuba ruwan zafi ajikinki.?! Wani irin kololon bakin ciki naji.wannan wacce irin musiba da rainin hankali ne? Nagansu sannan yamayar dani shasha.juyar dakai nayi.ahaka mutane sukayita zuwa suna gaysheni hardasu furyad da zafyra.da inna.dakuma kannena su aliyu.su hajiya dasauransu.uwar jinyan kuwa aisha alka ne duk tarude.wani irin tsananta naji. Ana gobe zaa sallameni. Tace majidadi nasan zakimin kallon maci amana.anma ba abunda kike tunani bane. Nadaga mata hannu.alamun tayi shiru a sanyaye tamike tabarni agun. Bayan ansallamoni su zafyra suka xo gaysheni.anan muke tattaunawa da kawayen nawa. To ke majidadi.wani irin yarinta ke damunki? matarda kinfimu sanin makiyarki ce sannan kisake mata?! Nace bahaka bane. Tazomin da fuskan lumana shiyasa gaba daya nasare da ita.furyad kuwa taja tsaki.ke sai uban zuciya anma da saurin amincewa da mutum. Tanaso tacuceki ai dole ta lallameki.kai furyad bahaka bane. Shikenan kya mutu da bakin ciki. Allah baku zaman lafiya suka mike suka barni agun.
 Ahmed ne yashigo da gudu nazo da zummar namar oyoyo .wani irin hankadanani yayi.yanunani da yatsa kishiga taitayinki.saiga aisha alka tafito cikin rangwada da kissa gajeran wando da vest a jikinta.dagudu ta rungumeshi shima ya lalumota kawai suka hau kiss. 'auzubilla nake fadi, mikewa nayi nabargun, abin bakinciki yadameni yanzu watana biyu da aure anma duk na sukurkuce narame.nadawo wani iri.ahmed yajuyamin baya.kamar bashiba.daga hantar sai mari sai zagi sai duka. Aisha tadawo tamkar matar gydan. Daya bayan daya ta rinjaye danginsa .baa ganina da gashin ido.ko taro zaaje anrika zamba dani ana nunani.abin yadameni. gashi innata tamin horo dakar na kuskura nagayawa kowa sirrina. A dangin ahmed hajiyarsa ce kawai take sona. To itama tana canada sunje aiki itada da alhaji.
Credits Benazzir

Add 08066680993 on whatsapp for more update and subscribe for http://insidearewa.blogspot.com stories





Feel Free To Comments Here...

No comments:

Post a Comment