Rundunar 'yan sandan jihar
Kano ta ce za ta sanya kafar wando daya da ma'abota shafukan sada zumunta wadanda
suke cin mutumcin jama'a da yin kalaman tayar da tinziri.
Kakakin rundunar 'yan sandan
jihar Kano, SP Majia, yace rundunar ta shirya tsaf wajen magance wannan
matsala, inda ya ce sam ba daidai bane wasu tsirari su ringa amfani da wannan
kafa wajen yin batanci ga masu mutunci ba, yace
wasu na amfani da wannan kafa wajen zagin malaman addini da shugabanni ta
hanyar hada hotunan su da matan banza ko dabbobi da yin zantukan da basu kamata
ba.
SP Majia , ya
kara da cewa rundunar zata samar da kwararrun jami'anta da suka iya amfani da
wadannan kafafen sada zumunta na zamani tare da basu duk abinda ya kamata domin
subi sahu da gano masu aikata wannan mummunar dabi'a ta zagi, cin mutumci da
wulakanta al'umma.
Yace duk wanda aka za'a dauki matakin ladabtarwa akan shi, ko dai aja masa kunne tare da gargadi, ko kuma a gurfanar da ko waye a gaban kotu.
Yace duk wanda aka za'a dauki matakin ladabtarwa akan shi, ko dai aja masa kunne tare da gargadi, ko kuma a gurfanar da ko waye a gaban kotu.
Check our new Website more updates http://insidearewa.com.ng/
No comments:
Post a Comment