Thursday 19 April 2018

Rundunar 'Yan Sandan Neja Ta Kama Gaggan Barayin Da Suka Addabi Jihar



Daga Comrade Zakari Y Adamu Kontagora
A kokarin kawar da aiyukan ta'addanci bisa ga umarnin babban sufeton 'yan sandan Nijeriya Ibrahim Idris, rundunar 'yan sandan jihar Neja ta yi nasarar kama wasu gaggan masu laifi da suka hada da barayin shanu, masu garkuwa da mutane, barayin motoci, fyade, da wadanda suka mallaki bindigogi ba bisa ka'ida ba.
Rundunar tayi nasarar kama wadanda ake zargin ne a wani kwarya-kwaryar samame da ta gudanar a kananan hukumomin, Suleja (Madalla), Mashegu, da Tafa inda ta kama mutum 19 tare da makamai a hannun su, kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan na Jihar Neja Abubakar Dan Inna ya tabbatar.
Daga cikin wadanda ake zargin sun hada da Ali Muhammad dan garin Sawmil a karamar hukumar
Mokwa da Isiya Hassan dan kauyen Bodiga a karamar hukumar Mashegu wadanda sukayi garkuwa da Umar Alhaji Manu inda suka karbi kudin fansa N170,000.
Sai Tukur Ibrahim mai kimanin shekara 35 dan karamar hukumar Borgu da Tambaya Bello mai kimanin shekara 22 dan karamar hukumar Mashegu wadanda ake zargi da satan shanu, an ansame su da bindiga kirar AK47 guda uku da harsasai guda 8, kakin sojoji, da shanu guda 14 da tumakai 20, awaki 12 da wayar salula guda 2.
Da wadanda ake zargi da aikata fashi da makami da mallakar makamai ba bisa ka'ida ba, da suka hada da Kingsley Eze dan garin Zugurma a karamar hukumar Mashegu da Fatima Musa 'yar karamar hukumar Kebe ta Jihar Sokoto da Audu Dambo Baumi Maikunkele dan karamar hukumar Bosso, Aminu Abdullahi Maikunkele dan karamar hukumar Bosso, Muhammad Abdullahi Maikunkele dan karamar hukumar Bosso. daga cikin abubuwan da aka samesu dashi sun hada da kananan bindigogi kirar gida guda 3, harsasai 11, wayoyin salula 3, da tabar wiwi da layu.
Hakazalika rundunar tayi nasarar kama wasu gaggan barayin motoci, Idowu Olaniyi da Ona Oge wanda aka sama da motar sata kirar Toyota Carina "E" mai lambar GGE 925 APP LAS. Da Daniel Ocheku Jukwai Abuja, Abdulmalik Sani AYA Abuja, Zubairu Usman Garki Durumi Abuja wadanda aka kama da mota kirar Accura MDX Jeep mai lambar MNA 435 JB.
Sai wadanda ake zargi da mallakar makamai ba bisa ka'ida ba tare da yunkurin aikata laifi da makaman da suka hada da: Baye Maune dan kauyen Malani a karamar hukumar Borgu da Jesy Adamu Sabon Wuse, a karamar hukumar Tafa wadanda aka kama da karamar bindiga kirar gida guda 2 da harsasai guda 4, da katin aiki na jabu na hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) da wukake da sanduna.
Da wani mutum mai suna Sanusi Aliyu mai kimanin shekara 25 dan kauyen Kutiriko Fadikpe dake karamar hukumar Bosso wanda ake zargi da yiwa wata yarinya mai suna Fatima Umar 'yar shekara 10 fyade.
Kakakin rundunar ya baiyana cewar da zaran sun kammala bincike zasu gurfanar da wadanda ake zargin gaban kotu domin fuskantar shari'a sannan ya jaddada aniyar su na cigaba da yaki da aiyukan ta'addanci a fadin Jihar.


Check our new Website more updates http://insidearewa.com.ng/

No comments:

Post a Comment