Friday, 27 April 2018

Matasan Kiristoci Sun Kashe Musulmai 27 Tare Da Kona Masallatai Biyu A Jihar Binuwai

Rahotanni sun nuna cewa akalla mutum 27 ne aka kashe, yayin da wasu da dama suka jikkata a rikici na baya-bayan nan a Makurdi, babban birnin jihar Benue.

An kuma kona masallatai da kuma hasarar dukiya a harin wanda ake zargin na ramuwar gayya ne da ake zargin 'yan kabilar Tivi da kai wa Hausa/Fulani.

Wadansu da suka ga lamarin sun shaida wa BBC cewa wadansu gungun mutane ne suka "tare hanyoyin cikin gari tare da tsare mutane, inda suka rinka kashe su."

Rundunar 'yan sandan jihar ta ki cewa uffan kan bukatar da BBC ta mata na yin magana kan lamarin. Shi ma sakataren yada labaran gwamantin jihar, Terve Akase, ya ce ba shi da labarin harin.

Sai dai wani Basarake na kabilar Tivi, wadanda aka zarga da kai harin, ya ce suna iya kokarinsu domin ganin ba a kai hare-haren ramuwar gayya ba.

Wani dalibi da ya shida lamarin wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce da idanunsa ya ga yadda gungun mutane suka "tare hanyar zuwa jami'ar garin kusa da wani asibiti suna tare mutane su doke su, kana kuma kuma su yi musu kwace sannan su kashe su."

Dalibin ya kara da cewa "Hausawa ne ko Musulmi ake yi wa hakan."

Shi ma babba limamin masallacin Izala na birnin, Sheikh Shu'aibu, ya shaida wa BBC cewa, da idanunsa ya ga "gawawwakin Musulmi da aka kashe 27" a asibitin koyarwa da ke birnin.

Limamin ya ce an ji wa wadansu "Musulmin rauni da dama," ba ya ga wadanda ba a gansu ba kuma.

Sheikh Shu'aibu, ya ci gaba da cewa, an "kona wadansu masallatai guda biyu" wadanda aka gyara su bayan an kona su a rikicin baya.

Sheikh Sha'aibu ya ce yanzu dai abin ya dan lafa, kuma dama lamarin dai yafi kamari ne a wajen birnin.

To sai kuma shugaban kabilar Tivi, Tar Makurdi Chief Sule Abenga, ya shaida wa BBC cewa:

"Na san cewa akwai zaman dar-dar a Makurdi, tun bayan da aka kashe wadansu limaman coci da wadansu Kiristoci, alamu suka nuna cewa za a iya daukar fansa,"

Ya ci gaba da cewa: "amma mun yi bakin kokarinsu don tabbatar da ganin hakan bai faru ba. Kuma shi bai san cewa mutanensu na aikata irin wannan ta'asa ba."

Matashiya.

Wannan zaman dar-dar din ya samo asali ne tun a ranar Talatar da ta gabata lokacin da ta bayyana cewa wadansu 'yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun shiga wata majami'a a wani kauye karkashin karamar hukumar Gwer.

Maharan sun kuma bude wuta irin ta kan mai uwa da wabi, al'amarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 17 ciki har da limaman coci biyu.

Rikicin manoma da makiyaya dai a Najeriya ya yi sanadin asarar rayuka daga dukkan bangarorin biyu.

Rikicin ya fi kamari ne a jihohin Filato da Benue da Taraba da Nassarawa da Kaduna.

A baya gwamnatin tarayya ta yi kira ga gwamnonin jihohin da lamarin ya shafa su samar da wuraren kiwo.

Sai dai gwamnonin sun yi fatali da wannan bukata, suna masu cewa ba su da isassun filayen da za su bayar.

No comments:

Post a Comment