Wednesday 10 February 2016

Dangin Mijina Episode 1 10th February 2015

Zaune take akan tabarma tana jera lemon dazata fitar tasiyar. Inna tafito. Ke yannan baki tafi ba tun dazu? sumayya tamike tace inna na tsaya jerawa ne saboda subada shaawa. Anan tadora akanta. Tayi sallama da innar tata. Bakin makaranta taje tazauna Suna fitowa break taje kusa dasu don su samu su siya. Hartama siyarwa cas tadawo gida kasancewar lemonta fresh ne kuma tana wankewa tsaf tajera hakan yasa mutane suke ganin tsaftanta harsu saya. Kwanon tadire Tashige bandaki. Innarta tace yauma sun sayene? summaya tace eh inna. Sallama majidadi yayi wato mahaifin sumayya, Inasu adamu da nuru ne? suzo muje masallaci.

Sumayya majidadi. Yata farko kuma ta mace agun aliyu majidadi dakuma hauwau. Wacce suke kira da inna. Tanada kanne biyu maza adamu da nuru. Suna zaune cikin wadatan zuci duk da bawai suna da arziki bane. Anma kam akwai na zuci. Sumayya har shekara sha daya ce tagama primary. Sai Allah bai hore musu na secondary ba. Hakan yasa tazauna a gida tana islamiyyanta kawai. Hartazo sukayi sauka. To ranan saukansune makarantansu ta gayyaci manyan yangwamnati suzo . Ahaka summaya taci kaututuka. Aciki aka bata scholarship nazuwa boarding school Aka bata daman zaban kowanne. Murna agun sumayya kaman ta rasu. Taje sa gudu gida ta sanarwa innanta sun kasance cikin murna a inda aka kawo makarantu uku ta zaba. Ko special school dake garin bauchi. Ko hassan gwarzo dake kano. Kokuma FGGC dake damaturu. Ganin tana bauchi yasa tazaba special school abinta.a satin admission dinta yafito. Inna tafara kintsa mata kayan yan boarding dai-dai karfinsu kaman: Su kanzone, Su gari ne, Su kulikuli. Aka zuba mata acikin akwatin ta na gwangoro. Tadauko kayan sallanta tazuba aciki. Ran lahadi suka shiga motan kasuwa da ita da majidadi. Suna zuwa majidadi yakai admission dinta. Registrar makarantan yayi sign, Sannan yace badamuwa zai iya tafiya ita kuma ta je hostel dakyar ta iya daukam akwatin. Mutumin yace inkinje kice akaiki A garba anan hostel din zaki zauna.. Tana zuwa ta zube agun da ita da kayanta. kowa sai hidimansa yake. Taga kowa taci hijab tayi hanyar wajen hostel. To ina zasuje? sai tashare kawai. Tarasa agunwa zata samu tayi tambaya. Tana haka saiga wata tazo wucewa kawai tadan tabata. Baiwar Allah don Allah inane A.garba? tayi mata wani irin kallo. Sannan tace up ko down? sumayya batare datasan me take fadaba ta amsa da to.
Tace biyoni muje. Haka kuwa akayi tashiga da ita sannan tamikata gawani gado. Kai yan dakinnan idan Summaya Malanjo tazo takuce mata ni nakawo mata new cormer. Sukace to tafice tabarni agun. Nazauna akan akwatina. Ina kalle kalle daga masu cin abinci sai masu tadi sai masu guga da iron din charcoal wasune suke shigo da gudu suna cewa kaiii yan dakinnan bazaku shirya kufuta arabic class ba? Sai yan dakin suka rikice suka fara gudu suna fita sukuma wannan matan suna binsu ganin haka yasa nima na rude Indauki akwatinane intafi dashi kokuma inbarshi? inacikin wannan tunanin wata ta cafko hannuna ke kiyi gudu mifita karsu miki duka. Nabita da gudu saida muka bar wannan fannin sannan muka dan nutsa tace meye sunanki? Sumayya Majidadi nikuma sunana zafyra Danbaba. Na dan gyada kai saiga watama ta fancako da gudu zafyra baza kuyi gudu ba! Zaarfe gate ba shiri zafyra ta fincikoni mukabi wannan din. Anma ina munyi latti donmu samu anrufe gate din anfara tarat latti. Nan wannan tafara narai narai da ido. Sai zafyra tace ke furyad wallahi kincika tsoro. Bulala biyu nefa. Furyad tace kut toki karbamin .kinsan sarai Ba da dadi zasu manaba. Nikam dama har kwalla tafitomun zafyra ta kwashe da dariya tace furyad kiga yaruwarki harda hawaye nan akazo kanmu Zafyra tamika hannu tashige. Aka kira furyad ana mata daya ta doka tsalle. Ina ganin haka nakara rudewa. Wata daga cikin seniors din kawai tafara dariya nakalleta a kasafai. Tace canavaro kizo kiga student dinki har da fitsari! Nanfa aka taru akaina ashe nayi fitsari bansaniba hakan ya matukar basu dariya. Sai dayan ta tambayeni meye sunanki? Ido na fal cike da hawaye nace Sumayya majidadi. Tace ayya awani hostel kike? Sai na tsaya ina kallonta bance komaiba. Tace yaushe aka kawoki nace yau. Tana cikin magana saiga wacce dazu takaini. Daki tazo wucewa da babban hijab. Sumayya malanjo. Yar kwananki ne fa. Sumayyan takalleta tace banganeba tace ae. Dazu nakaita yar A.garba ce. Kayanta na kwananki saiki duba mata gun zama. Shine tajani tace badamuwa mukaje hostel. Tace kayanki ne wannan! ? Nace ae nawane. Tace to ga gado nan. Anan zaki zauna. Inkina bukatar wani abu saikizo guna ko takwara na? Tafada tana murmushi wanda wushiryarta saidaya fito nace tom nazauna na kimtsa kayana da jikina har aka dawo anan naga ashe agefen zafyra da furyad aka hadani. Tun daga lokacin muka dawo kawaye tare muke yawo. Duk da cewa duk sunfini auki ni tsayi kawai nafisu. Zafyra anma tafi furyad jiki saidai furyad tafi zafyra haske. Furyad irin matsoratannanne. Kuma criminal ko aika zaayi saitace mu zalle inbamu yaddaba sai ta zalle abunta. Criminal ce sosai. Bata taba yadda taje aika kullum a escaping take. Zafyra kuwa ana cewa abu to zatayi obey before complain ce sosai acewarta duniyan nawane dahae zamu takura makanmu? ajinmu daya sannan seat dinmi daya. Tare muke wanki muke guga mudebo ruwa. Hatta abinci tare mukeci. Duk dana fahimci cewa daga furyad har zafyran yan gidan masu akwai ne. Baabunda suka nema suka rasa. Anma dangantaka dani bai damesuba suna budewa muci. Har ranar ziyartar iyaye tayi yakasance nikadai ce ba'azominba anma duka anzomusu tare mukayi komai basu gwadamin komai. Sannan ita anty summaya malanjo tana lura damu sosai ashe sunhada dangantaka da furyad shiyasa bama wani shan wuya
Har muka dawo gida hutu, Inna tayi murna sosai ganin ban rameba. Nima naji dadi. A gun nabasu labarin makarantan dakuma kawayen danayo innata taji dadi sosai haka abbana. Lokacin komawa dayayi muka shirya tsaf muka koma.a daddafe muka gama shekarar mu tafarko.tabiyu .harta uku. Yanzu mundawo JSSCE. inda zafyra da furyad sunmin alkawarin zuwa nace musu to. tunda nashiga secondary innata bata. Kara dauramin tallaba. Acewarta na girma. Yanzu a gda muke sanaarmu kuma ana ciniki. Watarana nafito daga masai kawai naga takalmin yan gayu adakin. Tare dajin muryoyi wanda nasaba jinsu bakuma zanmanta dasuba. Nashiga dakin su zafyra ne da furyad muka fara ihuuu muna tsalle atake nadaura musu abinci ba kyankyami sukaci, muka ci hiran mu sannan suka mike zasu tafi anan inna tamusu goma na arziki sukaji dadi. Mukayi sallama kwanci tashi muka koma aji hudu inda muke ganin muma munfara girma hakan bakaramin dadi yamanaba. Muka kama gun zama tare mu ukunmu dama yanzu a makaranta anshaidemu mu ukunmu muke komanmu. Da sati biyu muka fara shiga aji a lokacin aka kawo sabbin yan bautan kasa.sukayi introducing dinsu a assembly muka wuce aji. To ranar maths muke dashi donhaka nafitar dakomai na, na maths na aje akan table nice dama a tsakiyansu zafyra na gefena na dama furyad kuma tahagu.yashigo da bakin glass a manne a fuskarsa muka mike gaba daya muka gaysheshi.bayan munzauna batare daya jiwo yakallemuba yace 'you know that cewa maths zankoyar. A zuciya na nace yazaayi musani mu almunsuru ne? kaman yaji mezance yace saboda i said it a assembly. Nan kowa ta nutsu saboda wannan ba alamun wasa a tare dashi. Yamana drawing shapes yazubo calculation dinsu. Na dauko pencil dina nazana sai naga nayi kuskure namika hannu zandau cleaner zafyra tace narigaki ai. Nikuwa nace wallahi saina fara. Haka akayi kuwa na fizge itama ta fizge munatayi yajuyo yace meye kukeyi haka kaman karnuka? raina yabaci dawannan kalman yasa ko kallonshi banyiba idona a kasa. Zafyra nema ta tsaya tana mishi bayani yace will you shut up you black fool!! Kutashi kubarmin aji. Nadago nakalleshi. Sai ya sare alamun jikinsa yayi sanyi komeya gani oho. Aa saiyakara bata rai. Meye kike zuramin ido da idanuwanki kaman na mage. Tashi ku fice. Namike sulum sulum mukafita. Munafita zafyra ta kwashe da dariya. Tace idon kulya hehehe.
To be continue....




Add insidearewa blog official whatsapp number 08066680993 for more updates

Credits To Benazzir

Feel Free To Comments Here...

No comments:

Post a Comment