“Jinin Jikina Episode 2
Isa ya muskuta ranshi yagama baci yamike yafice. Kuka Ali
yasaka shikadai yasan abunda ke damunshi. Kokadan nadama bata ranshi don
aganinshi abunda yakeyi shine daidai.
Wata rana nana tafito makaranta ali nabiye da ita. Wani mota
ne ta tsaya daidai ali. Hakan yasa nanan tayi sauri gudun karma yaganta yamawa
ali magananta. Don tafara gajiya da ganin kattan dasuke hawa kanta. Ta tsallake
titi yayinda shikuma mai motar ya tsaya gun ali sukadanyi magana.
Can ya karaso gunta yana wani sham kamshi don tsabar iskanci
meye nawucewa kibarni?. Tuni ta tsorata dashi. Ganin yanufo kanta dagudu tahau
kan titi. Yana naaaana kisauko. Anma ina! Motar datake bayanta tuni tadaga da
ita. Shikuwa gigice wa yayi yanufo kanta yafara balbale mai mota da masifa.
Ibanda rashin lura yaza’ayi ka kadeta mai motan yafito wani saurayi fari
kyakkyawa tuni yanufa kanta batare daya lura da abunda shi ali ke fada.
Daukanta yayi zai sata motan. Juyin duniyannan yayi ali yariketa anma ina
yagagara. Wasune suka taimaka acikin yan tsirarun mutanen dasuka taru don ganin
meke faruwa. Aikuwa kafin ali ya hankara har mai motan yawuce. Tuni yatari
mashin don yabishi. Traffic shi yarabasu haushi da takaici kaman yaci kanshi.
Tayaya zaigane wani asibiti aka kaita? Kokuma wani guru zaije da ita?
Shikuwa tuki yakeyi duk hankalinsa
atashe lallai yau idan yar mutane tamutu yazaiyi?. Asibiti yanufa tuni aka rufu
akanta emergency akayi da ita. Addua yakeyi, zufa na kwaranya ajikinsa. Akalla
bayan awa daya saiga likitan yafito tuni yace masa suna bukatar jini leda uku.
Bashiri yace a debi nasa. Aka gwada jini aka ga yazo daya tuni aka deba . Shima
aka bashi gadon don yahuta. Kwanan nana uku bata farfado shikuwa tuni yakira
iyayensa yafada musu. Sunmasa jaje sosai. Tare da mata addua. Adaren ranan
tafarka . Budewa nafarko bata fahimci a inda takeba. Sai can tadaga hannunta
zata dora akai tuni taji zafi nan danan kuwa tayi yar kara. Dasauri yamike a
tsaye yakaraso kanta. Sannu . Idonta tabude takaleshi. Akaro nafarko kenan daya
mata asalin kallo. Lalle Allah yayi halitta anan. Dubi manyan ido agun
yarinyanna. Shida zuciyarsa sai tadi sukeyi. Yadan muskuta tareda cewa barin
kira miki Dr. Yana fita yakira likitan
suka shigi ajere. Nan likitan ya gwadata sannan yace. Abinci zataji tasha wadannan
magungunan zata warke insha Allah. Nan yayita masa godiya.
Yafice yayinda shikuma yazauna yafara
hada mata tea. Yahada mata mai kauri. Nana kuwa tsaf karantanshi takeyi. Itadai
don kar ace tayi karyane anma dazatace bata taba ganin namiji mai kyau irinshiba.
Yanda kasan shiya kera kanshi. Yazuba mata tare da dagowa yana cewa kisha
zakiji dadi. Kawar dakanta tayi. Aikuwa tuni yagyara zama yafara lallami. Kinga
kin rame kinyi kashin wuya. Duk kindawo wani iri. ‘Please i think u should take
It’. Kallonsa take wow. Turancinsa ma yanda kasan balarabe irin yanda laravawa
suke turanci. Tagirgiza kai. Can dai yarasa yazaiyi yace mekikeso?. Tayi shiru
kamar bazata amsa ba can tace meye sunanka? Dago wa yayi yakalleta dakyau
sannan yagyara zama yace sunana AHMED SULTAN. Anma abokai na sunfi kirana da
sultan. Tayi shiru sannan tace uncle sultan. Baisan sanda ya kwashe da
dariyaba. Noooo am not old. Just call me with my name please. Tadanyi murmushi
sannan tace yaya sultan. Yayi murmushi saboda dadin daya ji yau ancemasa yaya
kasancewarsa da tilo agun iyayensa. Yace naji dadin sunan. Takaleshi jiran
yakarasa anma yayi tsit. Tadan muskuta zata gyara zama tare dacewa wash! Wayyo
Allah! Dasauri yamike tare da gyara mata. Yahada mata tea da ferfesun kayan
cikin tare da bata yana bata tana kurba yana bata tanacin ferfesu. Wasa wasa
taci tas takoshi.
Yafita yanemo nurse tare da cemata
bari yaje yadawo. Nurse ta taimaka mata tayi wanka tsaf. Yasiyo doguwar riga
mai kyau daga gani yasha kudi tasaka tsaf. Ta bala’in yin kyau sosai. Nanda nan
ramarta tafito anma tayi kyau. Ta kallabe dankwalinta tazauna agefen gadon.
Nurse din tanemo mata sallaya ta tashi tabiya sallolin dake kanta. Ta idar
kenan. Tashafa addua ta dade tana addua wa mahaifiyarta dakuma halin dasuke
ciki. Takuma roki Allah yanuna mata mahaifiyarta anan kusa bada jimawa ba. Tashafa
tare damikewa takoma kan gadon tazauna nurse din tamata sallama tafice. Minti
kadan saiga sultan ya shigo. Yanemi gu yazauna tare dacewa sannu. Ta daga masa
kai. Yace ina marar lafiyar take?. Tace wacce marar lafiya?. Yamike yabude kofa
yagadai tabbas dakinne ba batan hanya yayiba? Yadawo yakura mata ido. Tabbas
itace dama haka take da kyau?. Gabanshi ne yaketa faduwa. Dasauri yakira sunan
Allah tare dacewa aiban ganekiba. Sannu yajikin. Murmushi tayi tare dacewa
dasauki. Yace marar lafiya kinyi sallah? Tace sunana nana aisha abbakar turaki.
Yakalleta dakyau sannan yace nice name.
Akwai wani abokin babana abbakar turaki.
Dasauri tace to bashi bane. ‘Ni babana ya rasu’. Dasauri yace oh am sorry Allah
yajikansa! yamasa rahama ameen ameen. Tashare hawayenta don yatuna mata da rayuwarta.
Hankalinsa yatashi don ganin hawayenta please dear meya sameki?. Batace
komaiba. Nan yafara lallaminta. Har aka kira magrib yamike yaje yayi yadawo.
Itama anan tayi. Bayan yazauna ne yace inaso kigayamin inda donginki suke
donnasan hankalinsu atashe yake aduk inda suke kigayamin insanar musu kobahaka
ba? Nanfa tafara sabon kuka tare dacewa banda kowa ni. Nan yaji tausayinta yace
kiyi hakuri toh zankaiki gidanmu kizauna. Nan ta girgiza kai tare dacewa toh!.
Ali kuwa hankalinsa yayi dubu duk
yatashi yanufi gida gun umma aikuwa yana zuwa yasameta yasanar da ita. Nan
hankalinta yatashi tafara fada. Tana hawaye dama kanata nakasa rayuwan
yarinyannan yanzu bukatarka tabiya kakashemin ya. Yanzu wayasan wanda yadauketa
nagarine ko bata gari?. Kuka take sosai. Ali kuwa saibada hakuri. Baitaba dana
sanin abinda ya aikataba harkuwa yanzu shi azuciyanci murnan barinta yakeyi
bakin cikinsa daya ganin cewa bugeta akayi a mota baisan ko tasamu lafiya ko a
a ba, anma yajima yana addua Allah ya nesantar da nana daga gareshi sanin halin
dasuke ciki.
To be continue insha Allah next
week…..
Godiya ga Binazzir
http://insidearewa.blogspot.com for
more
Feel Free To Comments Here...
No comments:
Post a Comment