Saturday, 2 July 2016

Halaccin Sarauta episode 31

Continuation of Halaccin Sarauta episode 31

To read the previous episodes click HERE


Bai amsa tambayanta ba yace "yajikin naki? karki kara magana" bata kara cewa komi ba, tana tunani ne taga waye yabata, taga yusuf garau donhaka tasan bashi bane, sufyan ma taganshi tasan bashi bane, taga inna taga antyn abuja duk sauran tsofi ne donhaka taciresu a lissafi, saikawai tasa aranta na siyarwa aka saka mata, nan tafara adduan Allah yasaka da alheri wa duk wanda aka samata kidney dinshi, yusuf yaki motsawa agefenta itakuma idonta zur akansa shima hakan jiyake kaman ya hadiyeta, inna ne suka shigo anma duk dahaka yusuf yaki matsawa saidai kowa yagaidata daga nesa.

Sufyan daya shigo yaganshi yasan meyakeji donhaka yajashi dakyar yace yaje yahuta ganin sufyan yadage yasa yusuf yanufi dakin likitan ranshi abace yatuna da tsohon bacin ransa, likitan yazaro ido don yaji labarin yusuf yasan mesuka aikata donhaka tuni yashirya dazuwansa , zama yayi akan kujera sannan yace masa "inaso infarajin bayani daga farko meyasameni , me kuma kuka shuka da gimbiya kuka min karya!, " yayi gyran murya sannan yace "yarima duk abinda yafaru kadaukeshi kaddara tun asali dana dubaka kai kanka bakada ishesshen lafiya, abubuwan dakake sha sundan maka lahani kadan, kidney dinka basu da lafiyan dazaka bawa wani, ana cikin haka kuma mahaifiyarka ta isar da sakon karmu cire, dafatan zaka fahimceni" yusuf bai ce komi ba yatashi yanufi kanshi fitsarine likitan baiyi a wando ba domin ya mugun tsorata yusuf yariko kwalan rigansa sannan yace "daga yau duk abunda yashafi aliya, babu wasa aciki inaso kasan dahakan" Juyawa yayi yabar office din dakin da aka kwantar da abdullahi yanufa idonsa biyu yanaso asallameshi anma likitan yace bayanzu ba saiya kara samun sauki donhaka duk asibitin tahau masa kai,

Yan biyu ne hassana da hussiena suka shigo kowacce taci kwalliya dakin da abdullahi yake aka nuna masa suka gaysheshi da jiki sannan suka ajiye ledan hannunsu yusuf yafita alokacin, harzasu wuce abdullahi yace kucika ladanku mana ku gayda aliya, hussiena kaman tace a a anma tana kunyan abdullahi donhaka tace masa toh, dakin da aka kwantar da aliya suka nufa, idonta biyu bakowa a dakin sai inna suka gaysheta kamar abun arziki sannan suka nufi gadon aliya hassana tagaidata yayinda hussiena ke mika mata sakon harara, aliya murmushi tayi don tasan dalili, can dai hussiena takalli tareda cewa "anma kinsan yarima yayi asaran kudin tara? Ace wannan zaicire sauran kodan shi kwaya daya yamika mata? Dasunan soyayya? Mayya duk yaran sarkin kin mamaye" inna ce tanufo kansu tareda katseta tanacewa "kuyi hakuri baason daga mata hankali" aliya ce ta katse ta tareda cewa "wani yarima?" Hassana taja tsaki tareda cewa "wanne kuwa abdullahin dakika nakike wa" wani nauyi taji akanta kaman ansauke mata dutse


To be continue....

Godiya ga Benaxir Umar da ta rubuta.

No comments:

Post a Comment