Wednesday, 20 July 2016

Hallaccin Sarauta Episode 35

Read the previous Episode Here

Mota ya fizga dakarfi sai alokacin aliya taga jikinta ajike anan ta tabbatar da aefa fitsari tayi anma wayake tanan yanzu, tunda kayan jikinta ba nunawa zaiyi ba goran ruwa tagani a motan tabude ta watsa ajikinta, fada yanufa dasu suka sami gurin acike, dakayar yasamu gun parking yana tafiya aliya tabi sahunshi fannin yakolo suka nufa wacce babu matsaka sinke ancika, tundaganan jikin aliya yayi sanyi komawa tayi tazauna, agefe wasu hawaye masu zafi suka fara bin kumatunta sufyan ne yakamo hannuta suka shiga shima dataimakon hauwau. Wacce tanuna cewa su yan gida ne suna shiga dakin acike agefe aliya ta tsaya sufyan yakarasa gun, abdullhi ne akwance agun macecce, duniya inazakije damu, mun aikata alheri mun mutu munbarta, dole kowani rai mamace ne, sufyan durkusawa yayi agun tuni dogarai sukayi gefe dashi don baabarin kowa kusa da gawan. Yakolo ma ba kanta dakyar aka danneta, aliya kuwa wani kyalli kyallu take gani a idonta tuni ta fizge dankwalin kanta tajuya dagudu zata nufi kan gawan rikota akayi, tuni sufyan shima yamike yarikota yusuf wanda ke can kuryan daki tuni

yafito ganin aliya tuni ya nufa kanta rikota akayi anma yadda kukasan karfin aljannu gareta wani fizga datayi bashiri suka fada tabaya kan abdullahi tanufa zata budeshi anma nanma dogarai suka kara rikota, tuni umma uwar soro tace a fice da ita, daukanta cak akayi akafice da ita, wani irin kuka takeyi wanda duk mai kallonta sai ya tausaya mata, itakanta tadawo abun tausayi , sumbatu takeyi "yarima meyasa zakamin haka? Yarima meyasa zaka tafi baka amsamin tambayoyin dake raina ba? Kasan cewa sanadina kamutu anma baka gayamin hujjanka ba! Innalilahi wainna ilaihi rajiun!" Kuka takara fashewa da, yusuf ne yajata, yasa aka nemo bilkisu tarikota suka koma gefe acewarsa akaita fanninshi harsaitayi shiru kafin tashigo cikin jamaa, Anyiwa abdullahi wanka yadda ake kowani mamaci, abdullahi kuwa yasha fatan alheri agun alumma, iyayensa sun sakamishi sunkuma nema mishi aljanna, hatta mtanem gydan dsuke karkashinsa suna aiki kowa alheri yake fada akan abdullahi, duk wanda yazauna da abdullahi yasan mutum ne mai tausayi, marar son fada, mai son gaskiya, mai adalci mai kuma bin hakkin dan adam, matarsa da mahaifiyarsa sunbada kyawawan shaidu suma akansu, a inda sarki dakanshi yake jawabi amfanin zuwa duniya kenan, kazamto nai kyautatawa mutane , kazamto

mai tausayi karkace don kafi karfin wane, ko wane yana aiki akasanka ka wulakantashi , kasani cewa shaidun duniya shine shaidan lahiranka, muguji duniya muzamto masu shiri akowani lokaci don ziyartar kabari, musani cewa aikin damukayi duk yana cikin littafanmu, yakuma yi jawabin cewa kar mutane suce don abdullahi yabada kidney dinshi shiyasa yamutu, wannan bahaka bane lokacinsa yayi, daya bada da bai bayarba dukka Allah yayi zaimutu yau, kuma mutane susani cewa akullum idan aka tambayi abdullahi maganan kidney dinshi da dalilin bayarwa yanada hujjojinsa anma babbar hujjarsa itace yayi alkawari kuma a matsayinshi na dan musulmi, na wanda yataso cikin mutunci da daraja a matsayinsa na balagagge wanda yasan hukuncin marar cika alkawari hakan yasa yacika alkawarin, kuma shi sarki yana alfahari dashi hakkika abdullahi abun koyi ne, Allah ya sa mucika da imani Ansamu ankaishi makabarta kafin sudawo aliya tasuma yakai sau uku, haka kawai takejin haushin kanta gani takeyi kaman itace musabbabin dalilin dayasa abdullahi yarasu, dakyar aka mata alluran bacci tasamu ta kwanta Sufyan kuwa abun duniya tamasa yawa dawanne zaiji, mutuwan amininsa kokuma bincikowan dayayi cewa hussieni shiya kashe mahaifinsa da mahaifiyarsa, dawani ido zai kalleshi duk yaga missed call dinsu anma bai dauki ko daya ba, atunaninsa basuda abin fada mashi gun inna yanufa yatarar tana kan sallaya tana ganinshi tashafa addua tareda cewa "sufyan ya akaji da hakuri?" "Alhmdlh" "Allah yajikanshi yamishi rahama" "Amin inna, dama nazo muyi maganane akan alh.hussieni" "Inajinka" "Kinsan shiya kashe iyayena shiyasa kika boyemin ko?" "Hmnm abdullahi kenan, rasuwa fa aka maka yakamata kayi hakuri ai yanzu ko" "Yanzu nakeson kifadamin amsata" "Nasani. Sannan alh.hamidu ma yasani, munga babu amfanin gayamuku ne,kuma nagayamaka anan nagayamaka, sufyan kadaina bincike, addininmu ma batason irin wannan binciken, tasar da kwantaccen magana,ana zaman lafiya kunje kun binciko abunda zai hanaku zaman lfy, yanzu dakasan cewa shine mezakayi?" "Lallai inna kinban mamaki, tambaya kikayi mezanyi? Kotu zamu shiga!, bazan hakura ba harsai anyiwa iyayena adalci, kina nufin

muna ji muna gani ankashe iyayenmu a banza kenan? Da ke! Da duk wani wanda yakeda hannu aciki wanda yasani da komi duk sainakaiku kotu, zaku fuskanci hukunci " Baikulataba yafice duk da ta tsorata tana kokarin yimasa bayani, fada yakoma har lokacin ance aliya bata tashiba ganin yusuf yayi donhaka yaje shima yazauna agefensa, yusuf na zubarda hawaye yace "kasan dalilin da yabata kodan shi?" "Nasani" "Menene" "Don yamata alkawari zai kareta koda ranshi zai cire yabata" "Bayan haka" "Yana sonta!! Itace mace tafarko daya fara so a duniya" Yusuf dama yasan dahakan yana son ya tabbatar dinne, ajiyan zuciya yayi wanda shi sufyan yagagara ganewa ko na farinciki ne ko na bakinciki Acan cikin fada kuwa fannin falmata jakadiya ce tashigo tana murmushi, falmata ta kalleta itama murmushin take, jakadiya tafada kasa tana kirari Sai ke Jaruma a cikin jarumai, jaruma acikin jagororin ma jagoranta Idan akaji ance kasaita in anduba kin cancanta taimako dare zuwa rana kin sabayi wa al'umma mai dukiya mai ran karfe Mai kudi uban matsiyata baki fushi ko anzage ki Baki zagi ko anzageki ja muje kece gimbiyar magimbiyata kara masu kece babbar su Mai girma agidan girma sannan kuma matar mai girma,uwar gida a gidan mai girma,Mai hidima a gidan hidima sannan kuma matar mai hidima, farin cikin mai hidima, zuciya hasken annurin mai hidima, zakanya saidai aganki anesa badai a matso kusa ba," Wani irin murmushi da dariya falmata tayi cikin jin dadi, ta daga giranta sama sannan tace "kinga na kashe da' saura uwarsa sannan uban gayyan uban gidan, yusuf shine sarki ba waniba"

To be continue....

Godiya ga Benaxir Umar da ta rubuta.

No comments:

Post a Comment