Saturday, 31 March 2018

An Kama Barayin Shanu A Jihar Taraba


Jami'an sojojin dake farauta a garin Mambilla sun yi nasarar kama wasu barayin shanu su shida tare da gano shanu 30 a garin Mayo-Ndaga dake karamar hukumar Sardauna a jihar Taraba.
A yayin da yake jawabi a lokacin da ake gurfanar da wadanda ake zargin, kwamandan dakarun sojojin, Laftanal Kanal Sani Adamu ya bayyana cewa an kama barayin ne a wani daji dake yankin a yayin da suke kan farauta.

Ya ce wadanda ake zargin sune: Hammanjulde Yahya (50), Umaru Yahya (40), Paul Samuel (35) Juli Adamu (30), Ibrahim Yusufa (27), da kuma Usumanu Buba (25).
Ya kara da cewa an kama su ne dajin Nyogor a lokacin da suke kan raba nama shanun da suka sato.Check our new Website more updates http://insidearewa.com.ng/

No comments:

Post a Comment