Saturday, 31 March 2018

Dalilin Da Ya Sa PDP Ta Nemi Gafarar Al'ummar Nijeriya — Fadar Shugaban Kasa


Fadar Shugaban Kasa ta shawarci al'ummar Nijeriya kan su yi takatsantsa da gafarar da jam'iyyar PDP ta nemi a gare su inda ta nuna cewa jam'iyyar ta yi haka ne saboda tana son sake kafa gwamnati ta kowace irin hanya.

Kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu ya ce har yanzu PDP ba ta karbi laifinta na wawushe arzikin kasa inda jam'iyyar ta bayyana shirin yaki da rashawa na gwamnatin tarayya a matsayin na wulakanta abokan adawar siyasa don haka babu wanda zai amince da wannan gafarar da suka nema.
Ya kara da cewa gwamnati na kalubalantar PDP kan su bayyanawa al'ummar Nijeriya adadin kudaden da suka sace sannan kuma su maido da wadannan kudaden wanda daga nan ne, al'ummar Nijeriya za su gafara masu.Check our new Website more updates http://insidearewa.com.ng/

No comments:

Post a Comment