Continuation of Halaccin Sarauta
To read the previous follow the link Halaccin Sarauta episode
"saketa!" Aikuwa aliya tajita akasa dasauri yusuf yanufeta yadagota zaifice da ita budan bakin falmata tace "zandaga maka nono yusuf, wlh inka kuskura kabita zandaga maka nono" cak ya tsaya ji yake kaman yayi hauka. Alokacin aliya tajanye jikinta tareda cewa "zan iya tafiya badamuwa karka damu" fitanta sashimsu tanufa inda kowa kallonta yake alamun tausayi bata kulasu ba takwanta, alokacin jakadiyar yakolo tazo ta dubata, acewarta yakolo na gaysheta da jiki, fitanta kenan alokacin yusuf yabar gydan don baiga amfanin zamansa ba, gydan aliya yanufa anan yakwanta yasha giyansa, barci ta kwasheshi, falmata kuwa tarasa yazatayi gwara tun wuri takauda aliya donhaka ta umurci azo da aliya, dakarfi aka kamo aliya tana kallonta aliya duk tacanja kamanni, falmata ta umurci da adauko bulali nan aka baza aliya ta kwashi dari masu karfi da zafi, tunda mahaifiyarta tahaifeta bata taba shan wannan azaban ba, aka kwara mata ruwan sanyi, falmata tace "sakamakon da ake samu kenan idan mutum yashiga hurumina," suma aliya tayi anma haka falmata ta umurci a watsa mata ruwan sanyi tana farkawa aka daure hannayenta tabaya da kafafunta aka kwantar da ita akasa,tasa aka dauko kankara aka jera mata a cinyoyinta,kakkarwa take, duk tafita hayyacinta burinta baisamu yacika ba zata mutu, dukka wanda yakegun dole yatausaya mata. Bilki ce taruga da gudu fannin yakolo tasanar da ita abunda ke faruwa, bashiri yakolo tafito isowanta gun tace akunceta falmata takalleta sama da kasa tareda cewa "a matsayinki na wacece?" Yakolo tace "a matsayinta na baiwa ta!, inbaki manta ba ai kinkoreta nadauketa!" Faalmata taji kaman ta makuro wuyan yakolo tsaki taja tare dacewa "zanga wanda zai daina abunda nasashi,inku jahilai ne takoma tazauna a kujera; yakolo tayi murmushi dakanta tanufi kan aliya ta kunceta. Tarungumota sannan tanufi fanninta da ita, falmata tsaki taja tabar gun tareda zagin bayin, A fannin yakolo ta aika aka kira likita yaxo yamata dressing jikin yabata magunguna, abdullahi ne yashigo ya tsorata ganin yanayin datake ciki, tana bacci anan sukayi shawara da mahaifiyarsa ayadda zasu yanta aliya,
To be continue insha Allah.
Thanks to Benaxir for sharing with us, for more follow the link
To download Inside Arewa application for easy access follow the link http://www.ambictproviders.com/InsideArewa.apk
No comments:
Post a Comment