Continuation of Halaccin Sarauta episode 13
Previous episode of
Halaccin Sarauta episode
Tana farkawa tayi mamakin ganinta afannin yakolo anma yakolo ta gwada mata bakomi, sallolinta tayi a zaune don bata iya tashiba, abdullahi duk tausayinta yacika sa gashi haryafara tsanar kansa yasan tabbas yasan aliya anma yamanta aina ne? Wannan wacce irin mantuwa ne, Yusuf bayan farkawanshi wanka yayi yacanja kaya sannan yarufo gydan yadawo fada, atake yafara neman bilki cikin kuka tasanar mishi da abunda yafaru, ranshi abace yanufi fannin mahaifiyarsa donjin baasi kamar kullum cemasa tayi "inzaka shekarana kana neman yanmatan da basu daceba baxan gaji da koransu ba, kanemo mai tushe mai asali,
" baice komi ba yafice , fannin yakolo yanufa wanda kowa saidayayi mamaki yagaysheta sannan yace "nazo daukan baiwa tace " tagane meyake nufi anma tace "wacce baiwar fa?, " yayi shiru sannan yace "marar lafiyannan aliya" tace "au! Aibansaniba kamanta mahaifiyarka ta koreta ne? Ni na karbeta, kuma daga yau na yantata donhaka daga kai har mahaifiyarka bakuda dama akanta!". Zaro ido yayi yayin daya tuna kalmomin aliya na "karka yantani, karabu dani kuma ka manta dani" subhannalahi ai ta tona mishi asiri aliya batason a yantata, anma shiyasan yantata shine kadai hanyan dazai iya soyayya da ita, baice komi ba yabar gun A haka aliya taringa jinya kullum yusuf na hanyan gaysheta wani lokacin suhadu da abdullahi wani lokacin kuma da shehu, wanda baya zamaagydan saboda makaranta wasa wasa saida aliya tayi sati sannan tawarke, aranan yakolo tabukaci tagayamata gaskiya, Tagayamata cewa ta yantata , aliya batasoba anma yanzu kam shine kadai hanyan dazatabi donta rama abunda falmata tamata, dole tarama saitaji zafi ninkin abunda taji, zataga itako falmatan wazai juya yusuf, uwace ita tafita daraja anma namiji kam inkika tsuguna kika haifeshi aikinsan wa ya mace kika haifawa, domin kuwa komi mace zaifara yiwa, dadday ne masu fara tuna uwayensu. Shiyasa bahaushe yace da ki haifi gwamna gwara kinhaifi matar gwamna domin gwamna matansa zaituna kafin ke, itakuwa komi uwarta da danginta, sungama magana da yakolo inda yakolo tabata kayyaki da kudade tace tatafi garinsu don hakan kadai ne zai tsirarda ita daga gun falmata, abdullahi ne yazo alokacin yazaunar da ita yace "dani da mahaifiyata muna tunanin akwai wani igiyan dangantaka a tsakaninmu dake inbahaka ba kuwa babu yadda zaayi ni kullum ina tunanin nasanki awani guri yayin da itakuma take tunanin cewa tana kaunarki haka kawai, toh ko dai babu mudai iyakacin gatan dazamu iyamiki kenan!" Aliya tayi godiya sosai tabbas baxata manta da hallacinsu ba, ko agun bayin kuwa subilki nata kuka kowa yasaba musamman bilki tafijin jiki, da kuka suka rabu tafice tanufi gydanta ga mamakinta taga makullimta baya shiga kuma ba kofanta bane, tuni tasan aikin yusuf ne don if barawone bazai gyra kofan ba, tazauna agefen kofan tana tunanin yadda zatayi saitaji alamun key a gefenta tuni tadaukatabude taga yabude, dakin warin giya da kwalaben giya hakan yatabbar mata da cewa yusuf ne yake zuwa dakin, abubuwanta ta tattars sannan tarufo kofan, tarar machine tayi taje takama hotel kafin tasamu gida dondai tasan batagama aikintaba babu abinda zaisa tabar garin, wanka taje tayi tanayi tana kallon tabon cinyoyinta na dukan da falmata tayi tasake shower yana zubo mata, tuni tafara tunanin iyayenta kuka tayu sosai wanda saida yasamata ciwon kai tafito tayi sallah sannan takwanta wayanta takunna, msgs tagani dayawa na auntynta kusan kullum saita kirata taji yatake, tajero mata txt tareda mata adduan samun nasara, saikuma malaminta yana tambayanta yaya aikin datasa agaba? Sai daidaikum yan makarantansu dakuma invitation na bikukunan frnds dinta, bacci ne yakwasheta, bata tashiba sai bayan magrib donhaka tayi magrib tasanyo dogon abayanta tafita reception don cin abinci, tayi ordern fried rice da grilled fish, game take awayanta saikawai taga mutum yazo yazauna, bata kulashi ba shikuwa sai kallonta can data gaji dakallon tadauki wayanta tacanja sit yakara binta tuni taji abincin yafita mata akai hanyar dakinta tanufa yakuwa bita saidata fakaici mutane tarikoshi dakarfi hannayensa tawullosu tabaya tarike kara yasaka. Cikin zafin nama tace "meyekake bina?" Karan yakeyi babu daman magana anma yadaure tareda cewa "inason zama abokinki" danna hannun tayi dakarfi tare dacewa "ni ba saarka bace! Not interested!" Sakeshi tayi tareda nufa dakinta nan yafara tunani oh mace dakarfi kaman doki,dahaka yakoma shima Yusuf kuwa shigowanshi gyda yadan siyo kayan kwalamansa yashigo fannin yakolo don gayda aliya, ga mamakinsa tace " nayantata tunda kasan hakan aikasan cewa zata tafi duk lokacin dataga dama, toh itama tatafi," zaro ido yayi yasake kayan dagudu yafice mukullin mota yadauko yatuka wani wawan tuki dayakeyi saida ya tsorata mutane gydan aliya yanufa ya bude yaga bata ciki, yaleka kasan gado yaga ta tattare kayanta, wani tsaki yaja bakin ciki nacinsa hannunsa yabude da bango yana magana shikadai "aliya wlh inasonki, meyasa kikatafi? Ina kike? Aina zanganki?
To be continue insha Allah.
Thanks to Benaxir for sharing with us, for more follow the link
To download Inside Arewa application for easy access follow the link
No comments:
Post a Comment