...idan Buhari ya kama Jonathan sai sama ta fado, cewarsa
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Dakta Sule Lamido ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da cewa shi ma yaci kudin makamai.
Lamido ya bayyana haka ne a shafinsa na kafar sadarwar zamani, Facebook, inda yace tsohon mai baiwa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara kan harkokin tsaro, Kanau Sambo Dasuki ya baiwa Buhari motoci masu sulke guda biyu bayan da Boko Haram ta kai masa hari a Kaduna.
Haka kuma Sule Lamido ya kara da cewa me ya sa Buhari ya gagara kama Jonathan, bayan duk wadanda ake tuhuma suna na da nasaba da tsohon shugaban?
“Wai a ina Dasuki ya samu dala biliyan 2.5 da ya rarrabawa manyan mutane yayin da ake gab da zaben 2015, laifin da ya sa har yanzu yake daure a hannun hukumar DSS? A ina Nenadi ta samu makudan bilyoyi da ta rarrabawa jihohi wanda ya sa a yanzu haka take gaban Kotu?
“Ga amsa, dukkaninsu sun samu kudaden ne daga babban bankin Nijeriya dake karkashin shugaban bankin na yanzu, Godwin Emefeile, kuma tsohon shuhgaba Jonathan ne ya bada wannan umarni", cewar Lamido.
Daga karshe Sule Lamido wanda yake takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP yace: “Don haka tunda Alkali Binta Nyako ta yanke hukucin cewar bai kamata a kama duk wanda aka basu umarnin yin laifi ba, Gwmanatin Buhari ba zata iya kama Jonathan bane, ta gwada mu gani, da sai sama ta fado".
No comments:
Post a Comment