Thursday, 7 June 2018

Uwar Nakasassu da Marasa Galihu na Jihar Kaduna , Hajiya Hadiza El-Rufai ta Sha Ruwa da Mata Nakasassu.

Uwar Gidan Maigirma Gwamnan Jihar Kaduna, Hajiya Hadiza El-Rufai wanda ake yi wa lakabi da “Uwar Nakassu da Marasa Galihu” yau Alhamis 7 ga watan Yuni, 2018 ta kira mata nakasassu da marasa galihu na Jihar Kaduna a nan Gidan Gwamnati na Sa Kashim Ibrahim da ke Kaduna don shan ruwa tare da su.

Hajiya Hadiza El-Rufai takan kira wadannan masu bukata ta musamman ne shan ruwa don nuna musu irin yadda Gwamnatin Jihar Kaduna ta damu da su. Wannan dalilin ya sa duk shekara ita uwar gidan gwamnan kan kira su Shan ruwa, sannan har ta ba su atamfofi don su je su dinka su sami kayan sallah.

A jawabin Kwamishinan Mata da walwalar Jama’a, Hajiya Hafsat Baba ta bayyana wa wadannan mata nakasassu, Gwamnatin Jihar Kaduna na nan tana gyarawa da gina sababbin cibiyoyi na koyar da nakasassu sana’o’i a mazabu uku da ke fadin jihar don su da ‘ya’yansu su zama masu dogaro da kai.

Sannan ta bayyana yadda Gwamnatin Jihar Kaduna ta dauki daya daga cikin wadannan mata nakasassu aka ba ta mukami na P.A a ofishinta duk dai don nuna wannan gwamnati ta damu da su.

Su ma a nasu bangaren, wasu daga cikin nakasassun sun bayyana irin jin dadinsu yadda wannan gwamnati ta damu da su, wanda ba a taba nuna musu irin wannan kaunar ba a gwamnatocin baya.

No comments:

Post a Comment