Read The previous episode click here
Feel Free To Comments Here...
Nace Allah sutura wallahi banyi
laifiba nahau bada hakuri anan nurse din ta ban magani kasancewar weekend ne
ranar kuma ba malamai yasa bawani staff dayasani.muka koma hostel dakyar su furyad
suka matsamin naci abinci gashi ranar wai anyiwa ss2 laifi akataramu a field
din makarantan. Aka ware ss1 daban aka bamu purnishment dinmu. Wata sister Y Amina
muhammed muna shiri sosai da ita. Tace majidadi kekan aibaki da lafiya jeki
daki ki kwanta nan namike na je daki nakwanta kenan har bacci yafara kwasana
kawai naji saukan duka wani irin firgit nayi saidatamin sha biyu a jere, tadaga
bulalan ta kundumamin wani ashar meya kawoki hostel ban iyacewa komai ba sai
wani hawaye dayake fitamin nace sister aisha wallahi sister Y Amina ne tace
nadawo, tace dakeda Y aminan malapar ubanku!!auxubillah nace dakarfi.
Wani
irin kara tasaka tafara duka na baji bagani saida sandunan suka karye dorinan
ya mokade anan metron tashigo ta finciketa ta wurgata gefe. Aisha dama bakida
hanksli? Me yarinyan tamiki dazaki mata duka har haka? Keda principal gobe
Allah yakaimu tafice matron kuma tajani takaini kan gado, alokacin andawo daga
purnishment din bawanda bai tausayaminba mate dinmu sai zuwa suke suna gaysheni
nayi narau narau ko ina a kumbure, wani irin zazzabi yarufeni haka narinka
jinya har ran monday. Dayake English mukedashi first period Ahmed G nashigowa
yalura bananan a zatonsa ko lattin danasabayine anma dayaga yagama first period
baiganniba. Yace wasu zafyra ina Mayah? dama Mayah yake cemin sukayi narai
narai da ido sai yan ajin sukace batada lafiya. Meya sameta? Anan kowa yayi
tsit kowa na tsoron fada daga baya azo aci kaniyanshi. Ya buga musu tsawa
badaku nakeba? sai furyad tace sister head girl ne tamata duka. Wani irin
razana yayi what!!? metayi? sukayi tsit nanma. Yace furyad tatashi tadaukoni
takaini dispensary shikuma yaje gun, anan nurse din tabashi labari meya faru.
Yaharzuka sosai tunda take dashi bata taba ganin bacin ransaba, adaidai nan
muka shigo yana ganina yace ashhaaa. Nurse shine ba’a mata treatment ba! Zafyra
tace a a. Tamata wani dukan aka karayi.yace kuzauna anan amata duk abinda
yadace. Yakallen yayi murmushin dole wanda nasan a dole yayi sannu mayah.
Allah yakara sauki yafice bayan angama
wankemun ciwukan ina zaune kawai naga kaf ss2 wanda suka min duka dawanda suka
sabaki dawanda suka sa hannu sunyi layi a kofan dispensary, yaleko mayah fitonan.
Na fita ina kishingida gatanan kufara. Abun yadauremin kai daya bayan daya suka
taso sunaban hakuri, nayi shiru a zuciyata nace don Allah ahmed G karufamin
asiri kar nakoma hostel suci kaniya na. Ina wannan tunanin saiga aisha alkali
itama tazota taban hakuri, sannan tajuya wani fincika yamata ya gaggaura mata
mari. Dan ubanki haka mukayi dake? Alkawarin damukayi dake kenan? Zaki zaga
kici amana? dama haka kike? to a kunnen umma. Wani irin kuka tasaka haba big
bross kayi hakuri mana abun yadaure min kai matuka, dama akwai alaka tsakanin
aisha alka da ahmed G?
Yasa sukayi layi tundaga admin block
yakesasu tsallen kwado har dinning hall. Yana binsu da bulala, sunyi narai
narai kam balaifi duk malamin dayazo yamishi magana baya ko kallonsu donhaka
saisu juya batare da sunce komaiba. Bayan sungama tsallen kwadon. Yace yau
anhutar damasu aikin makaranta. Haka yasa suka share classes, hostel, da kuma
admin block. Yasa suka wanke bayan gidan teachers ranar har karfe biyar suka
kai suna aiki nikuwa yafita yakawo abinci yakawomana mukaci mukayi nak hankalina
a kwance.furyad kuwa duk tabi ta tsure wai kar a koma hostel sumana duka.
Makaranta kuwa kowa sai yadada tabbatar da zarginsa akan cewa muna soyayya da
ahmed g inbahaka ba wannan hukunci ai tsauri gareta. Bayan yagama sasu aikin
yakirani sannan yace gata agabanku barin rantse muku kuji, wallahi tallahi ko
dauko cokali kuka sata zaku wahala ahannuna. Inada sunayenku ba ita zata
fadamunba, securities nasaka donhaka saiku kiyaye. Sannan dukka masu post
acikinku daga yau kutabbata kunyi ban kwana dashi zansa principal gobe
yacireku. Ko bacemun kowaccensu cikin sanyin jiki suka mike, aisha alka ce
tazauna. yace tazo tataho tare da durkusawa, yaya kayi hakuri bazan karaba.
Na kalleshi shima kallon nawa
yake sannan yace mayah? Wannan kanwatace , cousin ditace na gyada kai sannan yace tatashi tatafi. Bayan
tafiyanta ne yake cemin babanta da babana uwarsu daya ubansu daya. A hatsarin
jirgi babanta da mamanta suka mutu, lokacin suna dawowa daga aikin hajj hakan
yasa take zaune a gidanmu har yui. Itada kanwata Itakuma tana FGGC Bansan
meyake damuntaba. Tana sona anma ni bana sonta, ni akwai wacce nakeso tun randa
nafara ganinita nakesonta anma ban gayamata bane. Sabidah ina ganin kaman tayi
karam!. Nayi kafaii ina kallonshi yau ahmed G ne yake cemin ‘he’s in love’.
Lallai nayarda duk jida kai na namiji a kasan takalmin mace zai aje. Haka
mukadanyi tadi sannan yace natafi masallaci a kishingide natafi, a masallaci ne
muka hadu dasu zafyra muna zaune muna dan tadi sai aka dauke wuta. Aka tada
gen. Shima yadauke muna jirane ayi isha’i. Sai gasu aisha alka da yan kwanansu
sunzo mu muna ganesu sukuma kasancewar a duhu yasa su basu ganmuba anma mu
mungansu.bayan sun idar sai dayan tacewa aisha alka, wai ni dama yasan
kinasonshine? wallahi yau anraina mana hankali ai wannan zaisa yarinyan ta
rainamu, aisha alka tace barshi. Wai adole ita yakeson aura. Wancan hutun
komawana naji yana magana cewa akwai wata dalibarsa yanaso anma bai gayamataba.
Dayan tace hehe. Aikuwa idan aka aureta kin kade. Aishan alkan tace kokuma ta
kadeba! Angayamata dangin miji wasane! ? Sukayi shewa sannan sukacigaba. Nikan
ganin antashi sallah ishai yasa muka mike. Muna idarwa muka wuce prep.
Awashegarin bansan yadda ahmed G. Yayi
da principal ba. Aka tarasu a assembly aka kwace green dankwali aka bawa wasu.
Principal din yayita korafi akan muguntan da prefect din sukayi. Wata sister Y
amina muhammed akabawa head girl. Mukam munji dadi koba komai munhuta tunda
muna mutunci da ita.
Feel Free To Comments Here...
No comments:
Post a Comment