Wednesday, 13 July 2016

Halaccin Sarauta episode 33

Continuation of Halaccin Sarauta episode 33

Read the previous episodes HERE

Jawowan dayayi yaga bangon envelope ne donhaka sai ya ajiye agefen pillow, yana zaune har yusuf yazo mikewa yayi yafice don tun randa yusuf yaje yacemar yagode baikara mishi magana ba. Har abdullahi zaifita yusuf yace "tsohonka na memanka" gabanshi ne yafadi dum donyasan ba maganan dazaamishi saina maganar bayar da kisney dayayi shiyanzu matarsa yake jin tausayi karya mutu su gaza kulawa da ita da dan cikinta, dakin yanufa yatatara abunda zai dauka yafice gyda yanufa yayi wankarsa matarsa duk ta tsorats don tasan baa sallameshiba yadawo, ta so tabashi abun karyawa baikulata ba yafice don ganin sarki mai ran karfe baisameshi ba don yana bacci dole yahakura yakoma Yusuf kuwa zama yayi dirshan agefenta ya tsura mata ido.

Tadawo gangar jikinsa tadawo wani gurbi arayuwansa itace tsoka da jininsa, tadawo tamkar bugun zuciyanta domin duk numfashin datayi sai yaji kaman daga jikinsa ne, bata farkaba sai takwas na safe likitan yaga warkewanta dawuri yakuma ce taci abinci sosai wanda ada ruwan lipton suke bata da abu mai ruwa hankalin kowa ya fara kwanciya banda na aliya damuwanta su sallameta awannan asibitin don tasamu tafita ta cimma burinta, sufyan ne yashigo alokacin yusuf yashiga gari anan ta mai bayani sannan tabada takardun daya karanta shima ya yarda da magananta nacewa saita gun alh.hamidu, donhaka yace zai danne damtse don yasamu kusanci da mahaifin hassana, alokacin kuma ta tambayeshi ko yasan dalilin dayasa abdullahi yabata wani bangare ajikinsa, bayaso yatada mata hankali donhaka yace "kinsan abokina ne, amintan dake tsakaninmu yabi," bata gamsu da bayaninshi dama yasan bazata yarda ba, zatamai wani tambayan ya tallafota tare da cewa ta kwanta tayi bacci, hakan yakara tabbatar mata akwai dalili yusuf ne zaigayamata, saidai tatuna guntun kishin shi donhaka ta share, tuni ta gargade zuciyanta da kartayi binciken dalili balle yadawo mata tashin hankali,

Dagari yama wayewa abdullahi yakoma gun sarki inda a tunaninsa fada zaimasa. Yamasa fadan kuwa sosai tareda cewa inhar kanaso ka gwada hallacinka kamata yayi kasiya, yanzu kai zaka iya mutuwa duk lokacin da jikinka ta gaji da wannan injin, nan dai abdullah yasha fada anma daidai da second daya baitaba nadamar abunda yayi ba, Satin aliya daya aka sallameta tuni takoma gida ankara gyra fanninta tasan aikin sufyan ne da antyn abuja wacce aranar tawuce abj, duk da tadawo gida mutane basu dauke kafa ba. Don gaydata alokacin sufyan yasami kusanci da nahaifin hassana tuni yashirya randa zaimasa tambayoyin hotunan yadiba sannan yaje gydan, hassana ta tarbeshi sannan tamasa iso bayan sun gaysa sai sufyan yayi bayanin meya kawosa tareda hotunan ya ajiye mai,alh.

Hamidu yayi murmushi sannan yace "dama nakai shekara sha biyu inajiran rana irin ta yau, ranan da yayan cikinsa zasuxo don jin bayani saidai nasan ku biyune, ina kanwarka? Kaje kadaukota itama tanada hakkin tasan meyasami mahaifinta" sufyan yace toh tareda ficewa gyda yaje ya kinkimo aliya a mota yamata bayani tuni jikinta yayi sanyi domun ta tsorata sosai, suka koma inda suka sameshi kamar yadda sufyan yabarshi yafara dacewa "iyayenku yan biyu ne masu son juna dakuma matukar kama, hakan yasa shakuwa a tsakaninsa, sarauta da son mulki shiya shiga ransubwanda shaidan yazo yashiga tsakani , bazan taba fada muku waya kashe iyayenku ba saidai ina rokonku dakuyi hakuri, ku yafewa kowaye ne, ku manta, don tsananta bincike baya jawo komi sai bacin rai," sufyan da aliya duk sun kagu suji bayani anma sai waazi yake akarshe yace "ranar karshe da mahaifinku da hussieni suka gana adaki kafin hussieni yabar gari, bawanda yake gun sai ni danake falo suna daki abunda naji kuwa shine hussieni yace ko duniya zata juya saiya mulka garrinnan, yayinda hassan ya musanta , hussieni kuwa yace su zuba sugani" donhaka kuhakura da binciken haka" sufyan da aliya sunyi sunyi anma mutum kam ya gunshe baki a bacin rai suka fito suka fice, hassana wacce tashirya don soyewa da masoyinta sai karar mota taji yafice, .gyda suka isa inda akarshe suka yanke shawarar dole mutum dayane yazama ansansu, hussienin mahaifinsu!

To be continue....

Godiya ga Benaxir Umar da ta rubuta.

No comments:

Post a Comment