Monday, 27 June 2016

Halaccin Sarauta episode 29 Saturday 27th June

Continuation of Halaccin Sarauta episode 29

Read the previous episodes click HERE

Yusuf kuwa tun yana jira yaji bazai iyaba, kuka yake wiwi sufyan yafara lallashinsa anma duk dahaka yusuf yagaza yana kuka yana cewa "aliya kitashi, namiki alkawari bazan kara shan wani abuba, aliya na nutsu nadaina duk abunda nakeyi, aliya wlh inasonki, dukkan kai nason dukkan ki, "jin abun yadawo sumbatu yasa sufyan yabashi gu, antyn abuja da inna dakuma yanuwa kakkani duk suna zaune ana jira likita yafito yace ansaka mata lafiya nima benaxir ina tsaye agefe inata adduan Allah yasa ayi aiki lafiya Bayan awanni kadan sai gashi likitan yafito sun bazama kanshi kaman zasu cinyeshi, anan yabukaci sufyan yazo nan da nan yusuf yabisu likitan zaiyi magana sufyan yace "badamuwa ana tare" binsa sukayi office suka zauna sannan yafara bayani "anyi aiki lafiya alhamdulilah jikinta kuma yakarba, yanzu bata tashiba don Allah duk wani abu na tashin hankali kar ayi agabanta, sannan inaga kar agayamata wa yabata kidney dinshi yanzu harsai ta warke," anan sufyan da yusuf suka mishi godiya sannan yamusu bayani akan akwai nurse dazatazo tamusu magana, suka fito ahaka sannan inna tamike tareda tambayan sufyan yace anyi lafiya, dakin abdullahi yanufa don suyi magana anan yace masa ai anyi aiki lafiya anma bata farka ba, yayi murmushi sannan yace "ina rokon alfarmarka" "Na mefa?" "Don Allah kasamu kayiwa yusuf magana da duk wanda yasan maganan nan wanda kasan zai iya fadawa aliya, don Allah kar afada mata nina bata kidney acemata siya akayi, " "Anma kasan dole tasani ko? Tunda yanzu bakamn da ba, dole kana yawan zuwa asibiti maganan gari baya buya" "Nidai kamin wannan alfarma abari sai bayan raina afada mata, don fada mata yanzu zaisa tafara diddigi banaso tagane cewa nine masoyinta dana guje mata,"

"Ba gudu mata kayiba, ita tagudu maka kadena fadan haka" "A a nidai don Allah kar afadawa kowa maganan nan tawuce, karta sani" Dahaka sufyan ya yarda bayan fitowarsa yakira yusuf yamasa bayani anma yaboye masa dalilin dayasa abdullahi yayi haka shidai yusuf yasan cewa abdullahi na son aliya ne inbahakaba bazai taba bada wani fanni na jikinshi yazabi mutuwa akan rayuwa ba, dahaka sufyan yabarshi harzai fita yaci karo wani likita wanda haushinsu yakeji alokacin akan meyasa zasu yadda abdullahi yabada jikinsa, ba gaira a dlili ya makuro likitan tareda tambayansa dalili, likitan yana neman hanyan kwacewa karya mutu don numfashinsa daukewa takeyi, dayaga zai wahala yace "gimbiya falmata ce tahana mu yarda kabayar" ahankali yasake wuyan tareda cewa "mekace?" "Gimbiya falmata ce ta aiko da wasika akan duk wanda yacire wani bangare na jikinka abakin aikinsa" Sakeshi yayi yabar corridor din mota yanufa yayi wani wawan burki yayi hanyan fada

To be continue....

Godiya ga Benazir data rubuta wannan labarin.

No comments:

Post a Comment