Continuation of Halaccin Sarauta episode 28
Read the previous episodes click HERE
Sufyan ne yarikeshi tareda cewa "wuce muje" bai iya tuka motan ba hakan yasa sufyan yafito dashi yakoma yafara tukawa, asibitin suka koma dasauri suka shiga, alokacin matan abdullahi kuka take sosai hankalinta yatashi nan da nan magana yazaga gari, har fada tunda yakolo take hankalinta baitaba mummunan tashi irin na wannan karon ba, a gigice tabar fadan ta umurceta da akawota asibitn, kuka take sosai.
Alokacin data iso asibitin yacika tam, mutane saisukaja gefe kawai suna kallon ikon Allah, yakolo ne ta bukaci tashiga dakin anan likitan yasa aka shigar da ita, don yace mata dan nata yanada jiki mai kyau tun awa biyu dasuka wuce idonsa biyu, hankalinsa akwance duk da zafin ciwo dake damunsa, cikin zafin murya da raunin zuciya tace "meyasa zakayi haka abdullahi? Baizama dole don zaka gwada mata kana sonta kasa rayuwarka a hatsari, haba abdullahi yanzufa kai rayuwa batada amfani agareka zaka iya mutuwa akoda yaushe aduk lokacin da jikinka tagaji da wannan injin, haba abdullahi!!"
Tunda yake baitaba jin mahaifiyarshi takira sunanshiba yasan cewa ta tabu matuka, donhaka yamika mata hannunsa tarikoshi gam kaman bazata sakeba "tun ina karami kin koyamin muhimmanci rikon alkawari da cika alkawari, a tarbiyan gidanmu na sarauta natashi naga mahaifina yana cika duk wani alkawari daya dauka , meyasa nima bazan kwatanta hakaba? Shin bakimin kwadayin aljanna? Shin bakimin kwadayin rahaman Allah? Don Allah ki kwantar da hankalinki, nasan ina son aliya anma cika alkawari shine musababbin bata sauran kidney dina, inban bataba duk nan babu mai bayarwa, sufyan nashi ba lafiya, yusuf kuma nazo wucewa naji gimbiya falmata ta aiko ace mishi karsu yarda subada na yusuf ko abakin aikinsu, kuma nasan cewa ko batayi magana ba bazaitaba yiwuwa yusuf yabada nashiba, tunda kinga yana shaye shaye bazai yiwu ace kidney dinshi lafiya lao ba, annemi nasayarwa baasamu daidai nataba, dole nacika alkawarin dana mata nacewa koda raina zanbayar don naceci rayuwarta, kitaimaka ki bano kwarin gwiwa don insamu inwarke, mutuwa kuwa inna mutu lokaci nane babu wanda yake mutuwa ba lokacinsa ba, " yakolo kuka take sosai tareda hamdala azuciyanta tana godewa Allah dayabata yaro mai ingantarcen tarbiya, mai kyan hali tunda take bata taba ganin abdullahi yayi alkawari yasaba ba, mutum ne mai daraja dan adam, taja numfashi sannan tace "nagode sosai daka fahimtar dani, Allah yarayamin kai yabaka tsawon rai yataimakeka,
Allah yadaga kafadunka" anan tamike tabar dakin kuka yacita sosai balle matarsa karshe gado aka bata anan likitan yasamu tanada ciki ga murna ga bakin ciki, yusuf kuwa yana makale a gefen dakin tiyatan dazaayiwa aliya, yaki motsawa azamansa agun falmata tasa akirashi yakai sau biyar daga karshe tashi yayi yawanke dogarin da mari saida aka fita dashi yace karsu dameshi, sufyan kuwa zuwa yayi yasiyo abubuwan dazaa bukata na abdullahi da matarsa, Mai martaba sarki yaji bakin ciki sosai musamman da falmata tace masa wa baiwa yabada kidney dinsa, shikadai a fada yarinka fada, daga baya ne da yakolo ta koma gida dakyar a kukan nata sai ganin mai martaba tayi akanta yana shigowa yafara fada akanme zatabarshi yafita haryaje yabada jikinsa ganin yadda yake fadan tasan cewa falmata ta shuka wani makircin anma yazatay? Dole tamai bayani hakan yasa tazaunar dashi tamai bayani dalla dalla tana kuka yaji tausayinta sosai yakuma ji son dansa yakaru, rungumarta yayi yana lallashi.
To be continue....
Godiya ga Benazir data rubuta wannan labarin.
No comments:
Post a Comment