Continuation of Halaccin Sarauta episode 30
Read the previous Halaccin Sarauta episode 29
Ayadda ya isa kofan gate din sukansu dogaran saida suka matsamishi sunga yadda yashigo da motan, abude yabar motan da mukullin ajiki yashige cikin gidan a birkice fannin falmata yanufa a harzuke dogarai dasuke kofan gun suna ganinshi suka matsa masa don ayadda yazo kaman guguwa ne ta tunkudoshi tana zaune a falo rike da waya a kunnenta yashigo fuskarshi a daure bata taba ganinshi haka ba, tuni tasha jinin jikinta ta tabbata angaya masa, ajiye wayan tayi tana kallonsa,cikin hushi da zafin murya yace "inaso kibani hujjanki nashiga rayuwata, kibani hujjanki na takurani," dakewa tayi duk da ta tsorata "bakayi girman da zaka yanke wani hukunci dakanka ba!, inbanda dolonci irin naka nadan fari tayaya zaka cire wani fannin jikinka a matsayinka na dan sarki, sannan kuma sarki anan gaba kace zaka bawa baiwa?!"
Murmushi yayi wanda tafi kuka ciwo yace "yanzu na fahimci inda kika dosa, toh inaso yau kisa aranki bakida da , sarki kuma kike can kinemi wanda zai cika miki burinki, baiwa???? Itace ta nutsar dani, takuma ladabtar dani abunda ke kika gagara yi!" Yana fadan haka yajuya yafice, ji tayi kaman ya watsa mata ruwan zafi, salati tayi tana rike kirjinta, yau dan cikinta shine ke mata gori,haryazo corridor yaga jakadiya yasan ita aka aika tafadi sakon, daya makuro wuyanta wani kara tasaka domin a tsammaninta zata leka lahira ne, dakyar dogarai suka karbeta suma yakoma kansu akarshe rikeshi akayi don abunsan yafara dawo karamin hauka, kuka yakwanta wiwi yanayi a daki tunda tahaifeshi baitaba tur da halayenta irin na ranan ba, yayi wadaran da halin mahaifiyarsa akan meyasa bazata koyi nagari ba don itama nata suzama nagari,
Matar abdullahi tafarka jikin nata da dan sauki gashi cikin mai laulayi ne, duk tadamu kishin mijinta yashiga ranta duk da yamata bayanin cewa arashin na mutane ne yabada nasa, toh ita tambayan anan shine yasan guda daya ne yasaura mishi akan meyasa zai bayar? Yana nufin zai mayar da ita karamar bazawara! Lallema duk tabi tadamu jira take yawarke don tasauke masa farillai da mustahabban rashin mutunci,aliya sai sha daya na dare tafarka da salatinta tafarka tuni sufyan ya kirkira su kowa yanufo gun dama abdullahi na asibitin, sai inna, yusuf kuwa yanacan shima bakanshi, bude idonta taga sufyan akanta duk tarame tayi kashin wuya, lebenta ya bushe idonta ya kumbura yayi jaa yariko hannunta yana murzawa idonsa fir akanta, dakyar tadan murmusa sannan tabude baki zatayi magana anma takasa, yace mata tayi shiru kartayi magana Allah yabata lfy. Inna ma sai faman tofa mata addua take taki motsawa daga baya kuma tamike ta dauro alwala tafara sallah tana addua Allah yadaga kafadun aliya, baccine yakara kwasan aliyan sannan yazauna agefe shima ya gyangyada sai asuba dayaji kiran sallah sai ya mike yafita dauro alwala yanufi masallacin asibitin, inna kuma a dakin tayi sallah, aliya sai karfe goma ta farka yusuf shima yashigo anma kana ganinshi kassan yana cikin damuwa,idonsa radau radau ya kumbura, yazauna agefenta itama kallonsa take yariko hannunta jikinsa yayi sanyi lao itakuma zafi kaman wuta, batayi magana ba har lokacin tagagara magana, yusuf kuwa shi dazaa cire zafin yakoma kansa dayafi kowa farin ciki, yazura mata ido alokacin likitan yazo dubata donhaka suka fita bashi wuri. Dawowansu dakin bayan likitan yagama yusuf yazauna agefe. Can dai aliya ta daure sannan tace "wayaban kidney dinshi?
To be continue....
Godiya ga Benaxir Umar da ta rubuta.
No comments:
Post a Comment