Saturday, 18 June 2016

Halaccin Sarauta episode 26 Saturday 18th June

Continuation of Halaccin Sarauta episode 26

Read the previous episodes follow the link HERE

Cikin wani yanayi na fargaba tace "yarima?" Dasauri tanufeshi shikuwa yanufi inda aliya take ya kunce igiyan da aka daureta dashi, ji yayi kaman ya rungumota ko zatasan halin da zuciyanta take ciki anma babu yadda ya iya, tuni kuwa abdullahi yashigo filin shima riketa yayi suka dagota wanda kowa saida yayi mamaki kenan aliya tasan dukkansu? Bilki ce tanufesu don riko aliya, sufyan ma gun yanufa nan da nan akasata a mota yanufi asibiti da ita, yayinda falmata ta yi umurni da a watse nan da nan yusuf yace baigama ba yanada magana, hankalin falmata yatashi tasan cewa asirinta zai tonu donhaka takara daure fuska anma yusuf bai saurareta ba, yakira likitan dasu abdullahi suka kawo mishi da likitan da falmata takawo, yacewa likitan falmatan yamasa bayanin meke damunsa cikin tsoro yace "zazzabi ne da rashin bacci,", yakalli likitan da sufyan suka kawo masa sannan yace masa "meka samu yake damuna?" "Allurai ne akayi ranka shidade da dan kwayoyi "

Yusuf yamike yahade rai tamkar sarkin dayake shirin yanke hukunci "kukama minshi harsai yafadi dawa yahada baki aka sashi abunda yayi," nan da nan dogarai suka kamashi, anan yahado da tsohon da aka kama wanda yake cewa tabbas shi mai kama mayune kuma aliya ma mayyace ita tacinye iyayenta, dukka yasa aka kamasu sannan yanufi fanninsa wanka yayi da zummar yabi aliya asibiti saidai fitowarsa yatarar da mahaifiyarsa tana jiransa, bai kalletaba balle yanuna yasan tana gun harta gaji donkanta sannan tace "in nina haifeka kasakesu" Wani kallo daya mata itakanta saidata tsure bai kulata ba don tunda yake itakanta bata taba ganin bacin ranshi irin na ranan ba, kaya yasa yafito don ji yayi yatsani munanan halayyan mahaifiyarsa don batada hali ko kadan tabari son mulki da son zuciya yarufe mata ido, bayason halin mahaifiyarsa ko kadan yasan shima da halinsu daya anma haduwarsa da aliya yacanja, yadawo cikakken mutum yadawo mai tausayi yakuma san darajan dan adam, yanzu yasan meya keyi kuma ya gode Allah daya hadasa da aliya akullum yana kara kaunanta sonta daban ne, dasauri yakunna motan sannan yafice daga fadan, asibiti yanufa wanda aka kwantar da aliya wacce ta gigice, sufyan duk tunaninsa karya rasata, haushin duk yancikin gydan yakeji don gani yake aliya zata iya rasa ranta, Allah kadai yasan kukan dayake a zuciyansa, tunaninsa Aliya ce kadai tarage masa yazaiyi insun rabashi da Aliya.

Donhaka duk tunaninsa ta tsaya cak yusuf ne yashigo a rude yana tambayan ina aliya, abdullahi ne yamasa bayanin cewa sunbata gado suna dubata,numfashi yaja yazauna yadafa kansa nauyi yaji kanshi yanayi, don shikanshi wankan dayayi ne ta taimaka masa yaji karfin jiki, sunfi awa azaune kafin likitan yafito nan da nan suka mike inda yace musu tasamu kidney problem don kaman anmata wawan bugi agun, kuma gaskiya dukka biyun sun lalace ana son acire kuma abata guda daya, bayan haka anason jini sannan kuma tabugu sosai akanta dole ajira aga farkwanta suyi adduan Allah sa tatashi lfy kar asamu wani matsala,sufyan dafa kai yayi ya tsuguna agun saiga hawaye suna zubowa, abdullahi da yusuf wanda shima ya rikice kallomsa suke, kishine yashiga ran yusuf akanme sufyan zai damu? Meye hadinshi da aliya? Atake yace likitan yacire nasa inyazo daya, anma sufyan nan da nan yamike tareda cewa muje aduba kidney din, da jinin , yusuf wani harara yasakar mishi domshikam ji yayi hankalinsa yatashi har bari hannunsa yake, likitan saiyaga kaman abumsun gasane, donhaka yace waye yafi kusa da ita? Yusuf yayi caraf yace "nine masoyinta" Sufyan bai kalleshiba sannan yacema likitan "muje ! Ni yayanta ne uwa daya uba daya!"

Ba yusuf ba hatta abdullahi dake kallon su sai daya tsorata wayan hanninsa yasake a kasa, tunaninsa ya tsaya cak, ya cukumo sufyan "kai dabban wani gari ne? Don kawai kana sonta zakace kai danuwanta ne?" Inna wacce tashigo asibitin a rude taga sufyan wanda yakirata yamata bayani tanufo kansu dasauri tanacewa "sufyan ina kanwarkan take? Yau munshiga uku innalilahi" yusuf sakeshi yayi don ya mugun tsorata, azatonsa yasan wacece aliya ashe yaudaran kansa yake baisan komi akantaba, jan jiki yayi gefe tareda zama akan kujera yayinda sufyan yanufi dakin likitan don samun karin bayani gameda kidney dazai bayar inda likitan yasanar dashi cewa dukka biyu sunsami matsala sun lalace donhaka dole acire asamata wani ko guda daya tasamu tayi surviving, tunda har kumbura tanayi wanda sai alokacin shi sufyan yalura dahakan shidai yasan yaga tacanja baiyi tunanin wani abuba tunda baidade da ganintaba anan yace shi yayanta ne uwa daya uba daya aka bashi duk wani fike dazai cika, yasa hannu sannan yace afara duba jinin , jininsu yazo daya atake aka diba , leda biyu yabayar yakwanta don yahuta bayan kwana uku zaa cire kidney dinshi daya abawa aliya, har kuka saidayayi akan gadon, yanason yar kanwarsa Bangaren yusif kuwa yarasa mezaiyi murna?haushi?takaici? Dole dai yayi dukka dole yayi farincikin cewa sufyan yayanta ne ba aure a tsakaninsu balle yadamu , nabiyi kuma dole yaji takaici da aliya taboye masa asalin cewa sufyan yayanta, tabbas hakane abdullahi yasanar mishi sufyan dan marigayi galadima ne anma baitaba kawowa aliya ba, lallai shi soko ne, meyasa aliya taboye mishi wannan bayan yasan babban sirrin ta balle wannan, shidai yanzu duk yarude damuwansa tafarka Inna kuwa duk ta tsure duk yanuwa na nesa saidata kira tasanar musu, antynsa ta abj ma tace zata biyo jirgi ta taho washegari, anan yusuf yasan cewa lallai aliya tanada gata, anma meyasa suka barta take bulayi agari?

Abdullahi kuwa ayanzu yatabbatar da inda yasan aliya. Tun randa yafara kallonta yasan cewa yasanta awani gu!, tabbas itace kanwar sufyan wacce suke wasa da ita ya kyalla yace yana sonta, wacce yanemeta yarasata, akacemasa tatafi abuja dazama, wacce itace first love dinshi, ba shakka itace shiyasa duk lokacin dayaganta cikin wani hali baya sharewa saiya taimaketa, tabbas itace innalilahi yazaiyi? Yanzu yafarajin sonta danye, ruwa tsundum yadawo, yazaiyi da yusuf? Yazaiyi yatabbatar mata dacewa itace?

To be continue....

Godiya ga Benazir data rubuta wannan labarin.

No comments:

Post a Comment