Sunday, 14 August 2016

Halaccin Sarauta Final Episode.

Hallaccin Sarauta Previous Episode

Zamu Fara sabon Littafi Wednesday Insha Allah.

Sunyi kokarinsu don ganin sunsamu laya kowani abu makamancin haka don samun babban kyauta kamar yadda aliya tamusu alkawari, basu sami komi ba haka suka hakura har dare ana abu daya, aliya duk tashiga damuwa da tashin hankali, anki abarta tahuta da mijinta ankuma ki abarta tazauna lafiya, Daredare takaranta surorin kamar yadda akace tayi takwanta zuciyanta cike da son kama kowacece, acan tafarajin kukan kulya da kare nan da nan tafara Allahumma ajirni fi musibati waakrijhi khailriha, tanayi tana hadawa da auxubillah, ahaka tazauna yusuf na gefenta yana tayata addua yagagara bacci duk da taso yayi anma yaki, hakan yasa suka zauna suna ta addua ahaka har asuba, asuba nayi yafice masallaci itama tayi sallolinta sannan tawuce kan gado , tana addua harta jira bacci ya kwasheta Tayi dan mafarkan Allah kuma yabata nasara ta jiwa kuran ciwo, itama ta ji ciwo bata tashiba sai karfe daya. Inda tayiwa yusuf bayani yace tacigaba dahaka har na sati kamar yadda malamin yace zata kashe kuran inhar tana kokarin fada dashi.

kullum tana fada dashi kuran yadawo baida ishashen karfi, aranan tafito tana son zuwa fannin yakolo ko zasu gaysa, wani bakin abu tagani rana ya hasko mata, harta wuce takoma tadauka ga mamakinta laya ne, hannunta na bari tadauka tana addua, harta isa dakinta tana isa tanemi babban container tazuba sannan tarufe, wayanta tadauka takira yusuf yana dauka muryanta na rawa tace "kayi sauri kazo gyda, don Allah kayi sauri" yadda yaji magananta tuni ya tsure dama yashiga kasuwa ne babu shiri yadawo fada, tana zaune a falo yashigo anan tanuna masa shima ya mugun tsorata anma dole yadanne nasa don karta rude, wurin malamin suka nufa dashi, yadauki layan sannan yace tayi addua ta tofa ajikinta ta kona layan agun, aikuwa tana haka yace toh yanzu saura takarasa nakasa kuran inhar tayi haka toh ba tabbas wacce tamata wannan sihirin, asiranta zai tonu dahaka sukayi sallama dashi. Sunkoma gida sukaga fannin falmata a cike arude yusuf yashige aliya na biye dashi abayanta, falmata ce adaki tana kwance sai kuyangu akanta, dakuma yakolo su umma uwar soro, mutane dayawa dai haka, hankalinshi tuni yafara tashi, yaleka ta dakyau ga mamakinsa ganinta yayi kaman ba itaba, kamanninta duk yacanja, tacanja wasu manyan kuraje ne suka fito mata, ga doyi kuma, kowa hannu na hanci tuni yakai nashi hannun , anan akace kowa ya watse aka barsu kadai adakin umma uwar soro tace takai awa daya ahaka, don tunda jakadiya tazo tamusu bayani akan falmata nakwance kawai saiga kurajen sunfara fitowa abun kuma bai tsayaba, shiru yayi zuciyarsa na masa zargi, anma duk dahaka yazauna, duk iya kokarin da akayi dawasu likitoti abu yaki tafiya wari yaki tsayawa, falmata acikin dakikai kadan tadawo abun tausayi, wanda hakan tuni yafara yawo a fada, falmata tayi sihiri yadawo kanta acewarsu kenan, kowa sai Allah kara yake, dama ta addabi kowa acikin fadan, kowa yanata farinciki, yayan cikinta ne kawai suke kukan abun, suma ni benaxir na tabbata don ita tahaifesu shiyasa, inbahaka ba babu yadda zaayi suji haushin abunda yake samunta, yusuf dai zama yayi agefenta yana kallonta yarasa ma yazaiyi sannan kuma mezaice mata.

Dahaka tana kallonshi tana zubda hawaye, aliya ma tana daga gefe tayi tagumi duk tsanar falmata datayi yaukuma tausayinta taji, tamike tadauko ruwa sannan tabata, tana jingine a kujera, tana kallon aliya yusuf ma nagefe, Wani abun mamaki shine tun ranan aliya tadena jin kukan kare da kulya, sannan tafara baccinta abun ya matukar bata mamaki hamdallah tarinkayi wa Allah tana godiya, tayi salollinta, Falmata ankaita asibiti anma sunbada shawaran ayi maganin gida nan da nan aka nemo mai maganin gargajiya, yusuf kuwa yahado da wannan malamin bayan dan magana dasukayi sai malamin yace mishi tabbas itace, yusuf jikinshi yayi sanyi donhaka dakyar yakira aliya malamin itama yamata bayani kuka tayi sosai jikinta yayi sanyi, tanata tunani duniyan shinawa yake? Da girmanka da mutuncinka zaka nemi gun boka , me boka zaimaka wanda Allah baimaka ba? Mezaka tanadar wa kanka agun boka? Daya wuci wulakanci da dizgi, duniyar kanta nawa take da mutum zai sa rayuwarshi ta kaskance, ta zama wulakantacce, Takoma gun falmata anma bata canja mata fuska ba, tacigaba da zama tana jinyarta da bayin dasukenan, Wannan hali na aliya yasaka falmata jin kunya, taji inama tunfarko bata kullaceta ba, bata mata asiriba, sannan bata musguna mata ba, tana kuka taroki gafaran aliya takuma nuna nadamarta a fili, aliya tanuna mata bakomi hakan yasa tacire komi aranta, mijinta kuwa tuni tasamu kanshi duk da dafarko yana fushi da halin mahaifiyarsa aliya tayi iya kokarinta ta gwada masa muhimmancin mahaifiyarsa dakuma hatsarin fushi da ita, tabbas yayi alfahari da aliya domin kuwa tazamto masa garkuwa, itace macen da annabi yace a aura wacce zata gyra maka yayinda kashiga hatsari wacce zata zamo maka garkuwa,yana alfahari da aliya yana kuma tausayinta a matsayin marainiya.

Falmata ahankali tafara samun sauki da yusuf yahado malamai anata addua da saukan qurani, domin sarkin yayi tashi harya gaji, Allah cikin ikonsa tasamu sauki duniya takoya mata hankali ta nutsu tazama mutumiyar arziki domin kuwa hatta bayi darajasu take, kansu yazama ahade da yakolo Yayinda aliya tahade da mijinta, abun alfahirinta,garkuwan jikinta sannan sanyin idaniyanta Sufyan yazo ya auri hassana wacce ta tare a gydan da sufyan ya kare mata,zaman lafiya alhmdlh nima benaxir omar ina jinjina muku dakukayi hakuri dani duk da matsalan dana rinka samu bansamu na karasa muku da wuriba dakuma rashin cigaba akan lokaci, nagode sosai Allah yabar zumunci Ina gayda rukayya bayero for helping out, yu really made me do dix, Kausar nd ummi aisha na sadaukar da littafinnan agareku don nuna godiyata agareku.

Godiya ga Benaxir Umar da ta rubuta.

No comments:

Post a Comment