Wednesday, 8 June 2016

Halaccin Sarauta episode 22

Continuation of Halaccin Sarauta episode 22

To read the previous episodes of
Halaccin Sarauta episode 21

Yana fita tarike kanta domin ciwo yake mata, itakanta tasan matsananinci so dakuma kishin datakeyiwa yusuf bana wasa bane,gashi yaje yadauko maganan yanmata yazatayi da rayuwarta inhar hakanne dagaske? Shikenan zaidaina sonta? Kawai tazauna tafashe da kuka, kuka takeyi nanma ta tuno da iyayenta tafara wani sabon babin kukan, inna ce tashigo ganin tana kuka tafara lallabinta dakyar tayi shiru. Itakanta tasan cewa aliya tayi rashin iyaye, saidai batason ta tada mata hankali ne anma ganin tadamu da ramako gakuma kukan datakeyi, don itadai tasan cewa dakyar rana yazo yafadi, aliya batayi kuka ba,a fuska akwai karfi anma zuciyanta mai rauni ne, saidata tabbatar cewa aliya tayi shiru sannan tace "inaso ki goge hawayenki ki saurareni, yau zanfadamiki tarihin iyayenki, tarihin rayuwarki, na boye da wanda ke kanki bakisaniba hatta yayanki baisaniba" jin haka yasa aliya ta gyaro zama tashare hawaye sannan tace "inajinki inna" "Mahaifinki hassan adamu shine galadima na 55 a garin yombi, kuma ya gada ne kaka da kakkani, sunyi auren soyayya da mahaifiyarki aisha, wacce tahaife ku rai biyu dake da sufyan, mahaifinki dan biyu ne haryau baki taba tunanin kitambaya ba?" Alokacin aliya ta tabbatar batayi wayo ba, tunaninta yayi nisa a yin ramako har bata hango kananun matsalan dake gabanta wanda matsalan da ake samu yanzu kenan, abu yasami mutum maimakon kazauna kabincika daya bayan daya zuciyanmu sai tayita ta mana raye raye muje har ga aikata zunubi,anan inna tacigaba "kekam ko ni kin gujewa kinki zama kinsanni, bayan ni ce gambon su mahaifinki su yan biyu ne hassan da hussieni, saini gambonsu, mu uku ne, hussienin mahaifinki yanzu haka yana raye anma baa garinnan ba, yana can senegal yana zaune da matarsa, kuma musabbabin tafiya shine mahaifinki dashi an bukaci abawa dayansu sarauta, sai shi hussien yagwada yanaso kuma mahaifinki bayaso, donhaka saiyake taimakawa don abashi bayan rasuwar galadima na 54 cikin ikon Allah sai mutanen fada sukaki yadda acewarsu hussieni na da aladun bature. Dawasu halaye wanda ni bansaniba anma sunfada anyi rikici sosai a kafin aka yanke bawa mahaifinki, randa akabawa mahaifinki aranan shi hussieni yabar garinnan bayan dogon magaanam dasukayi adaki dagashi sai hassan, haryau bawanda yasan mesuka fada, kuma tunranar hussieni ya tsani hassan dinsa, yakuma tsaneku, donhaka son yusuf shiga gydan sarauta inason gayamiki sai me shiryi, wacce kikeda kyakywan niyya, mace mai ilmi hazaka da karamci, don sarauta dakike gani yana raba uba da da, balle wa da kani Bayan tafiyan hussieni munyi jimami sosai, don mahaifinki har a asibiti ya kwanta don kewar danuwansa, munyi rashi sosai saidai ya gwadamana baya sonmu, yagwada mana abun duniya tafi masa mu, dakyar mahaifinki ya taso daga ciwo, sannan bayan haka yazo yanuna rashim amincewarsa na karban sarautan, nanma anyi daga kafin yakarba don inhar sarautar tabar hannunmu zata koma wani gida ne bazata dawoba, kaka da kakkani sarautar tamu ce, bayan mahaifinki yahau tundaga ranan yafara samun barazana, mafarkai kala kala, gashi ke kanki nasan zaki tuna lokacim da ummanki tayi barim yanbiyu sau uku, sufyan yazo yafara abu kaman tababbe bayason makaranta yafara bin almajirai babban dalilin dayasa hassan yadaukeshi yakai kasan waje kenan donhaka malamai suka bashi shawaram yadagashi a garin yombi, dalilin dayasa kenan kikaga anrabaki da danuwanki, kekuma ba abunda yasameki, wanda hakam yasa mutanen gari suka fara surutun cewa lallai lallai asiri akayi muku wanda bayaso babanki yasami magaji, ummanki tadamu sosai musamman da aka rabata dashi [10/10, 9:06 PM] Adda Bena: Ana haka shikanshi hassan yafara samun matsala da yan fada, kinsan ance baasamun mugun sarki sai mugun bafade, donhaka yalura duk munafukai ne agefen sarkim saiyazama shikadai mutum dayake kin yadda da maganganunsu, donhaka tuni tsana da keta, da hassada yakara shiga tsakani, donhaka rayuwarku gaba daya tadawo abin hatsari, hakam yasa ya kwasheki yakai makarantan kwana don kar wani mummunan abu yasameki, ran mutuwan mahaifinki kuwa ina asibiti mai gidana yana jinya, aka turomin labarin mutuwarsa, nayi jimami sosai nabukaci adauko ki daga makaranta akacemin a a abarki don kuna jarabawa, da sati daya surukata tarasu munje kaue taaziya kafin nadawo kika dawo kika tattara kika tafi abuja koda nadawo nayi bakin ciki anma dana gane gun wa kikaje saina bari kawai nasam zata rikeki amana, mukan yi waya da ita lokaci lokaci Tana gayamim awani hali kike ciki, saidai bantaba yarda tahadamu ba, aganina guduna kike zanbaki wuri, kinji takaiccecen tarihinki nasan bakisan da hakaba, iya abinda zan iya sanar dake ayanzu ne, saikuma ina gargadinki da duk wani magana dakikeyi nacewa zaki dau fansa, kidenashi na gargadeki daki daina, karkije ki janyo abunda zai dameki dakuma tashin hankali agareki, abinda yawuce yawuce, inkuma kinki yadda zaki girbe abunda kika shuka, domin bishiya kikeso ki tumbuke, dafatan kinjini?

Godiya ga Benazir data rubuta wannan labarin.

No comments:

Post a Comment