Continuation of Halaccin Sarauta episode 24
Read previous episodes here 23
Tuni ya tallafota bashiri tamike "meye haka zaka rikeni" saketa yayi awh dama idonta biyu dakyar takoma don taji kunyan abunda tayi. Cikin borin kunya tace "mekazomin anan, ilya yana nan baiyi nisa ba" "Ki kira ilyan ko kasheni yayi ba inda zanje yau saikin gayamin menamiki,aliya hussiena ba budurwa ta bace so ake ahadamu da ita naki babanta abokin babana ne alh.hamidu, tuni tazauna tareda zaro ido, don ta tuna cewa sufyan yace mata alh.hamidu shine wanda suke tare da mahaifinta ran ajalinsa, dasauri ta sake fuska donkar ya fuskan komi "to ni meruwana?"
"Nidai don Allah kiyi hkr. Kezan aura kenakeso ke zuciyata take bida "nan yagama sumbatunsa anma aliya ko cikanka batace ba, yana fita tajawo wayanta sufyan takira yana dauka yace "menenee? "Kazo gida nasamu labarin alh.hamidu" bata saurayi mezaice ba ta kashe wayan cikin minti talatin saigashi ya iso "Aina kika samu labarin? Keda kike nanike a daki?" "Meruwanka? Yusuf yazo yana ban hakuri akan yan biyun dasuka min hauka ranan, wai yaran aminin sarki ne alh.hamidu" "Allahu akbar, duk bincikena banje kansa ba, don naga baida sarauta anma tazo gidan sauki, yaran yanbiyu ne? "Ae! Bazaka gane wanne bace hassana ko hussiena" "Tazo daidai zanyi soyayya da daya, kozan sami kusanci da mahaifinsu ko yakikace?" "Kayi da hussiena" "Munafuka don kihadani fada da yaronnan ko?" "Oho dai kaikasani" "Kedai ki tabbata babu wanda yasan alakanmu don anasani shikenan ansan kema yar galadima ce plans dinki duk zasu rushe" Ficewa yayi yabarta bai nufi ko ina ba sai fada fanni abdullahi da matansa, yasamu tarba sosai anan yagwada sa cewa yaga yar alh.hamidu kuma yanaso, abdullahi yayi farinciki inda yace wacce aciki? Sufyan yagwada cewa hassana yakeson aura, aikuwa nan da nan yafara murna yara masu hankali kayi saan mace dawannan yace su shirya daredare zasuje gun mahaifinta, Daredare suka sha manyan kaya suka nufi gydan alh. Hamidu wanda yakarbesu hannu biyu biyu, abdullahi yayi bayanin kudirin sufyan a matsayinsa na dan marigayi galadima, nan da nan alh.hamidu yace "hassan adamu? " Abdullahi ya gyada kai tareda cewa "ae shi"
"Masha Allah ashe zankara ganinka? Mahaifina aminina ne sosai, Allah yajikan rai" Dukkansu suka amsa da "ameen" "Ban isa naci amanar abotana da mahaifinka ba, donhaka in hassana ce nabaka!" Sufyan yanuna farincikinsa yakuma yi godiya ayayinda akace suzo washegari don ganin yarinya Ranan sufyan yayi bacci mai dadi ganin cewa yadauko hanyar bayyanar gaskiyan mutuwan iyayensa, Washegari yashirya cikin janfa ya sha turare sai kamshi yake suka nufi gydan shida abdullahi ayayinda aka musu iso, yana zaune kanshi a kasa gabanshi na fadi wanda shikanshi yarasa dalili tayi sallama ahankali muryanta cikin sanyi sannan tashigo, alokacin yadago yakalleta, tanada haske saidai bata da tsayi, kananun ido gareta anma tanada karan hanci, kyaunta dan daidai masha Allah, dama shi bai fiyeson bakaken mata ba, musamman wanda yafisu haske, abdullahi ne yatabashi tuni yadawo daga duniyan tunaninsa yafara amsa gaysuwarta,
kanta a kasa a zuciyanshi yace "anma aliya munafuka ne, yanzu wannan salihan yarinyan zatace taje tamata fada?wannan ai daga gani ba ruwanta salihar macece, suka gaysa sannan abdullahi yafara neman sasantasu itakanta hassanan tana fara ganinshi taji ya kwanta mata arai, domin kuwa sufyan yahadu namiji ne awaye, mai kyau da kwarjini taji ta narke da sonsa awansu biyu suka fito tarako su har gate sannan yakarbi numban wayanta, suna fita daga gidan tashiga dagudu gun hussiena wacce take labe take kallonsu tsaf suka hau tsalle da murna , su hassana anyi mijin aure, Sufyan kuwa yaki daina murmushi shikam sonta yake, karfa yagagara cika aikinsa harya ajiyeshi a gydansa sannan yakara fitowa yataho gydan inna, yayi hakanne donkar abdullahi yasan gydan saboda bacin rana, aliya tana kwance yashigo "Adarennan yaya meza kacemin?" "Ke. Tashi! Sharri zakiyima hassana ko? Yarinyannan yar salaha da ita ba ruwanta, "Ko dai taje ta nutsu don kissa irin na mata nikam kabarni bacci zanyi" fannin inna yaje yaci yakoshi sannsn yafice" Washegari aliya taci wanka tsaf tashirya cikin atamfa dinkin yakarbeta sosai ba kadan ba, tana zaune, sallama akayi wasu dogarai ne sukace wa inna ana neman aliya a fada Hankalin inna yayi dubu yatashi tazo fannin aliya "mekika yi musu?" "Babu , suwaye?" "Daga fada ana nemanki" tayi tunani iya tunani tarasa meya hadata dagun, tafito a sanyaye suka tisata agaba sai fada
To be continue....
Godiya ga Benazir data rubuta wannan labarin.
No comments:
Post a Comment