Halaccin Sarauta Episode 34
Read the previous Episodes HERE
tuni suka fara tunanin hanyar dazasu je su sameshi ko shi yazo, Washegari sufyan yaje gun alh.hamid tareda rokonsa ko akwai hanyar dazaayi asamu hussieni yazo, yace mishi hanya daya ne kadai zaisa hussieni yazo, in ance mishi anga ajiyan mahaifinsa, ajiya ne wanda kakanku yayi wa hussieni haryau baasamu ba, donhaka dole kusamo wannan hajiyan don hussieni yazo, sufyan ya amsa da toh anma shi tuni ya shuka dabararsa, wasikar jaki yayi yasa aka tura inda yake fadawa hussienin shine dan hassan kuma ga ajiyarsa a hannunsa, yayi hakkanne don baida kudin dazaice zaije bayan haka baisan yadda kanin mahaifin nasa zai karbe sa ba, gwara yajawo shi yazoshi duk da taimakon alh.hamdiu yanemi address din yatura Aliya ta warke garau haka ma abdullahi rayuwa tacigaba da gudana musu, duk da aliya ta dan ja baya da yusuf anma tana sonsa , daidai da kankanin lokaci sonsa baitaba raguwa mata ba, abdullahi kuwa yanzu da taimakon injin bature yake rayuwa, yariga daya cire rai wa duniya don yasan wahalarshi tazo karshe.
Acikin wata biyu wata rana sai labari ta iso sufyan cewa ga hussieni yazo gari, ya tare ne agydan alh.hamidu hakan yasa aliya da sufyan suka shirya tareda inna don zuwa gayda shi, kasancewar sunsaba da gydan shigansu sunyi mamaki don kammanin mahaifinsu ne sak a fuskan hussieni sai yanmata guda biyu wanda duk daga kallonsu ansan yan biyune, zasuyi saan aliya, kyawawa dasu suma kammanin mahaifin suka dauko, hussieni ya tarbesu sosai a matsayin yayansa, aliya taji dadi ganin cewa itama gata da yanuwa tuni suka saba da yanbiyun, sunsha tadi sosai sai can dare sannan su aliya suka dawo gyda Washegari sufyan ne ya koma anma wannan karon duk acikin gyda suke, alh.hamidu da hussieni suna falo donhaka sufyan yashirya don yaje yatambayeshi yarike hannun kofan zaishiga yakasa kunne donjin mesuke fada, Alh.hamidu yace
"kasan cewa yarannan sundameni maganan mahaifinsu sai tsananta bincike suke, ni bansan mezance musuba, kasan dai bazan bude baki nace musu hussienin mahaifinsu shiyasa akashe mahaifinsu don samun sarauta" "Nagode daka rufe maganan baka furta ba, ni bansan tayaya zanyiba, nayi nadaman abunda na aikata gashi idan ina kallon yaransa duk sai naji na tsargu mussaman macen, itace na cuta da maraici, hakika son zuciya da zugin shaidan su suka sani na aikata abunda nayi,yanzu kunsamamin ajiyan ne? Don da wannan ajiyan zan iya karban sarautar sarki bana galadima kawai ba, nadawo gida bazan koma ba,"
Sufyan dake rike da hannun kofan yasake jiki a sanyaye yafice batareda kowa yasaniba, gyda gun aliya yanufa yashiga tana bacci don tace mai haka kawai takejin faduwar gaba da ciwon kai yace tayi bacci inta tashi tasameshi agydan alh.hamidu, zura mata ido yayi hannunsa na bari yana shafa gefen fuskanta, farkawa tayi tazauna tareda cewa "yayah" bai amsataba yafara kokarin share hawayensa, tunda take bata taba ganinshi awannan yanayun ba, tuni jikinta itama yahau bari "yayah! Meya faru? Waye ba lafiya?" Hannunsa na bari yariko nata yarungumota kuka yake sosai mai tsananta zuciya, tuni tafara itama duk da batasan dalili ba, cikin yanayin tausayi yace "aliya hakika agarin bincikenmu yau mun bincikawa kanmu tashin hankali, aliya alh.hussieni shiya sa aka kashe mahaifinmu" tsak ta tsaya tana kokarin daidaita numfashinta anan wayan sufyan tayi kara cikin yanayin tausayi yadauki wayan, "hello, naam" Salati taji yafarayi yamike cak "abdullahi? Innalilahi!! Innalilahi wainnailaihirajiun!! Gamunan zuwa! Innalilahi!" Fitsari tasake awando wani kuka yaci fuskanta, gabanta ya tsananta fadi, "yayah meya sameshi?" Baikulata ba yace "shirya mutafi" dankwali kawai tadauka tabishi, nima benaxir gabana yana fadi nabishi don ganin meya faru!
To be continue....
Godiya ga Benaxir Umar da ta rubuta.
No comments:
Post a Comment