Halaccin Sqrauta Episode 36
Read Previous Episode HERE
jakadiya tana rusune harta mike ta fice. Bawanda yakai falmata farin ciki aranan saboda tana ganin wanda zai tare mata sarautar danta yafadi kasa yamutu, shehu kuwa baiyi hankalin dazata sashi a sahun masu karban sarautan ba. Donhaka tuni tafara tunanin hanyan dashi kanshi sarkin zai mutu, babu tsoron Allah babu tunanin lahira, tunaninta shine takashe duk wanda tasan zaishiga tsakaninta da mulkin garin, Sai dare sannan aliya tafarka atake sufyan ya tallabota yadawo da ita gida yana ganin inna baikulataba yashige da aliya ciki, saida yatabbatar takwanta ya rufo kofan sannan yafito inna tana tsaye tana jira yafito, baikulata ba tana kiransa, inba don babu gun da zaikai aliya ba da gidan nata saisu tattara subar mata shi, Cikin dare aliya tayita firgit tana wasu mafarkai, dolenta tamike,alwala tadauro tafara sallah har asuba tana yiwa abdullahi addua, tausayin matanshi da abunda zasu haifa yacikata, Dasafe sufyan nazaune wayansa tayi kara alh.hamidu ne yake cemasa yazo suna jiransa, baiyi bacciba tsabar yana tunanin hanyan dazsi bullowa maganan, motansa yaja yafice gydan alh.hamidu yanufa suna zaune a tsakar gydan suna jiranshi, sun gaysa yabasu girmansu sannan yazauna, inda hussieni yake tambayansa alkawarinsa, sufyan yayi murmushi sannan yace "komi zaizama naka idan kabani tarihin yadda akayi ka kashe mahaifina!" Ba hussieni ba har alh.hamidu saida yabude baki don mamaki,hussieni yagagara cewa komi,hakan yakara tunzura sufyan, hawaye ne suka fara zubo mishi yafara magana cikin sanyin jiki "Ashe karshen duniya zatazo dahar danuwa zaisa hannu yakashe danuwansa saboda dukiya?saboda mulki?" Bawanda ya amsa mishi kaman tsoffin barayi da aka kamasu hussieni kanshi akasa yafara magana "kai mahaifinka ne.
Nikuma danuwana , wlh tlh ba abunda nashirya yafaru ba kenan, Allah dai yayi zanzama sanadi, tabbas munyi musu da shi batun mulki anma ban kwallafa raina ba. Nasan na umurta da amai dukka anma bance sukasheshi ba, bankuma ce suhada da mahaifiyarka ba. Allah yayine lokaci yayi don Allah kayi hakuri, karkuma kabari kanwarka taji alokacin sufyan yayi kukan zuci daya tuna da iyayensa anma tuni ya watsake saboda ayanzu zucuyarsa tabushe yana tunanun daukar fansa, recordern dayake recordn yasawa stop sannan yamike yafice batare da ya ce musu komi ba dama yakira lawyernsa awaya tuni yadamka masa shaidansa tareda basa go ahead nashigar da kara kotu, koba komi yanzu yaji sanyi aransa
Aliya kuwa tacanja gabadaya ba abinci sai ruwan lipton, sufyan yayi lallamin harya gaji yusuf ma yayi nass Bayan sati biyu alokacin anwatse a gun rasuwa. Sannan alh.hamidu da alh.hussieni sun shiga kotu inda zaa fara sauraren karansu Aliya tadan sake, yanzu hankalinta ya kwanta maganan rama mutuwan iyayenta anmma abunda yafi bata ciwo shine danuwan mahaifinta shi yakashe mahaifinta. Abunda ciwo,saidai yanzu tabar komi agun Allah har lokacin sufyan baya magana da inna , aliya tayi iya kokarinta anma yafaskara yusuf na iya kokarinsa ganin ya farantawa aliya yayinda soyayya mai karfi tashiga tsakaninsu, tuni yafara maganan aurenta yasamu falmata da zance atake tace batasan zance ba, nan yakoma kan yakolo ta yadda takuma sa albarka inda anan yasako waziri da sarki, dafarko waziri yaki amincewa acewarsa dole yusuf yadauko yarinya mai asali, nan fa yusuf yazayyana masa rayuwar aliya tundaga farko dakuma wahalhalun datasha waziri yayi mamaki sarai anma yace zai gwada tunkarar sarki, sarki yanajin magana yatambayi wacece atake waxiri yace yar marigayi galadima,sarki yaji dadi sosai tuni yafara murna, wannan yarinyan ai ita keda asali, nan waziri yace "anma akwai matsala mai martaba, yarinyan tashin hannun mace tayi dakuma tashin gari" Sarkin yayi shiru don tantance me wazirin ke nufi donhaka yace "yi bincike mai tsanani muji"dahaka waziri yabar maganan, falmata taji labarin abunda ke faruwa donhaka ta nufi sarki da maganan anma yanuna mata shi ba ruwansa,don
shikanshi yanaso yusuf yayi aure, baitaba tsammani kuma yusuf zaikawo yarinya yace yanaso ba donhaka tuni tarikice duk tana tunanin hanyoyin dazata hanashi wanda shi yusuf har daina zuwa gaysheta yayi tsabar yasan kalan mitanta, Aliya kuwa tasan bakaramin rikici bane zai afku donhaka tuni tafara lura da takunta, ga masu nufinta da sharri, ita anata taso ta tattara tabar garin bata da dsmuwa da gun anma dole tajira a idar da case din iyayenta a kotu, Waziri yayi iya bincikenansa akan aliya tuni yakira yusuf "Kana sane da tayi bauta agydannan?" "Tayine alokacin batasan kowa ba" "Kasan dai yanayin rayuwarta bai shiga danaka ba" "Nasani shiyasa nake rokonka daka sa baki, kaikadai ne inka yabeta sarki zsi yadda, don Allah kataimaka" "Zan yi iya kokarina, anma kai kasan halin mahaifiyarka" Dawannan suka rabu inda yaje yagabatar da zancen da duk wani tarihin aliya agaban sarki, sarki yadannan approve makake, nima dai benaxir na dannan approve duk da munsan amincewan mezai jawo, ansa rayuwar aliya cikin hatsari da damuwa, anma munsan cewa aliya ce kadai zata iya gyrawa falmata duwawun zama, muje zuwa gobe insha Allah saina dora.
To be continue....
Godiya ga Benaxir Umar da ta rubuta.
No comments:
Post a Comment