To read the previous episodes episode follow the link
sufyan yamike yana karkade kayan jikinsa tareda kallon yusuf, yusuf baiji kunyan wani abuba yakara nufa kanshi ya damko shi dakarfi abdullahi wanda ke filin yanufi kansu don rabasu, anma yayi latti domin sufyan yasha naushi, yusuf tsakaninsa da Allah ya mammaujeshi alokacin dakyar abdullahi yasamu ya kufce sufyan sannan yashiga tsakaninsu, wasu ne sukaja yusuf don yadena abun kunyan dayakeyi wanda magana tuni ta yadu, yarima yana fada ,sufyan mota aka nufa dashi don yawuce masaukinsa gogan naku kuwa fada aka wuce dashi alokacin zuciyarshi tafasa take duk ya rikici a gigice aka kaishi fanninshi falmata ce tanufo kanshi don labari ya isota cewa fada yake akan liya, cikin fushi wanda bai taba ganinta aciki ba ta umurci kowa ya watse yabarta da danta "yusuf mekakeso namaka? Kai ba karamin yaro ba yusuf, wani irin rayuwa ne haka yusuf? So kake ka kasheni?daga yau acemin kasha giya, jibi mata, yau kuma akan baiwa kake fada?
"Kidena cemata baiwa saboda a yanta ta, rabon dakiji anganni da wata tun yaushe? Tun ran da nahadu da aliya!, giya fa? Tun yaushe???" "Da Allah min shiru da bakinka da rimi rimi abun arziki kadena sha, meyasa kadawo sha?" "Saboda narasa wacce tahanani sha" "Kana nufin kacemin ba don Allah kabari ba sai don ita?" "Dazan bari dana bari tuntuni, anma don ita nabari Allah nagani donhaka karkiga laifina. Kinaso in nutsu kema ya kamata kidena musgunawa yaran wasu, kidena neman batanci da yaran wasu" Hannu tasa ta gaura masa mari, wanda saidayaga walkiya a fuskansa."ina magana kana magana?; yaushe nahaifeka? Kai wato mace dadi ko, kaje ta tusaka kasan pant dinta," "Nifa ko tabata bantabayiba" "Yimin shiru munafiki, duk duniya bawanda karaina kaman ni, nagaji zangayawa sarkin saimugani ko shi zaka ji maganansa!"
Bata saurari mezai ce ba tafice, fanninta tanufa, gaskiya yakamata tadauki babban mataki akan aliya, jakadiya takira tareda cewa " kinemomin duk inda aliya tashiga ki kawomin ita nan" Aliya kuwa tana zaune akan gado tana game din candy crush bacci yaki daukanta, sufyan ne yakirata awaya tadauka "Kekuma kina tareda mahaukaci ne bansaniba?" "Waye mahaukacim?" "Mahaukacin saurayinki mana, zaimin hauka a bainar jamaa, total yarinta?" Tana kwance ne saidata mike, ita duk tunaninta hala yusuf yasha wani abune yaje da zafin kishinsa yayi wani yarintar, "Yaya meyasameshi? Yana ina? "Anma zanmiki rashin mutunci, bazaki tambayi jikina ba saina wani kato? Nidana sha duka?mtsw" "Kayi hakuri bazai karaba, anma don Allah yana ina?" "Gidan ubansa" "Shikenan don Allah kana hakuri dashi" Bai saurareta ba yakashe wayansa don yaga itama giyan soyayyan ke dibanta.
Ta kashe wayan takira wayan yusuf wanda ke kashe ahaka taketa tryn har bacci ya kwasheta, bata juyaba sai asuba, Har rana tana tryn numbansa baya shiga ta tattara sallayanta tanufi tsohon gidanta a kofar gydan taja kujera tana zaune tayi hakane dan yusuf ko zadu hadu, wasu yanmata ne guda biyu kana ganinsu kaga yan biyu don inka cire kayan jikinsu dasuka saka daban daban kominsu na siffar jikinsu iri daya ne, suka nufo kanta daya sanye da abaya daya kuma sanye da atamfa Mai abayar takarewa aliya kallo bisani tayi tsaki sannan tace "yanzu wannan jaka dabbar ce daman? Baka mummuna kaman kasam takashi na!? Shikuwa yarima meyagani anan? Mai atamfan itama takare mata kallo sannan tace "bar munafiki nema yake yajamin raini da kaskanci, ta ina zaahadani dawannan gidahumar? Banza talaka!" Aliya zuciyanta na tafasa musamman datagano maganansu cewa mai atamfar ce budurwar yusuf. Bata kulasu ba tadanne zuciyanta tanufi sgiga gidan, coke din hannunta tasaka ta watsawa aliya a jiki, wani juyowa da aliya tayi ta damko makokoronta "KE WALLAHI TALLAHI NI KARAMAR MAHAUKACIYA CE!!! ZAN ZUBAMIKI RASHIN MUTUNCI!!!
To be continue insha Allah all thanks to Benaxir for more follow the link
No comments:
Post a Comment