Tuesday, 5 July 2016

Halaccin Sarauta episode 32

Continuation of Halaccin Sarauta episode 32

To read the previous episodes click HERE

Fita sukayi adakin suka barta da bugun zuciya har cikin ranta ta tsorata kwanyanta yafara caji, tasan haka kawai mutum bazai cire koda yabayar ba, wani zuciyan tace yanzu haka tsabar zumuncin dake tsakaninku ne, harta bar maganan ahaka saikuma ta tsorata data kara tunawa sunce guda dayan data rage masa yabayar, inna ce tariketa ta kwantar da ita anma aliya ta gagara kwanciya duk ta tsure hankalinta yatashi tuni tamike a tsaye tana cewa "inna nikam ko dai zanfita ne? Ina yaya?" Duk a gigice take hakan yasa inna tarikota tareda cewa "kwanta, barin kira miki yayankin" fita tayi don tanemo sufyan bata ganshi ba donhaka saitayi magana da nurse daya don su samu sudubata a lokacin shigowansu jikin ya rikice aliya duk ta tsorata sosai nurse dinne ta rikota itakuwa duk ta gigice dakyar aka kwantar da ita wani irin kuka take mai shiga zuciya tana kama jikin inna,

"inna kitaimaka kinemomin yayana" batasan meye matsalarta na, anma ta tsorata bashiri tafita duk da batada tabbacin ko zataga sufyan din filin asibitin tanufa tazaga bataganshiba donhaka takoma ta dakin abdullahi tanufa ganinshi azaune a rikice tace "yarima ina sufyan? Kataimaka ka nemoshi munshiga uku aliya" agigice yamike yacire kalulan hannunsa sannan yace "muje" dagudu gudu suka nufi dakin alokacin aliya ta bankade nurse din tana cewa akaita gun sufyan, abdullahi ne yakomota yariko hannunta sannan yace "aliya kikalleni" kallonsa tayi agigice tarude anma yadda ya zura mata ido tuni taji wani nutsuwa yashigo mata, ya kwanto mata, hannunta na bari tace "yariiiiiim" "Shhhhh karkiyi magana kiyi shiru" Shirun tayi kaman yadda yace addua yatofa mata sannan yace wa inna insha Allah bazata kara firgita ba, zama yayi dirsham agefenta acewarsa sai sufyan yazo zaitafi, wata nurse ce tashigo tareda rokonsa yakoma daure fuska yayi kaman yaga malaikar mutuwa yana cewa ba inda zanje kuma karta nima takurashi, hakan yasata fita don tasanar da manyanta, inna tayi tayi dashi yamike yafice anma yaki yarda, tuni tafara nadamar kiransa anma abdullahi yakafe, aliya kuwa tana jingine a kwance tana ta tunani, tarasa tayaya zata tambayeshi inkuma yabata da zuciya daya ne fa? Yazatayi? Wani irin nauyinsa takeji yanzu fa duk gadaranta akwai kidney dinshi ajikinta, ita damuwanta sufyan yazo ta tambayeshi gaskiyan alamarin, Sunfi minti talatin ahaka kafin yashigo, shigowarsa yasamu aliya tayi bacci abdullahi na gefenta, tuni yanufo kansa, "kaida bakada lafiya kazo gadin wata marar lafiyan?"

"Kai nake jira kadawo, firgita takeyi shiyasa nayi hakan" sufyan ne yajashi suka nufi dakin da aka kwantar dashi, sannan yadawo dakin da aka kwantar da aliya sannan yazauna cikin mintuna kadan saiga bilkisu dama sufyan yaroka abarta tafito don sunfi sabawa da aliyan yakolo ta amince, shigowan bilkisu dole tajira aliya ta tashi bayan farkwanta alokacin sufyan yanufi gun abdullahi , aliya naganin bilki ta wangale baki sanin cewa zuwanta bana banza bane bayan bilki tamata jajen yajikin sannan tamika mata wani takarda tare da cewa duk abunda kikeson sani yana cikin nan, Allah yabaki saa, bashiri tafice don tsoro takeji Aliya ta paki idon inna tasaka tacikin bargo taboye sannan takoma ta kwanta, can dai tamike tasaka akasan katifan tamayar ta kwanta.

Bayan sun watse daredare anbarta da inna wacce tabude baki sai bacci take, taciro takardun tabude hotuna ne tsoffi dakuma wani enlarger karami, mahaifinta ne da alh.hamidu mahaifinsu yan biyu saikuma sauran biyun su uku, da mahaifinta dawani wanda take kyautata zaton cewa shine dan biyun mahaifinta hussieni sai alh.hamidu gabanta ne ya tsananta fadi, ta mugun tsorata asaninta tace bilki ta bincika mata alakan alh.hamidu da fadan gidan kusancinsu ta bakin tsoffin bayin dasuka san kan gydan, karshe kuma ga abunda bilki takawo mata, tasan bilki batayi makaranta ko ilmin dazatayi wannan binciken ba, dole akwai wanda yasan sirrinta, waye toh? Sufyan? Inhar shine toh bazai bawa bilki ba dakanshi zaiboye. Abdullahi? Tasan abdullahi bazai taba kawo aikinta ba, don baigama sanin alakarta da sufyan ba balle abunda yakawota(a tunaninta abdullhi baisan cewa ita kanwar sufyan bane), yusuf? Salati tayi tabbas yusuf ne shine kadai namijin da yasan sirrinta , amma meyasa yataimaketa? Nanma dai tagodewa Allah damuwanta burinta yakusan cika, yanzu dole tasami hanya da alh.hamidu don taji daga bakinshi meya sani, tunda duk shine mafi kusa acikinsu Batayi bacci ba har asuba nurses sunzo sun dubata suka fice ana idar da asuba bacci ya kwasheta, abdullahi ne yashigo dakin don ganinta inna tana wuridi yadan zauna agefe, idonsa ce tahango mai takarda, jaa yayi don yaga menene (Salam, akwai batu jiya dayayi ta zagawa akan na rasu, ba ni bace wata benazir muhd ce yar nasarrawa, nagode ga dumbin masoyana dasuka kira donjin lafiyata, duk wanda aka tayar ma hankali ko yashiga wani damuwa ina rokon afuwa don Allah nidai ina raye, Allah yabamu tsawon kwana,)

To be continue....

Godiya ga Benaxir Umar da ta rubuta.

No comments:

Post a Comment