Wednesday, 1 June 2016

Halaccin Sarauta episode 16


Bata amsa ta ba saidai cewa datayi "ina kasuwa zankiraki idan nakoma gida saimuyi magana kedai kiduba dakyau zai iyayin wani abu daban, nibansan gurinki yazo ba sai yanzu dayake kirana" kashe wayan tayi aliya ta tsaya kallon wayan, bataci ta zamaba gwara tamike dakyau tanemi mafita duk da tasan cewa yusuf baxai taba fadawa kowaba, dole tafita neman danuwanta!, dole tabi diddigin kisan kafin sarki yarigata yasa akamoshi. Murna zatayu ko bakin ciki? Anma dai koba komi its a relief tanada danuwa ba ita kadai aka bari ba, tuni tafara tunanun yadda zataga bilkisu din abakin bilki ne kadai zata sami lbr, kayanta tacanja tadauko wani katon roba tafita shago takarbi pure water tajuye aciki ta tusa wayanta acikin zanin sannan tanufi hanyar fada,

ahanya mutane su tsareta don siyan pure water abun yafara batamata rai ita tasaka ne don bukatunta daban akan meyasa zaana tareta don asiya? Dahaka dai tanufi fadan inda ta fara survey din gurin duk rashin hankalinta da kuma basiranta babu hanyan bi, katangan ma dogo ne irin dogon da babu dan adam dazai gwada shiga haka, agun aka siya pure watern dukka don yanada sanyi sosai roban da kudin tamikawa wani almajiri tadawo gyda, kwanciya tayi akan gado itakam zatayi hauka gashi ankusan shan ruwa haryanzu batasami hanyan shiga fadaba. Tasan dole tabi hanyan daya kamata tabi wato yusuf,bayan asha ruwa saigashi yazo ganinta yayi akan sallaya yaga batamasan yazoba hakan yatabbatar masa dacewa tunani take, shi gani yake kaman ita takashe waxiri anma yadda tayi dazu tasashi kokonto,

kuma dayaje fada yasami lbrn duk abunda aka kawo aci daga kicin bilki tana fanninsa a lokacin toh kodai aliya tanada wani ne bayan bilki? Kokuma gaskiya ne ba ita takashe shiba? Hakadai yazauna agabanta ganin tadamu batasan yazo gunba yabuga kanta kadan tuni takaleshi yayi murmushi tareda cewa "waya taba minke yanzu na ajiye tarbiya ta da rawani na Nazuba mai farillai da mustahabban rashin mutunci" kallonsa tayi tareda cewa "kaifa asalim dan tasha ne ko baa taba gayamaka ba?" Yayi dariya tareda cewa "gashi kinfadamin? Bazaki kira bilki kiji daga gareta ba?" Jin yafadi haka ta tabbatar gwadata yake donhaka Allah ma yataimaketa bata fara fadaba, donhaka tace "a a bani da abun fada mata"* tuni yaji sanyi aransa don yatabbatar da ita tasata zata bukaci taji wani abu tadin mutuwan suka farayi inda tabugi cikinsa taji abunda takesonji , tabbas wanda yasa maganin daga kicin yafito tadaisan yayanta bazai je as bawa ba don bawanda zaiyi tunanin haka , toh yazama kenan yana da mai taimaka masa bata idar da tunaninta ba yacigaba dacewa "yanzu inaga bikin abdullahi zaa daga saboda rasuwannan, " "Wacece budurwarsan nan?" "Yar galadiman yanzu" "Ni naganshi ma dazu dawani da na tambaya akacemin dan galadima marigayi ne" "Toh bantambaya ba wani galadiman ba, tunda san ke kadaice agun wanda yarau da ko?"

Gabanta yayi mummunan fadi anma tadaure takirkiro murmushi zuciyanta na bugawa dakarfi tace "ae! Nikadai suka haifa saidai dayan galadiman, wat a bad luck duk sauran masu sarautan basu mutuwa sai galadima!" Ya jinjina kadan sannan yace "yanzu gashi wazirin yarasu shima ai Allah dai ya dakatar ahaka" "Ameen" "Sarki yasa ayi bincike sosai you have to be careful sosai, don nasan wannan bazai dauka dasaukiba acikin fadansa akashe mutum" Duk ta kagu yabar mata dakin tayi tunani donhaka tafara baccin karya, ganin haka yasa yace "opps! Harkinyi bacci barin koma " Yana fita yarufo mata kofan tawaje tuni tamike tazauna dakyau, yayanta yaje as mutumin arziki yana shuka tsiya daga kasa, lalle toh ai babu marabansu da ita, gashi batama san sunan yayan ba, yanzu yazatayi? Tunani yazo mata tunda yusuf yace suna yawan zama tare dole ta ziyarci fada, Taci wanka tasha kyau sosai abaya ne bski ajikinta tafice tsum tanufi fada ganin fadawan suka fara tsareta tanuna musu cewa tazo gaysheda gimbiya yakolo, dolenta tajira aka tambayo gimbiya sukace ai aliya ce. Nan tabada dama aka shiga da ita, Tagama survey dinta kafin tanufi fannin yakolo tana isa yakolo tagwada farincikinta sosai takuma ja ta ajiki, aliya tagwada mata yau tazo gari don tagaydata nan da nan yakolo tace "toh dole nabaki masauki, zaki zauna a fada harsai lokacin dakika ga daman tafiya"

To download Inside Arewa application for easy access follow the link

No comments:

Post a Comment