Wednesday, 1 June 2016

Halaccin Sarauta episode 15


To read the previous episodes follow the link

Fitanshi baikai awa daya ba saigashi da bilkisu,tana shigowa aliya tajata suka shiga daki tabarshi a falo, shigansu bilkisu tayi mamaki kwarai, kallon gidan takeyi dakuma aliya wacce taga wautanta na rashin gane aliya tunfarko, tabbas aliya batayu kama da baiwa ba idan tayi laakari da yanayinta, aliya ta numfasa sannan tace " kiyi hakuri bilkisu ke kadai na yarda inasokitaimakeni, anma saikinmin alkwari cewa har mutuwarki babu wanda zaki fadawa" bilki tayi shiru,azaman duniya idan ana kirga masu sonta tasan dole aliya tazo aciki, domin ta taimaketa sosai donhaka batareda wani tunani ba tanuna amincewarta anan aliya ta fara kissamata labarinta daga farko har karshe akan waccece ita, dakuma dalilinta nazuwa fada!, bilkisu ta tsorata sosai don bata taba kawo haka arantaba, anan taroki bilki datazama idonta acikin fada, bilki babu gardama ta amince aikuwa aliya ta mata alfarman komeye takeso zata mata, dawannan suka fito yusuf na falo har bacci yafara kwasansa domin sun dade adakin, bilki tafito haka yamayar da ita kamar yadda ya fito da ita, dawowansa yasami aliya na kallo shi abun na damunsa toh batada yanuwane suka barta take wannan garajen? Kayan kasada? Hakadai yazauna akujera yadurkusa dakanshi takaleshi ganin yadda yayi tace "meye ka sunkuyar dakanka kaman shege a rabon gado" abun yabashi dariya anma yadaure fuska bai tanka ba, ganin haka yasa itama ta tsuke tareda cewa "alakarmu bazata yiwuba inhar bakadena shaye shaye ba, daga yau kadena!" Yayi shiru yana kallonta ko falmata datace yabar shaye shaye tana masa fada baitabajin yadena ba sai ranan, yasa aranshi bazaikara shan wani abuba, "insha Allah nadena" jinhaka yasa tasake masa sukadanyi tadi duk maitarsa nason sanin meye plans dinta taki fadamishi, anan yake cemata auren abdullahi bayan sallah, ta ce "ni yakamata nashiga kasuwa ma saboda banda kayan azumi ko kadan, muje karakani" aikuwa suka fice tsum dogon riga iya gwiwa dakuma wando takara sawa sannan sukafito yakalleta dakyau azucinyanshi yace "wannan yarinyar yarbariki ne wlh" kaman tashiga zuciyansa tace"karkayi tunanin ni yar bariki ce, nayi rayuwar kudu" yayi murmushi tareda cewa "kinyi kyau" dakafa suka taka har kasuwa shikam har kafofinsa sunfara ciwo yasan yau sai yayi jinyansu amma itakuwa ko ajikinta tasaba , suka siya komi don inhar zata mika kudi shiyake mikawa, ganin zai rainata tace "nifa ba irin yanmatanku bane na zamani dazakuna kashewa kudi donku siya zuciyarsu" yayi murmushi sannan yace "oh mata dai, yanzu da bansayaba zakije kice yarima guda dan sarki anma haka yabarni nasa kudi nasiya tsabar rowa" abun yabata dariya tace " toh aiku mazanne hannunku kaman kuna ajiyeshi agydakafin inbanda haka ai kasan shi kyauta yana kara dankon zumunci, zuciya tanason mai taimaka mata, ko mata da mijine wlh inkana kyautata mata darajanka dabanne, aanma wasunku sai balain rowan tsiya, wani lokacin kunsan mace tafi karfin abu duk dahaka kumata mana, ko bazata karba ba. Anma wai saikuce kuna gwadata ne, waxaku rainawa hankali, gwara kanayi kana ihsani," tabashi dariya nan yakara tabbatarwa macece mai experience na rayuwa, anma yadanne ransa yace " samarin g.s.u marowata ne kenan?" Kut wlh a a, mukam yan gombe akwai kyauta" "Ta ina kika zama yar gombe????" "Oho dai gwaramu kaida kagama a.t.b.u samarin atbu neda rowa" "Allah kije kiga mu har mota muna saya" "Ae naji wannan zubairun" Ganin me masara sukayi ta tsaya tana dubawa tadauko daya tabashi tareda cewa "Ci" yakarba ya gutsura " hmmm dadi" Suna tafiya sunaci baisaba ba duk saiyajishi a tsarge anma yahadu da yar tasha yazaiyi da rayuwansa?" Gyda suka nufa kicin suka ajiye na ajiyewa sannan suka fito, yamata sallama yanufi gyda Tun ranan suka soma shakuwarsu har azumi tashigo shine yarage zuwa don yana wuni bacci ne, aliya kuwa alokacin takafa ibadunta, tanajin labari lokaci lokaci agun bilki idan tasa yusuf yadaukota, falmata bata canjaba, donhaka aliyama bata ajiye kudirinta ba, aliya tayiwa bilki kayan sallah, yayinda shima yusuf haka yasiyo akwati guda yaciko da kaya yakawo mata, taki karba anma ya ajiye yafice yabarta, taji dadi koba komi her first love worth it, ayanzu son datakewa yusuf yawuce duk wani tunaninta, akullum addua take Allah yabarsu tare, Yusuf kuwa satin farko shiru baisha giyaba , ana shiga nabiyu yafara canjawa, kana ganinsa kaga marar lafiya watarana ansha ruwa yashigo gun aliya anan yazauna kaman zaimutu tayi tambayan duniya anma yace mata bakomi, bata rabu dashiba harsai da ya rike cikinsa yana cewa "aliya ki gafarceni, kishi nakeji " dasauri tadauko masa ruwa yasha anma ya girgiza kai alamun bashibane alokacintagane meyake nufi, babu giya agidan duk tarude "karka mutu bazaka mutuba, Allah yaga zuciyarka kaci gaba da danneea" idonsa yayi jajur, duk yafita hayyacinsa batasan lokacin data fitaba, giyan taje tasiyo takawo mai tareda cewa gashi kasha kadan, ahaka harka bari" yakalleta idon jajur yace "nariga nayi alkawari bazan kara shaba, kibari kawai" hakan yasa ta je toilet tajuye gaba daya tafito sai karfe gomandare sannan yasamu kanshi yakoma gyda nanma yaje yakara tarar dawani tashin hankalindon falmata cewa tayi yaje shan giya baikulata ba hartagama hargowanta tafice anan kuma labari ya iso mata cewa kullum ana ganinsa tareda wata, nan ta bukaci a dubo mata wayene! Dukkan sarakunan gari ancika makil a fada, donyin council meeting wanda akeyi kowani laraba, masu sarautan duk kowa yazauna don a tattauna matsalolin al umma dake faruwa, inda anan aka shigo musu da kayan sha da ciye ciye, sungama lafiya inda waziri yasanar da auren abdullahi dazaayi a sati mai xuw, sannan yamusu barka da sallah, zaikoma yazauna sai yafara rike wuya yana muzurai, duk hankalin kowa yayi kanshi anan yakwanta yana muzurai, farin yawu yafara fitarwa, tuni aka nemo likita anma kafin ya iso, waziri yace ga garinku Labari tuni yazaga gari aliya wacce ta idar da karatun quraninta taga yusuf yashigo a birkice idonss jajur yana cewa"aliya nasan kinzo daukan fansa ne anma kina mace meya hadaki da kisa?" Takalleshi tareda cewa "wana kashe? Sannan meyasa zanyi kisan?" "Karki rainamin hankali waya kashe waziri?" Mikewa tayi zummur tareda dafa kirji"yarasu? Alhndlh? Amma waye haka yataimaken? Kenan bani kadai bace me harinsa" "Abunda zakice kenan? Ke wato kin kwashe kayanki agaban manzo" "Bawani kwashe kaya. Wlh bani bane, anma inaso nasan waye, burinmu daya, ni nayi niyan kashe waziri anma bada hannuna ba, naso nabi hanyar da hukuma zata hukuntashi, nawa tona masa asiri ne kawai" Ficewa yayi yabarta "Aliya tuni tafara tunani, azumi na garata anma haka tamike taji wayam batajin yunwa, duk ta kagu tasan waye mai tayata aikinnan, Wayarta ce tayikara daukan dazatayi taga antynta ne "Aliya ki saurareni kiji yayanki yazo yadamu ingayamasainda kike naki fada jin kince kar infada kowa, anma kuma yanemoki donhaka kizama ashiri zai iya samunki kibi ahankali don yadau alwashin kashe su ne acewarsa kina bata lokaci" Aliya tayi kufum kafin tace "wani yaya? Dama imada yayane? Yaushe aka haifeshi? Ina yatafi tuntuni?

To download Inside Arewa application for easy access follow the link

No comments:

Post a Comment