Saturday, 30 July 2016

Hallaccin Sarauta Episode 37

Continuation of Hallaccin Sarauta Episode 37

Read the previous episodes HERE

falmata kashe kanta ne batayiba domin amincewar da sarki yayi, ta tura duk wanda take ganin zai iya magana wa sarki anma taci tura, waliyyim aliya shine alh.hussieni anma sufyan yayi kif da ido akan bai san zance ba, dole akarshe aka bukaci alh.hamidu yazama waliyyi, duk soyayyan dayakewa hassana yayine domin yasamu hankakinta anma daga karshe yaga sone na gaskiya , hussiena ma tasha alwashin zaman lafiya kam aliya da yusuf bazasu sameshiba agydan Anyi zama a kotu inda lawyernsu sufyan yaci karan, kotu tabawa alh.hussieni zaman prison na shekara ashirin da daya sannan ta bukaci daya fidda gadonsu ko kuma kotu taci tararsa, a ranan aliya tayi kukan farim ciki tunda take bata tabajin kwanciyan hankali irinna ranan ba, jitayi kaman ansauke mata dutsen badr akirjinta, tuni ta maida hankalinta kan batun aurenta duk da tasan tashin hankalin dazata shiga, antyn abuja ne ta bukaci taje don su samu ayi siyayyanta, ta tattara dan komatsanta duk da yusuf bai so ba, shi yanzu babban damuwansa yaga ya aureta, Sunyi sallama tatafi yayinda yakoma fada, shigansa yatarar da bilkisu da abincinsa, zama yayi yarike kai yana tunani kansa yamasa nauyi har yanzu falmata taki yarda da auren, yasan son zuciyanta ne anata tunanin wai saidai ya auri hussiena, shi haryau hussiena bata kwanta masa arai ba , bilkisu ce tayi tari hakan yadawo dashi daga tunaninsa yakalleta sannan yace "meke faruwa acikin gyda gameda aurena" kanta a kasa tace "Gimbiya yakolo tafara shiri, yayinda gimbiya falmata bata fara ba, ita shirinta da hussiena takeyi" Baice komi ba yatashi yafice sannan yanufi fannin falmata anma sa iso sannan yashiga daga ciki tana zaune akan kujera yazauna akasa abinda bayayi, hakan yatabbatar mata da bukata yazo dashi, bata kulashiba yasa kanshi akasa sannan yace "Ina neman amincewarki na auren aliya" "Ban bayarba, kuma ko bayan raina ban sa baki ba" "Inaso kibani hujjanki wanda addini ta haramta min auren aliya" "Yar kan titi!! Yarinya tagama gantalinta agari! Kowani dan iska ya kwasa! Kainan tayi fitsari tabaka kasha ba dole kabiya kaman agwagwa ba!" Ga mamakinta taga yamike yafice , baikuma cewa komiba, tunda shi mahaifinsa yasa albarka hujjanta ba kwakkwara bane dazatace masa kar ya auri aliya, fannin yakolo yaje, yasami hauwa tana ganinsa tafice don haryanzu tsoronsa takeji, yakolo tayi murmushi tareda masa iso, bayan karasowarsa yazauna dum a kasa, nan da nan tagano alfarma yazo nema, yagaysheta ta amsa masa sannan yace "Naje gun gimbiya na nemi ta amince min auren aliya taki yarda, kuma hujjojinta ba ingantattu bane, kitaimaka ko zakisa baki" "Bakomi yusuf, kasan mahaifinka inta sa rai akan abu, kai yakamata ka lallabata anma zan gwada kokarina kaji"

"Nagodr Allah yasaka da alheri" Ficewa tayi, tuni abdullahinta ya fado mata arai, tasan yarinyar dayakeso aketa rikici akai, gashi cikin mata yafara fitowa duk da sunriketa tana fadan akan saita haihu tukun zasu barta tafita, Yakolo tayi iya kokarinta don fahimtar da falmata anma falmata kaman ana zuba mata man fetur, dahaka biki ya matso kusa aliya tadawo gari saidai tagagara zama, rokon yusuf tayi akan ko zai taimaka yabata aron bilkisu, haka kuwa akayi , tuni bilki tafara taimaka mata, jin aliya zata auri dan sarki tuni dangin nesa da wanda aka manta dasu suka fara bayyana kowa saiyace yazo auren marainiyan Allah, Ran jumaa aka daura auren aliya da yusuf, inda akayi dinner daredare nagani nafada, munsha gwaggori munsha rawa,yusuf na makale da matarsa, hannunsa gam anata shi yanzu gani yake duk duniya bawanda yakaishi hakuri da juriyan dayayi, angama dinner inda aka kai amarya fanninta side guda aka ware mata a fada, dakuna uku da falo biyu,tabbas tasamu kaya tasha gata, sufyan yashare mata hawaye tayi kukan rashin iyaye anma batayi maraici ba, kowa yayi mamakin ganin yadda falmata tasake ranta da maganan biki, harwani jan aliya take ajiki, acewarta komi yawuce,anma aliya tagagara sakewa da ita, randa aka kaita an watse aliya tana kunshe jikin gyalen kyabban da aka rufata dashi duk ta kagu tana jiran angon nata,don tsoro takeji dakin ya mata girma sosai, kukan kare tafaraji, dafarko bai dametaba anma datayi tunanin gydan babu inda aka ajiye kare, tuni tafara tsorata kodai yusuf yasiya ya ajiye a fanninta ne? Toh anma matsalanta shine jin kukan take kaman agabanta yakeyi, hannunta ne yafara bari tafara salati da dan karfi sannan taji shiru, can kuma takarajin kukan karen daga nesa saikuma karan kofa, saura kadan tasake fitsari awandonta taji anbude kofan, yusuf ne batasan lokacin data rungumoshiba, jikinta na bari jinhaka yasa shima ya kamata, sunfi mintoti ahaka kafin yajawota yazaunar da ita akan lallausan gadon,

"leeya meya sameki?" Bata bashi amsaba, tafarajin wani kukan karen wannan karon harda kulya, salati takeyi jikinta na bari, tuni jikinsa yayi sanyi domin bata cikin hayyacinta, alwala yadauro yace itama tayi anma dole saida yarakata toilet din don tsoron datakeji. Tafito yajasu sallah yakamo kanta yatofa mata addua, sannan yafara tambayanta akan littafai daga kan fiqhu, hadiths da dan tauhid, yayi mamaki sosai dayaga tanada sani, baitaba zaton tasani sosaiba, daganan ne yace "mezakici?" "Babu kabarshi" Cire mata kallabin yayi, sannan yarikota naman ya yaga kadan yafara bata tana tauna ahankali yabata da soya milk haka taci takoshi sannan yace tadan kwanta, tana kwanciya taji kukan karen zumbur tamike kaman an tsira mata allura, rikota yayi yana tofa mata addua, atakaice haka suka kwana a zaune har asuba, dazaran zata kwanta sai kukan kare ko qulya, asuba nayi sukaji shiru, hakan yabashi daman fita masallaci, tana sallah bata fitoba saboda baccin daya kwasheta, karfe shida daidai saiga umma uwar tsoro falmata ta turota buga mata kofan tayi can dai tabude, bata tasheta ba ta nufi kan gadon taja bedshit din tafice, kaiwa falmata tayi wanda tana zaune tana jira ganin babu komi akan bedshit din yasa ta salati, tana cewa "saida na gayawa yusuf wannan yarinyan tagama gantalinta, yaki yarda, kue kudauko min ita," Dauko aliya cak akayi aka wurgata akasa. Jiri ne yake dibanta anma tuni ta warsake don ruwan sanyi tas falmata tasa aka watsa mata, alokacin yakolo tazo ranta yayi mummunan baci, inba raina darajan dan adam ba yazaayi matar danki dan cikinki zakina wulakantawa? Tuni fa gyda ya hargitse, nima benaxiratu idona na rufewa anma dole nabudesu don ganin mexai faru.

To be continue....

Godiya ga Benaxir Umar da ta rubuta.

No comments:

Post a Comment