Saturday, 11 June 2016

Halaccin Sarauta episode 23

Continuation of Halaccin Sarauta episode 23

Read the previous episodes here



Aliya ta gyada kai wanda itakanta inna tasan cewa baikai har zuci ba, tana tantama dakyar ta amince anma tana tsoron abunda zaije yadawo idan aliya tayo bincike, bata cika son bincike ba itakam, tadai mike tabarta, tana fita aliya ta watsa ruwa tasako dogon riga tadaura dankwalin sannan tafito, inna ta kalleta "ina zuwa?"

"Kasuwa" ta amsa, inna takare mata kallo , saidai batace komi ba saikin dawo, aliya tasan mezatace donhaka ne ma tagodewa Allah datayi shiru, Allah yagani batason takuri rayuwarta ba tsanani, tafice saidai itakanta tasan tafita ne don taji gydan ya isheta batada dalilin fita, ganin me awara tayi tanemi gu tazauna tasiya ta murmuzashi a cikin ledan yadawo kaman kwado sannan ta tusa a jakarta, gydanta nada taje haryanzu baa shiga gydan ba, tashiga tazauna taci awararta ta koshi dama tana yawo da coke dinta, takora da coke sannan tafito da zummar takara gaba, hanyan fada tanufa kai tsaye batareda wani tunani ba, harta yanki kwana taga sufyan agabanta bai saurari mezatace ba ya damko hannunta ya wuce da ita basu tsaya ba sai awani lungu, "Meye kuma yaya?" "Bakida hankali ko? Ina zakije?" "Fada zanje" "Kimusu meye" "Na ga yusuf" "Mahaukaciya,wuce mutafi" Fizgan hannunta yayi suka isa bakim titi ya tsari keke napep suka hau sannan yayi kwatancem gun,

"Da kafana nazo, dakayi hakuri zankoma da kafana!" Bai amsata ba har suka isa yamikawa mai keken kudinsa sannan suka shige inna tana tsakar gyda taga yazo yawuce da aliya donhaka ta dauraye hannunta dama tana wanke kayan miya ne, tabisu don ganin meke faruwa, "Bakida hankali ne? Sau nawa zangayamiki aliya sau nawa zangayamiki ki fita hidimar fada!, kifita rayuwarsu, mutanennen baruwanki dasu, yusuf dinnan nagayamiki mahaukaci ne ki hakura dashi kinki yadda wato ga karamin dan iska" Inna tashiga dakin ganin yana matsifa yaki shiru tace "meyene yake faruwa? "Inna kiga shigan jikinta, yarinya gaba daya tadawo inyamura, aladan yarbawa, kinmanta akasan hausa kike? Kinje kin dauko dabian wasu kina mana anan!" "Yau nashiga uku zaku kasheni, meye zaka wani ce yarbawa, agarin yarbawa nazauna? Kaidai inzakayi matsifanka kayi ai gwara ni kai fa? Wayasan mekake aikawata, dogon riga ne ajikina meye aibunsa, ?" "Dakikasa dogon rigan shine zaki cire dankwalin?kin yafashi a gefe ,kokuma kisaka gajeren wando kina yawo a kasuwa, zanga ta inda zaki auru a garinnan, dawannan halin tashan kikeson auren dan sarki? Wazai baki? " Haushi suka bata itadai tasan ba laifi tayiba sunbi sunsa mata ido, wacce tasa atamfa ta rataye gyale awuyanta tarufo jikinta baaga laifinta ba? Saita datasaka abaya dayarufe jikinta don kawai tayafa gyalen?"nikuma nce maka zan auri yusuf ne? Ko na ce maka zanyi aurene? Basai ku aurar dani nagani ba" bai kulata ba yace "inna karta kara fita dawani shigan daya sabawa addini, wannan ai karamin hauka ne!" Yana fita tamike aranta tana cewa inga karamin beran dazai takurani , da tuntuni bakasan daniba saidana girma nasan darajana da mutuncina, tsaki tayi tamike akan kujera baccine mai nauyi ya kwasheta bata farka ba sai magrib tamike tadauro alwala tayi sallah sannan takunna tv duk da batagane mesukeyi don wani indian film ne tadai zurawa tvn ido sallama taji anyi anshigo tagane muryan anma tarufe idonta kaman tana bacci, yashigo yazauna ganin tana bacci yazura mata ido, yarasa yazaiiyi yanason aliya baikuma san meyasa takeson juya masa baya ba, saiyanzu yasan dalili da hussiena takirashi awaya yatabbata tazo tasami aliya ne, yadda yasan kishin aliya yasan saiyayi dagaske, ganin tanata runtse ido yaki ya tafi yasa tadanyi juyi.

To be continue....

Godiya ga Benazir data rubuta wannan labarin.

No comments:

Post a Comment