Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan ya bayyana cewa abin kunya yadda a halin yanzu kasashen duniya ke buga misali da Nijeriya a matsayin kasar da Harkokin tsaro suka tabarbare.
Jonathan ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da bude wata gada da Gwamnan Ekiti, Ayo Fayose ya gina inda ya bayar da misali da Shugaban Kasar Ghana, Nana Akufo wanda a kwanan nan ya yi izgilanci ga hukumomin Nijeriya kan rashin tabbatar da tsaro.
No comments:
Post a Comment