Wasu 'yan bindiga sun kai hari a Zamfara inda suka kashe mutum 27 a karamar hukumar Maradun.
'Yan bindigar sun kai harin ne a ranar Juma'ar da ta gabata cikin yankin Gidan Goga da ke karamar hukumar Maradun.
Tsohon kwamishinan watsa labarai na jihar Alhaji Ibrahim Dan malikin Gidan Goga ya shaida wa BBC cewa 'yan bindigar wasu matasa ne a yankin da suka dauki bindigogi suka shiga daji.
"Sun iske manoma suna shuka da safe suka bude masu wuta bayan sun yi gargadin a kauracewa yin shuka a gonakin yankin," in ji shi.
Ya ce lamarin ya kara muni bayan da 'yan banga suka yi kokarin kai dauki, inda 'yan bindigar suka kara kashe wasu mutane baya ga manoman da suka kashe da farko.
Me ya sa babu wanda ya damu da rikicin Zamfara?Zanga-zangar matasa kan yawan kisan mutane a Zamfara
Tsohon kwamishinan ya ce yawancin mutanen kauyukan da ke yankin, bugaje ne makiyaya da ke rikici inda suke zargin juna da sace-sacen shanu, kuma yanzu rikicin ya shafi hausawa manoma.
Ya ce an tura jami'an tsaro bayan da al'amarin ya faru kuma sun janye daga yankin bayan an yi jana'izar wadanda suka mutu.
Jihar Zamfara dai na cikin jahohin arewa maso yammaci da ke fama da yawaitar kashe-kashe da sace-sacen mutane da dabbobi.
Gwamman mutane ne suka mutu a 'yan watannin da suka gabata sakamakon hare-haren da aka kai wasu kauyuka a jihar ta Zamfara.
Daruruwan mutane aka kashe a Zamfara a tsawon shekaru shida da aka kwashe ana fama da matsalar tsaro a jihar.
No comments:
Post a Comment