An Sanya Wa Katafaren Asibitin Da Sanata Shehu Sani Ya Gina Sunan Balarabe Musa
Da yake jawabi a yayin bikin bude Asibitin wanda ya gudana a Unguwar Bagado Kamazoo yankin Karamar Hukumar Chikum ta Jihar Kaduna, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewar la'akari da halin kunci da kuma takura da Jama'ar yankin ke ciki dangane da batun kiwon lafiyar su, ya sanya shi zabura wajen gina musu Asibiti na zamani domin amfanin su da 'ya'yansu harma da jikoki wadanda za su zo anan gaba.
Sanatan mai wakiltar shiyyar Kaduna ta tsakiyan ya kuma kara da cewar, ya sanya wa Asibitin sunan Dattijo tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa, bisa ga irin kokarin da Dattijon ya ke da shi na kishi gami da taimakon talakawa inda ya bayyana shi a matsayin abin koyi ga Shugabanni na kwarai.
Da yake tofa albarkacin bakin shi dangane da muhimmin aikin da Sanatan yayi, Dattijo Balarabe Musa ya bayyana jin dadi gami da farin cikin shi akan kwazo da kokarin Sanata Shehu Sani, wanda ya bayyana shi a matsayin wakili nagari kuma Shugaba wanda ya damu da damuwar Jama'ar shi, sannan ya kara da cewar irin su Shehu Sani sune Shugabanni nagari wadanda suka dace da suja ragamar Al 'umma, wadanda ba su damu da tara abin duniya ba, babban abinda ke gaban su shine yadda za su tsamar da Jama'ar su daga halin damuwar da suke ciki.
Mista Adamu Giwa shine Sarkin Kauyen Bagado, ya mika godiyar Jama'ar shi ga Sanatan wanda suka bayyana shi a matsayin Mutum Karimi wanda baida nuna wariya ko wani bambanci a tsakanin jama'a, domin a tarihin garin nasu na Bagado babu wani Dan siyasa da ya taba kai musu dauki sai a wannan karon da Sanata Shehu Sani ya share musu hawaye, a bisa ga wannan dalilin su basu da wani Shugaban da za su zaba a yankin Kamazoo da Karamar hukumar Chikum, karamar hukuma mafi girma a jihar Kaduna mallakar Kabilar Gwari, sai Sanata Shehu Sani.
Sanatan Kaduna ta tsakiyan ya kuma jagoranci kara bude wasu manyan Asibitoci guda biyu wadanda ya gina a garin Gadagau dake yankin Karamar Hukumar Giwa, da kuma daya Asibitin dake garin Gadani ta Karamar Hukumar Igabi.
Dukkanin Al'ummomin yankin Kananan Hukumomin Uku da aka zanta da su, wato Kananan Hukumomin Giwa da Igabi da kuma Karamar hukumar Chikum, Kananan Hukumomi uku daga cikin Bakwai wanda Sanatan ke wakilta a Majalisar Dattawa, sun bayyana cewar ba su da wani Dan takara da za su zaba sai Sanata Shehu Sani a kakar zabe da ke tafe ta 2019.
No comments:
Post a Comment