Daga Yusuf Ibrahim Yakasai (BBC Hausa)
Tun bayan rasuwar Halifan Tijjaniya a Najeriya da kasashe makota Shaikh Isyaku Rabi'u, hankula suka fara karkata kan wanda zai gaji matsayinsa a darikar, wacce ke da dimbin mabiya.
Kawo yanzu dai mabiya darikar ta Tijjaniyya na ambata wasu shugabanni da ake ganin sun cancanci matsayin.
Sai da alama za a iya samun sabanin ra'ayi tsakanin 'yan Tijjaniyya, kasancewa kusan kowa na da nasa gwanin.
Ko da a lokacin da aka bawa Shaikh Isyaku Rabiu matsayin ma, wasu shugabannin darikar kamar Shaikh Dahiru Bauchi sun nuna rashin amincewa.
Kuma bayanai sun ce tuni ma wasu suka fara bayyana sha'awar matsayin.
Asalin halifancin Tijjaniyya a Najeriya
Halifancin darikar Tijjaniyya ya fara ne bayan shekarar 1963 lokacin da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na daya ya bar sarautar Kano ya koma Azare da zama.
A lokacin ne jagoran darikar ta Tijjaniyya na duniya Shaikh Ibrahim Nyass ya nada Sarki Sanusi a matsayin halifansa a Nijeriya.
Shaikh Inyas ne ya fara nada Sarki Sanusi na daya (na farko daga dama) a matsayin halifansa a shekararun 1963 bayan ya bar sarautar Kano
Shaikh Dahiru Bauchi ya shaida min cewa a shekarar ya hadu da Shaikh Nyass a birnin Makka a lokacin aikin Hajji, kuma ya ba shi sako wajen Shehunan Tijjaniyya a Najeriya musamman ma Kano da kuma Sarki Sanusi (wanda a lokacin ya koma Azare bayan barin sarautar Kano), cewa ya nada shi halifansa.
"Duk mai son ziyarata, to ya ziyarci Sanusi" In ji Shaikh Nyass, kamar yadda Shaikh Dahiru Bauchi ya fada.
Daga baya ne bayan ya dawo daga aikin Hajji, Shaikh Nyass ya aiko da takardar nada Sarki Sanusi a matysayin halifansa.
Nada Shaikh Isyaku Rabiu Khalifa
Khalifa Isyaku Rabi'u ya fuskanci kalubale bayan nada shi a matsayin Khalifan Tijjaniya a 1995.
Tun bayan rasuwar Khalifa Muhammad Sanusi a 1990, ba a nada wani a matsayin ba sai 1995 lokacin da jikokin Shehu Tijjani daga Maroko suka nada Isyaku Rabi'u a matsayin halifa.
Sai dai matakin ya haifar da takaddama tsakanin manyan darikar, inda wasu shugabanni kamar Shaikh Dahiru Bauchi suka nuna rashin amincewa da nadin.
Shikh Dahiru Bauchi ya shaida min cewa Shaikh Nyass ne kadai ke da ikon nada halifa, kuma tunda a lokacin ba ya raye, babu wanda ke da ikon nada wani a matsayin halifan Tijjaniyya.
Don haka, wasu ma na ganin Shaikh Isyaku Rabi'u sai dai ya zama halifan Sarki Sanusi, amma ba halifan Tijjaniyya ba.
To sai dai tun bayan nada Isyaku Rabiu, malamin ya rungumi al'amuran darikar ka'in da na'in, musamman wajen kashe kudi, da yi wa jikokin Shehu Tijjani da 'ya'yan Shehu Nyass hidima.
Abubuwa hudu da za a iya tuna Khalifa Isyaka Rabi'u da suYadda rayuwar marigayi Khalifa Isyaka Rabi'u ta kasance'Ba a bukatar wani halifa yanzu'
Rasuwar Shaikh Isyaku Rabi'u ta sake bude wata kofar ta neman halifancin darikar, abin da ke nuna cewa duk wanda aka nada tamkar shi ne jagoran mabiya darikar a Najeriya.
Wasu jagororin darikar na ganin babu bukatar nada wani halifa, tunda batun halifancin ba ya cikin sharuda ko ka'idoji na darikar ta Tijjaniyya.
Babban limamin masallacin Abuja Shikh Ibrahim Ahmad Maqri na ganin batun halifanci a darikar ta Tijjaniyya ba wani abu ne mai muhimmanci ba, abin da ya ke mafi muhimmaci shi ne kiyaye ka'idojin darikar da yin aiki da su, da kuma hada kan jama'a.
Shaikh Maqri ya ce ko da nadin da aka yi wa Sarkin Kano Sanusi I "dalili ne na addini, dalili ne zumunci, dalili ne na karfafar 'yan uwantaka, da kuma rage damuwa na abin da ya faru da Khalifa Sanusi".
To amma ganin yadda zamani yake sauyawa da kuma yadda aka shafe shekaru sama da 20 'yan darikar ta Tijjaniyya suna daukar Shaikh Isyaku Rabi'u a matsayin jagora zai yi wuya yanzu su zauna ba tare da jagora ba.
Wa zai karbi mukamin a yanzu?
Tuni dai wasu a darikar suka fara yunkurin neman wanda zai zama sabon Khalifa, kuma da alama za a iya kai ruwa-rana.
Shaikh Dahiru Bauchi.
Shaikh Dahiru Bauchi ya ce ya wuce a ce za a nada shi halifancin Tijjaniyya a yanzu, domin tuni Shehu Inyass ya nada suYana daga cikin almajiran Shaikh Ibrahim Inyass 'yan kadan da suka rage a rayeTun a zamanin Shikh Inyass yana cikin mutanen da ke kare darikar Tijjaniyya da yadataShaikh Inyass da kansa ya ambace shi "Kakakin Faida (Lisanul Faidati)"Mahaddacin Al-kur'ani ne kuma yana daga cikin manyan malamai a NajeriyaWasu na ganin shekarunsa sun ja don haka bai kamata a kara masa wani nauyi ba
To amma a tattaunawar da muka yi da shi Shaikh Dahiru Bauchi ya ce shi ba ma ya bukatar matsayin, domin kuwa tuni Saikh Inyass ya nada shi halifansa tare da wasu manyan darikar.
"Ai ni na wuce nan, Shaikh Ibrahim da kansa ne ya nada mu halifofi mu, kuma shi kadai yake da iko ya dauki daya daga cikinmu ya daura a kan mu gaba daya," in ji malamin.
Ya kara da cewa, "Shi halifa a cikin Tijjaniyya kamar janar ne a cikin soja, ba guda daya ba ne, don haka kowa ya san wanda ya fi shi."
Wasu jagorori a darikar Tijjaniyya na ganin Shaikh Dahiru Bauchi ba ya ma bukatar wani nadi na musamman, duba da irin matsayinsa a darikar da yadda yake da mabiya, da kuma iliminsa.
Sarkin Kano Muhammad Sanusi II
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na daga wandada ake ganin sun cancanci matsayin halifancin tijjaniya a Najeriya, matsayin da asali kakansa ne ya fara rikewa.
Asalin mukamin dai na Sarkin Kano Sanusi na daya ne, wato kakan sarki na yanzu. Sarkin Kano na yanzu ya kama harkar darikar sosai bayan ya zama sarki. Ya taba bayyana cewa gwaninsa shi ne Sarkin Sanusi na daya, kuma yana so ya gaje shi. Yanzu yana da mulki da kudin da zai iya yi wa darikar hidima fiye da wasu shugabannin da damaYana da ilimin addini da na zamani, kuma yana kara samun karbuwa a tsakanin wasu musulmin NajeriyaYa ci gaba da jagorantar zikirin Juma'a da ake yi duk shekara a gidan Sarkin Kano, wanda aka fara a zamanin Marigayi Ado Bayero.
Wasu bayanai na nuna cewa tuni wasu mabiya darikar da kuma wasu makusantan sarkin suka fara nuna cancantarsa.
Shaikh Shariff Ibrahim Saleh
Wani babban jagoran da ake ganin ya kamata ya zama jagoran mabiya darikar ta Tijjaniyya a Najeriya shi ne Shaikh Shariff Ibrahim Saleh Alhusayniy.
Yana daga cikin manyan malam darikar Tijjaniyya da Musulunci baki dayaYa yi karatu a wajen manyan malamai sama da 300 a kusan dukkan kasashen musulmai na duniyaYa yi karatu a wajen Shaikh Inyass, kuma wasu na yi masa kallon daya daga manyan almajiransaWasu na ganin ya fi kowa cancantar zama jagoran darikar a Nijeriya
To amma malamin bai fiya shiga cikin al'amuran shugabanci ba, ya fi maida hankali wajen karantarwa da rubuce-rubuce da bada fatawa da kuma tafiye-tafiye.
Don haka wasu na ganin ko da an yi masa tayi da wuya ya karba.
Da gaske ne Shehu Ibrahim Nyass ya bayyana a Maulidin Abuja?Ganin Shehu Ibrahim Nyass karama ce - Dahiru BauchiAikin da ke gaban sabon jagoran Tijjaniyya a Najeriya
Nijeriya ita ce kasar da ta fi yawan jama'a a nahiyar Afirka, kuma yawan mabiya darikar a kasar ya zarta na kowacce kasa a nahiyar.
Kuma saboda muhimmancin da Shehu Inyass ya nuna na kasar a fuskar darika, ya sa wasu ke kallonta a matsayin cibiyar darikar bayan Maroko da Senagal.
Don haka duk wanda zai zama jagora tamakar ya dauki nauyin 'yan darikar ne a kasar da wasu kasashe makwabta kamar Nijar da Ghana da sauransu.
Shaikh Maqari na ganin babban abinda ya kamata ya sa a gaba kamar hada kan 'yan darikar da sauran musulmin kasar, musamman wadanda suke da sabanin fahimta.
Yace kuma dole ne sabon jagoran darikar ya maida hankali wajen nisanta darikar da bara-guri da suke aikata wasu abubuwa da suka ci karo da addinin musulunci, kuma suka fakewa da sunan darikar.
Wasu malaman darikar kuma na ganin dole ne a yi cikakken nazari kafin a zabo wanda zai zama jagoran darikar.
Malamai kamar Shaikh Nura Muhammad Arzai na cewa dole a samu mai jajircewa, tsayayye, mai kamewa mai tsayawa a kan manufa.
Ya ce ana bukatar mai cikakken ilimi na addini da na zamani.
Malamin ya kara da cewa ana bukatar sabon jagoran ya zama yana da wadata da zai iya kamewa daga abin hannun mutane, kuma zai iya daukar nauyin gudanar da al'amuran darikar.
A yanzu dai za a zuba ido a ga yadda za ta kaya musamman ganin irin tasiri da mukamin ke da shi a darikar ta Tijjaniya.
Darikar Tijjaniya a takaice
An kafa darikar ne a kasar Aljeriya a shekarar 1784. Sheikh Ahmad ibn Muhammad al-Tijjani ne ya kafa ta. Ta yadu zuwa sassan duniya daban-daban, inda ta ke da mafi yawan mabiyanta a Arewaci da kuma Yammacin AfirkaTana kuma da karin mabiya a Afirka Ta Kudu, da Indunisiya da kuma sauran sassan duniya. Akwai sauran dariku na Sufaye a addininin Musulunci amma Tijjaniya ta fi kowacce girmaSun ce suna da muhimman ayyukan ibada guda uku a kowace rana:Neman gafarar Allah; Yin salati ga Annabi Muhammad (SAW) da kuma kadaita AllahSai dai ana zarginsu da wuce gona da iri wurin nuna soyayya ga Shehunnansu, lamarin da wasun su ke musanta waAna alakanta Sheikh Ibrahim Nyass da farfado da darikar a karni na 20 bayan ta kwanta damaAn haife shi a kasar Senegal kuma jama'a kan yi tattaki daga sassan nahiyar da dama domin ziyartar kabarinsaDarikar Tijjaniya ta kasu kashi-kashi musamman a kasashe irin su Nijeriya inda suke da mabiya sosai.
No comments:
Post a Comment