Sunday, 27 May 2018

RAMADAN: Sheik Zakzaky Ya Raba Kayan Abinci Ga Mabukata

Daga Ammar Muhammad Rajab

Kamar yadda ya saba a duk shekara a lokacin azumin watan Ramadana, tun kafin gwamnati ta kama shi, Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky, yana raba kayan hatsi wadanda suka hada da Masara, Gero, Shinkafa, Suga da sauran su a irin wannan lokacin. Shekara na uku kenan (duk da yana tsare) a jere duk da Shehin Malamin gwamnatin Nijeriya na ci gaba da tsare shi, amma Shehin Malamin ya ci gaba da wannan aikin alherin ga al’umma.

A bana ma kamar kowacce shekara, an raba hatsin a inda aka saba rabawa a cikin Unguwanni na cikin karamar Hukumar Sabon gari da Zariya wanda ya hada da: Unguwannin Sabon gari, Unguwan Gwado, Hayin Ojo, Dogarawa, Tohu, Samaru, Shika, Likoro, Chikaji , Muchiya, Tudun Wada, Tudun Jukun, Zariya cikin gari, Dan Magaji, Unguwan Dankali, Wanka da sauransu.

Rabon na bana, an fara shi tun daga farkon watan Ramadanan nan har ya zuwa yau 11 ga watan Ramadan ba a kammala ba. Hakazalika a bana rabon ba a garin Zariya kadai ya isa ba, an raba a garin Kaduna. A bangaren Abuja kuwa, an raba a Mararrabar, Karmajiji, Gwarinfa, Suleja, Masaka, Gwagwalada, Lugbe da sauransu.

Idan mai karatu bai manta ba, shekaru kusan Uku ke nan, gwamnatin Nijeriya na rike da Shehin Malamin, duk da kuwa wata babbar kotun Nijeriya a karkashin mai shari’a Gabriel Kolawale ta ce a sake shi a kuma biya shi diyyar naira miliyan 50 shi da matarsa bisa tsare shi da aka yi ba da hakki ba, kuma a gina masa gida a duk inda yake so a Arewacin Nijeriya, amma har yanzu gwamnatin ba ta bi wannan umurnin ba.

No comments:

Post a Comment